Sashen Hausa na BBC ku ka kama akan mita ashirin da ɗaya da ashirin da biyar da kuma mita talatin da ɗaya. Ko kuma a shafin mu na internet a BBCHausa.com da kuma manhajar TuneIn a BBC Hausa. Masu sauraro, Badriya Tijjani Kalarawi ke muku sallama a cikin shirin mu na hantsi.
Jiragen yaƙin Faransa sun kai sabbin hare-hare a Cadi (Chad) akan abinda suka ce. Wani ayari ne na 'yan bindiga ɗauke da manyan makamai. Wataƙila da [unintelligible] hamɓarar da gwamnatin Cadi.
Tarayar Turai ta ce masu sanya idanunta kan zaɓukan Najeriya za su je ƙasar, dukkuwa, da barazanar da gwamnan jihar Kaduna ya yi akan zuwan su.
Ko ƙanƙani ba shi da nufin ya nemi a jima wani ko a hallaka wani ko ɗan Najeriya ko ɗan ƙasar waje dangane da harkar zaɓe. Magana ce yake yi da ta shafi kare kishin ƙasa da mutincin ƙasar sa ta Nigeria. --wakilin gwamnatin tarayya Garba Shehu
Sojan Zimbabwe sun ce sun kammala aikin da suka yi na samar da kwanciyar hankali da bin doka a ƙasar.
Za mu ji wani mataki da gwamnatin Amurka ta ɗauka akan Kamaru.
Niger: The Minister of State for the Interior Mohamed Bazoum ya jagoranci wata tawaga da ta haɗa da 'yan majalisu da manyan jami'an ƙasar zuwa garin Adze* na cikin gwadomar Abalak da ke jihar Tahoua domin tattaunawa da al'ummar yankin kan abinda ya shafi harkokin tsaro da zaman lafiya na yankin.
Nigeria: Rahotanni sun tabbatar da cewa wata gobara ta rutsa da wasu 'yan gudun hijira a sansanin Munguno, Borno. Za'a ji ra'ayin masana dangane da wannan lamari.
Nigerians living in Cote D'voire: 'Yan Nijar da ke rayuwa a ƙasar Cote D'voire sun koka kan yadda suke samun matsala da katin ɗan ƙasa. Ganin cewa muhukuntan na Niger sun ƙi sabunta katin da ta yi daidai da zamani. Lamarin da ya sanya suke fuskantar matsala na gudanar da mu'amalarsu a ƙasar ta Cote D'voire.
Morocco: Hukumomi a ƙasar Morocco sun sanar da janyewar ƙasar daga cikin gurundunar ƙawancen Saudiya a ƙasar Yemen tare da kiran jakadan ƙasar daga birnin Riyadh. Ko me hakan ya ke nufi, za mu ji ra'ayin masana.
Shirin Ko Kun San da Tahir Amir Rajiyola*.
Shiri na musamman (Special Report) dangane da zagayowar ranar nasarar juyin-juya halin Musulunci na Iran.
Shiri na Matambayi Baya Ɓata da Muhammad Auwwal Bauchi.