Tafsirun Suratul Asr: Quran/103 (English Tafsir from Mufti Muhammad Shafi's Ma'ariful Quran)
Mubuɗin Sura
- Sunanta: Wannan Sura ta fi shahara da Suratul Asri amma a wasu littattafan tafsiri da Sahihul Bukhari an kira ta Suratu Wal-Asri.
- Sanda aka saukar da ita: Sura ce Makkiyya.
- Jerin saukarta: Ita ce Sura ta goma sha uku (13) a jerin saukar surorin Alƙur'ani, ta sauka bayan Suratus Sharhi kafin Suratul Adiyat.
- Adadin ayoyinta uku ne (3).
- Falalarta: An karɓo daga Abu Madina Ad-Darimi ya ce: "Idan mutum biyu daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) suka haɗu, to ba za su rabu ba har sai ɗaya ya karanta wa ɗayan Suratul Asri sannan su yi sallama da juna. [Abu Dawud] <> Sayyidna 'Ubaidullah Ibn Hisn reports that whenever two Companions of the Holy Prophet met, they would not part company until one of them had recited Surah Al-'Asr in its entirety to the other. [Transmitted by At-Tabarani].
- Babban Jigonta: Duk rayuwa ɗan'adam asara ce idan babu bin Allah a cikinta.
- Daga cikin abubuwan da ta ƙunsa akwai:
- Tabbatar da tsananin asara ga waɗanda suka kafirce wa Allah suka rungumi saɓon Allah.
- Tabbatar da tsira ga muminai masu kyawawan ayyuka masu kira zuwa ga gaskiya.
- Falalar haƙuri a kan bin gaskiya da kauce wa ƙarya da jajircewa a kan haka.
Tarjama da tafsirin aya ta 1-3
- Na rantse da zamani.
Wal asr
I swear by the Time, [1] - Lalle mutum yana cikin asara.
Innal insana lafee khusar
man is in a state of loss indeed, [2] - Sai dai waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari, suka kuma yi wa juna wasiyya da gaskiya, suka kuma yi wa juna wasiyya da haƙuri.
Illallazina amanu wa amilussalihati watawa saubil haqqi watawa saubisabr
except those who believed and did righteous deeds, and advised each other for truth, and advised each other for patience. [3]
Tafsiri
Allah ya buɗe surar da rantsuwa da zamani wanda ƙunshi dare da rana waɗanda su ne mahallin dukkan ayyukan bayi. Ya yi wannan rantsuwa ne kuwa domin ya tabbatar da cewa, duk wani ɗan'adam yana cikin asara a rayuwa, kowa da gwargwadon tasa asarar.
Sai Allah ya togace wasu bayinsa daga aukawa cikin wannan asara, su ne kuwa waɗanda suka siffantu da siffofi huɗu:
- Imani da Allah duk abin da ya umarci bawa ya yi imani da shi, wanda hakan ba zai yiwu ba sai da ilimin sanin Allah.
- Aiki na ƙwarai, wannan kuwa ya ƙunshi duk ayyukan alheri na sarari da na ɓoye; masu alaƙa da haƙƙoƙin Allah, da masu alaƙa da haƙƙoƙin bayinsa, na wajibai ko na mustahabbai.
- Yi wa juna wasiyya da gaskiya, wadda ita ce kwaɗaitar da juna a kan yin imani da yin aiki na gari.
- Yi wa juna wasiyya a kan haƙuri wajen bin Allah da barin saɓa masa, da haƙuri da ƙaddararsa marar daɗi.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Allah yana rantsuwa da duk abin da ya ga dama a cikin halittarsa. Bai halatta Musulmi ya yi rantsuwa da komai ba sai da Allah.
- Nuna muhimmancin lokaci wanda a cikinsa mumini yake ribatar zamansa na duniya wajen neman yardar Allah.
- Imani da Allah da aikata kyawawan ayyuka su ne suke sanya bawa ya samar wa kansa kamala.
- Yi wa juna wasiyya da bin gaskiya da yin haƙuri, da su ne kuma mumini yake samar wa ɗan'uwansa kamala.
- Aiwatar da waɗannan al'amura huɗu ne suke kuɓutar da bawa daga faɗawa cikin asara ta duniya da ta lahira, suke kuma sanya shi ya ci ribar rayuwarsa ta duniya.
- Kira zuwa ga gaskiya yana buƙatar juriya da haƙuri. Hakanan riƙo da gaskiya yana buƙatar juriya da haƙuri.
Additional exegesis
Imam Shafi says that if people thought about Sūrah Al-'Aşr carefully, it would be enough for their guidance. It is a concise but comprehensive Sürah, which in three verses, outlines a complete way of human life based on the Islamic worldview.
In this Surah, Allah swears an oath by the "Time' and says that mankind is in a stale of loss; exception, however, is made of people who are characterized by four qualities:
- faith;
- righteous deeds;
- advising each other for Truth;
- and advising each other for patience.
This is the only path to salvation in this world, as well as in the next world. The Qur'anic prescription comprises, as we have just seen, of four