Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Theme and Subject Matter

In this Surah, the people have been warned of the evil consequences of worship of the world because of which they spend their lives acquiring more and more worldly wealth, material benefits and pleasures, and position and power, and in vying with one another and bragging and boasting about their acquisitions until death. This one pursuit has occupied them so much that they are left with no time or opportunity for pursuing the higher things in life. After warning the people of its evil end they have been told as if to say: "These blessings which you are amassing and enjoying thoughtlessly, are not mere blessings but are also a means of your trial. For each one of these blessings and comforts you will surely be called to account in the Hereafter."

Central Theme

Save yourself from materialism and takathur! Or else you will go to hell. Prepare for the grave and akhirah! Do not be ingrate.

Ayat 1 - 5: Will you be occupied by the duniya until you enter the grave?

Ayat 6 - 8: The principle reason for takathur is the absence of belief in jannah and jahannum.

Mabuɗin Surar

Sunanta <> Its Name

Wannan Sura ta fi shahara da 'Suratut Takasu' kamar yadda ya zo a cikin yawancin litattafan tafsiri da masahifu. Ana kuma kiran ta da 'Suratu Al-Hakum' kamar yadda ya zo a cikin Sahihul Bukhari. Ya zo cewa sahabban Manzon Allah (SWT) suna kiran ta da 'Suratul Maƙbara' domin a cikinta ne kawai wannan lafazin 'Al-Maƙabir' watau maƙabartarsu ya zo.

Sanda aka saukar da ita <> When it was revealed

Yawancin malamai suna ganin cewa surar Makkiya ce. <> Most scholars think it's a Makkan sura.

Jerin Saukarta <> Order of revelation

Ita ce Sura ta goma sha shida (16) a jerin saukar surorin Alƙur'ani. Ta sauka bayan Al Kausar kafin Al Ma'aun.

Babban Jigonta <> Its Central Theme

Tana jan kunnen mutane a kan kada su bari duniya ta shagaltar da su har su manta da lahira.

Daga Cikin Abubuwan Da Ta Kunsa Akwai

  1. Gargadin mutane da tsawatar musu a kan cewa kada su bari duniya da kyale-kyalenta na tara dukiya da 'ya'ya (wealth and children) su shagaltar da su su daina tunanin mutuwa da ranar lahira har mutuwar ta zo musu ba zato ba tsammani su wayi gari a makabarta.
  2. Kwadaitar da su a kan su yi wa kansu tanadin abin da zai kubutar da su daga wutar Jahannama.
  3. Tunatar da su cewa za a tashe su a ranar alkiyama kuma za a yi musu hisabi game da ni'imar da aka yi musu ba su gode ba.

Fassara da tafsirin Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo

1. Alfahari da yawan ('ya'ya da dukiya) ya shagaltar da ku.

2. Har kuka (mutu kuka) ziyarci kaburbura.

3. A'aha! (haka bai kamace ku ba) da sannu za ku sani.

4. Sannan a'aha, da sannu za ku sani.

5. Tabbas da za ku yi sani, sani na hakika.

6. Tabbas hakika za ku ga wutar Jahima.

7. Kuma ma tabbas hakika za ku gan ta gani da ido na hakika.

8. Sannan kuma tabbas hakika za a tambaye ku a wannan ranar game da ni'imomin (da kuka mora a duniya).

Tafsiri:

Allah (SWT) ya bude Surar da tsawatar wa mutane game da yadda alfahari da tara 'ya'ya da dukiya ya shagaltar da su daga bin Allah (), suka doge a kan haka har sai da suka mutu suka shiga kaburburansu.

An karbo daga Abu Huraira (4) ya ce: Manzon Allah (s) ya ce: "Ba talauci nake ji muku tsoro ba; ina ji muku tsoron alfahari da tara dukiya; ba kuma kuskure nake ji muku tsoro ba, ina ji muku tsoron ganganci ne." [Ahmad #8074 da Ibn Hibban #3222 da Hakim #3970].

Sannan Allah (3) ya nuna musu cewa bai dace a ce irin wannan mummunar dabi'a ta alfahari da tarin dukiya ko 'ya'ya ta dauke musu hankali ba har su kai ga barin da'ar Allah, domin ba da jimawa ba za su san rashin amfanin abin da suka yi. Allah (*) ya tabbatar musu da cewa, tabbas da sun san za a tashe su a gaban Allah, ya yi musu hisabi da sakayya a kan ayyukansu, to da lalle ba su shagala da tarin dukiya da alfahari da 'ya'ya ba.

Sai kuma Allah (3) ya tabbatar musu cewa lalle babu makawa sai sun ga wuta a ranar alkiyama, gani kuma na hakika wanda babu kokwanto ko kadan a cikinsa.

Ya kuma ya tabbatar musu cewa lalle ba makawa sai an tambaye su a ranar alkiyama game da ni'imomin da Allah () ya yi musu, kamar ni imar lafiya ko ta wadata da makamantansu.

An karbo daga Abu Huraira (4) ya ce: Manzon Allah (@) ya ce: "Bawa yakan ce: "Dukiyata, dukiyata', alhali abu uku ne kawai nasa a cikin dukiyarsa; abin da ya ci ya karar, da tufar da ya sa ya kashe, da abin da ya bayar sadaka ya yi wa kansa ajiya. Duk abin da ba wadannan ba, to zai tafi ne ya bar wa mutane." [Muslim #2959].

An karbo daga Abdullahi dan Shikkhir () ya ce: Na je na sami Manzon Allah () yana karanta wannan Surar, yana cewa: Dan adam yana cewa, 'Dukiyata, dukiyata', shin kana da wani abu ne a dukiyarka in ban da wanda ka ci ka karar, ko ka sanya a jikinka ka kashe, ko ka yi sadaka ka zartar?" [Ahmad # 16305 da Muslim #2958].

An karbo daga Abu Huraira (+) ya ce: Manzon Allah (3) ya ce: "Farkon ni'imar da za a tambayi bawa a kanta ranar alkiyama shi ne za a ce masa: "Yanzu ashe ba mu ba ka lafiyar jiki ba? Muka kuma kosar da kai da ruwan sanyi?" [Tirmizi # 3652 da Ibnu Hibban #7364 da Al-Hakim #7203].

An karbo daga Abu Huraira () ya ce: Wata rana Manzon Allah () ya fita sai ya hadu da Abubakar da Umar a hanya, sai ya tambaye su ya ce: "Me ya fito da ku a wannan lokaci daga gidajenku?" Sai suka ce: "Yunwa, ya Manzon Allah." Sai ya ce: "Na rantse da Allah, abin da ya fito da ku ni ma shi ne ya fito da ni, don haka ku taso." Sai suka tashi, sai suka zo gidan wani mutumin Madina amma sai suka samu ba ya nan. Lokacin da matarsa ta ga Manzon Allah (@) sai ta ce: "Maraba lale-lale." Sai Manzon Allah (a) ya tambaye ta ina mai gidanta ya tafi? Sai ta amsa da cewa: "Ya tafi ya nemo mana ruwan sha." Suna tsaye sai ga wannan mutum ya dawo. yana ganin Manzon Allah (s) da sahabbansa su biyu sai ya ce: "Na gode wa Allah, a yau babu wanda ya kai ni manyan baki." Sai nan take ya fita ya je ya samu hantsar dabino burarre da nunanne, sai ya ce: "Ku ci wannan." Sai ya dauki wuka, sai Manzon Allah (s) ya ce masa: "Kada ka kuskura ka yanka dabbar tatsa." Sai ya yi musu yanka suka ci naman wannan akuya suka ci dabino, suka sha nono. Bayan sun ci sun koshi sun sha ruwa sun yi nak, sai Manzon Allah (*) ya ce wa Abubakar da Umar: "Na rantse da wanda raina yake a hannunsa, tabbas sai an yi muku tambaya game da wannan ni'imar a ranar alkiyama." [Muslim #2038].

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

1. Tara dukiya ba shi ne abin zargi ba; abin zargi shi ne dukiya ko 'ya'ya ko matsayi su shagaltar da mutum ya manta da da'ar Allah da tunanin lahira.

2. Zaman kabari zama ne na wucin-gadi ba na har abada ba, shi ya sa aka kira shi da ziyara ba zama ba, wannan ya tabbatar da tashi bayan mutuwa domin yin hisabi da sakamako a kan ayyuka.

3. Ilimi na hakika wanda yake ratsa zuciya shi ne ilimin da yake hana bawa yin alfahari da yawan abin da na duniya, yake zaburar da shi domin yin aikin da zai amfane shi a lahira. ya mallaka

4. Ranar alkiyama rana ce da za a yi wa mutane tambaya a kan ni'imar da aka ba su a duniya.

Pages in category "Quran/102"

Pages in category "Quran/102"

The following 11 pages are in this category, out of 11 total.