This Surah takes its name from ayah 33 of Al-i-Imran, like the names of many other surahs, is merely a name to distinguish it from other surahs and does not imply that the family of Imran has been discussed in it.
Recite the two bright ones, al-Baqara and Surah Al 'Imran [2] --Abu Umama Ku karanta masu haske biyu: Suratul Baqara da Ali-Imran. --Daga Abu Umamata Al-Bahili (rA)
Sanda Aka Saukar Da Ita: Malamai sun yi haɗu a kan cewa an saukar da Suratu Ali Imaran ne a Madina, wato bayan hijira.
Jerin Saukarta: Ita ce ta arba'in da takwas (48) a jerin saukar surorin Alkur'ani.
Adadin ayoyinta: A lissafin yawancin malamai adadin ayoyinta dari biyu ne (200), amma a lissafin mutanen Sham adadinsu dari da tis'in da tara ne (199).
Sababin Saukarta: Tun farkon Surar har zuwa aya ta 83 sun sauka ne game da sha'anin kungiyar Nasara da suka zo Madina wurin Annabi (SAW) a shekara ta tara bayan hijira, don haka ne yawancin ayoyinta sun yi magana a kan Annabi Isa Almasihu alaihissalam.
Falalarta: Za ta jagoranci masu karatunta a ranar alkiyama, kamar yadda ya gabata a hadisin An-Nawwas (rA). An karbo daga Anas (rA). Ya ce: "Idan wani mutum a cikin mu ya karance Baqara da Ali Imaran sai darajarsa ta daukaka.
Rarrabuwar mutane wajen imani da ayoyin Alkur'ani masu bayyanannun hukunce-hukunce, da masu rikitarwa.
Gargadin kafiraimakiya Allah da Manzonsa da nuna musu cewa iko da karfi da dukiya da 'ya'ya ba za su amfana musu komai ba ko su kare musu azabar Allah a duniya da lahira, kamar yadda ba su amfani kafiran da suka gabace su ba, irin su Fir'auna.
Ishara zuwa ga yakin Badar da bayanin abubuwan da suka faru a yakin Uhudu.
Bayanin abin da dan'adam yake sha'awa a ransa tare da nuna masa abin da ya fi masa alheri, watau abin da Allah ya tanadar masa a lahira na ni'imamadawwamiya.
Bayanin halayen ma'abota Littafi daki-daki da tona asirinsu da bayanin sabanin da ke tsakaninsu na addini da aika-aikarsu ta ƙarya ta ayoyin Allah da kashe annabawa da masu wa'azi da rashin mika wuya ga hukuncin da ya zo musu a littafin Allah da kiran da Manzon Allah a ya yi wa wanda yake jayayya daga cikinsu zuwa ga mubahala (watau addu'artsinuwa). Sai kuma umarnin da aka ba wa Manzon Allah na ya kirawo su zuwa ga kalmar Tauhidi da jayayya da su game da Annabi Ibrahimu (alaihissalam) da fada musu gaskiya a kansa.
Bayanin cewa, son Allah ba a baka yake ba kawai; dole ne sai an bi Manzon Allah tukunna an yi masa da'a a cikin umarninsa da haninsa.
Ambaton annabawa da bayanin matsayinsu da zabin Allah gare su, da kuma bayanin ƙissar Annabi Isa da mahaifiyarsa da kissar Annabi Zakariyya da dansa Annabi Yahya.
Ambaton wasu daga cikin halye na kwarai da tarbiyyantar al'ummar Musulmi a kansu, kamar wasiyya da tsoron Allah da takawa da rike igiyar Allah da watsi da tsoron rarrabuwar kai da rungumar kira zuwa ga Allah da sauran halaye na kwarai da Surar ta yi tsokaci a kansu.