#
|
Hadith 1
|
Hadisi na ɗaya
|
1
|
On the authority of Ameer ul-Mu’mineen (the Commander of the Faithful), Aboo Hafs `Umar ibn al-Khattaab radiAllaahu anhu, who said: I heard the Messenger of Allaah ﷺََ say:
|
An karɓo daga sarkin muminai, Baban Hafs, Umar ɗan Alkhaɗɗabi Allah ya yarda da shi yace: Na ji Manzon Allah ﷺََ yana cewa:
|
2
|
Actions are but by intentions and every man shall have only that which he intended.
|
“Dukkan aiyyuka suna tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya;
|
3
|
Thus he whose migration (Hijrah to Madeenah from Makkah) was for Allaah and His Messenger, his migration was for Allaah and His Messenger,
|
Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da Manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa.
|
4
|
and he whose migration was to achieve some worldly benefit or to take some woman in marriage, his migration was for that for which he migrated.
|
Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce dazai same ta ko kuma wata matar da zai aure ta to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa.
|
5
|
It is related by the two Imaams of the scholars of Hadeeth, Aboo `Abdillaah Muhammad ibn Ismaa`eel ibn Ibraheem ibn al-Mugheera ibn Bardizbah al-Bukhaaree
|
Shugabannin maluman da suka rubuta littatafan hadisai ne suka ruwaito shi; Wato: Baban Abdullahi Muhammadu ɗan Isma’ila ɗan Ibrahima ɗan Almugiyrah ɗan Bardizbah,(AlBukhariyy), A cikin ingantattun littatafansu [Sahihul Bukhariyy, [lamba: 1]
|
6
|
and Aboo-l-Husain Muslim ibn al-Hajjaaj ibn Muslim al-Qushairee an-Naisaabooree, in their two Saheehs, which are the soundest of compiled books [i.e. the most truthful books after the Book of Allaah, since the Qur’aan is not ‘compiled’].
|
Da kuma Abul Husaini Muslimu ɗan Alhajjaju ɗan Muslimu, Alqushairiyyu Annaisaburiyyu. (acikin Sahihu Muslim), [lamba: 1907], waɗanda kuma sune mafi ingancin littatafan da aka rubuta.
|
7
|
|
|