"Nasan wasu za su yi ta tambaya ta yaya kwamfuta za ta taimaka wa harkar noma? To bari mu dawo bangaren ‘na duke tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar’ wato noma da kiwo. Wadannan sana’o’i a wannan zamani za ka ga yadda na’urar kwamfuta (computer) ta ke taimakawa wajen ganin ingancin Gona da abin da manomi zai shuka, da yadda ake yin taki, da yadda ake fitar da magungunan kwari, da dai makamantansu. A yau akwai kwamfutoci wadanda suke sarrafa kayan gona, kamar irin computer da take tsotse ruwan jikin tumatiri ta kyafeshi a cikin dan kankanin lokaci, babu ruwanka da shanya wa da makamantansu."
https://regexr.com/5faqn#:~:text=%5B%5BNasan%5D%5D%20%5B%5Bwasu%5D%5D%20%5B%5Bza,wa%5D%5D%20%5B%5Bda%5D%5D%20%5B%5Bmakamantansu%5D%5D.
https://hausa.leadership.ng/ilimin-sarrafa-kwamfuta-wajibi-ne-a-wannan-zamanin/