More actions
Sababbin kalmomi a Hausa: Fassarar wasu kalmomin kwamfyuta (kashi na uku) via Bakandamiya [1]
- accessories = mataimaka
- active window = taga/alkuki mai aiki/mai rai
- address book = littafin adireshi
- anti-virus = riga-kafi
- arrange = jera/tsara
- backup = gida biyu/tanadi
- bold = kaurara
- border = iyaka
- break = dakata/daukewa
- bug = cuta
- change = sauya/canja
- chart = lissafi a zane/giraf
- clip art = zane/hoto
- clipboard = kilibodi
- columns = layin tsaye
- compatible = mai jituwa
- content = makunshi
- crash = lalacewa
- create = kirkiri
- date and time = kwanan wata da lokaci
- debugging = waraka
- dialog box = zauren akwatun bayani
- dictionary = kamus
- document name = sunan aiki
- double density = tagwayen rumbu
- download = juya daga wata kwamfyuta/kwasowa
- draw = zana
- end notes = karin bayani (na karshe)
- envelope = ambulan
- font size = girman rubutu
- font style = salon rubutu
- font = sigar rubutu
- footer = kanun kasa
- footnotes = hashiyar bayani
- format = tsari
- header = kanun sama
- high density (diskbel) = babban rumbu
- highlight = haskaka/nuni
- hyphenation = karan dorantawa
- icons = alamomi
- initialize = shirya/soma
- input = shigarwa
- insert = ratsa
- install = saka, dora
- italic = tafiyar tsutsa
- kill = goge/shafe
- label = shaida/alama
- look up = nemo
- margin = iyakaci
- multimedia = masilimant
- object = abu
- online = kan-layi
- output = fitarwa
- page break = raba shafi
- page layout = zubin shafi
- page number = lambar shafi
- paginate = yi shafi/shafinta
- paint = fenti/shafa
- paragraph = sakin layi
- password = makulli
- press = matsa/danna
- random acess memory (ram) = ram
- read only memory (rom) = rom
- recycle bin = kwandon shara
- rows = layin kwance
- ruler = rula
- scandisk = likitan rumbu
- search = dubo/binciko
- shadow = inuwantawa
- shift = gusar
- shutdown = kashe/rufe
- sleep = huta, kwanta
- soft copy = danyen rubutu
- space = fili
- special character = alama ta musamman
- spelling = babbaku (karatun) hajjatu
- spread sheet = teburin lissafi/jadawalin lissafi
- start = fara
- startup diskette = kundin tayarwa
- status line = layin bayani
- store = adana
- table = tebur/jadawali
- tabs = matsawa/alawus
- thesaurus = sisaros
- tools = kayan aiki
- underline = jan-layi
- untitled = marar suna/kurma
- verify = tantance
- volume = murya
- window = taga/wundo/alkuki
- word art = rubutu a siffar zane
- word count = kirgen kalmomi
- zoom = kusanto