Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

40 Hadiths in English <> Hadisai 40 da Hausa

Hadith 1 <> Hadisi na 1

# Hadith 1 Hadisi na ɗaya
1 On the authority of Ameer ul-Mu&#8217;mineen (the Commander of the Faithful), Aboo Hafs `Umar ibn al-Khattaab radiAllaahu anhu, who said: I heard the Messenger of Allaah ﷺََ say: An karɓo daga sarkin muminai, Baban Hafs, Umar ɗan Alkhaɗɗabi Allah ya yarda da shi yace: Na ji Manzon Allah ﷺََ yana cewa:
2 Actions are but by intentions and every man shall have only that which he intended. “Dukkan aiyyuka suna tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya;
3 Thus he whose migration (Hijrah to Madeenah from Makkah) was for Allaah and His Messenger, his migration was for Allaah and His Messenger, Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da Manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa.
4 and he whose migration was to achieve some worldly benefit or to take some woman in marriage, his migration was for that for which he migrated. Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce dazai same ta ko kuma wata matar da zai aure ta to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa.
5 It is related by the two Imaams of the scholars of Hadeeth, Aboo `Abdillaah Muhammad ibn Ismaa`eel ibn Ibraheem ibn al-Mugheera ibn Bardizbah al-Bukhaaree Shugabannin maluman da suka rubuta littatafan hadisai ne suka ruwaito shi; Wato: Baban Abdullahi Muhammadu ɗan Isma’ila ɗan Ibrahima ɗan Almugiyrah ɗan Bardizbah,(AlBukhariyy), A cikin ingantattun littatafansu [Sahihul Bukhariyy, [lamba: 1]
6 and Aboo-l-Husain Muslim ibn al-Hajjaaj ibn Muslim al-Qushairee an-Naisaabooree, in their two Saheehs, which are the soundest of compiled books [i.e. the most truthful books after the Book of Allaah, since the Qur’aan is notcompiled’]. Da kuma Abul Husaini Muslimu ɗan Alhajjaju ɗan Muslimu, Alqushairiyyu Annaisaburiyyu. (acikin Sahihu Muslim), [lamba: 1907], waɗanda kuma sune mafi ingancin littatafan da aka rubuta.
7 One day while we were sitting with the Messenger of Allaah ﷺََ there appeared before us a man whose clothes were exceedingly white and whose hair was exceedingly black; Wata rana muna wurin Manzon Allah ﷺََ, Sai wani mutum ya zo mana mai tsananin farin tufafi,

Hadith 2 <> Hadisi na 2

# Hadith 2 Hadisi na biyu
1 Also on the authority of `Umar (radi Allaahu ‘anhu), who said: An ruwaito daga Umar Allah ya yarda da shi yace:
2 One day while we were sitting with the Messenger of Allaah ﷺََ there appeared before us a man whose clothes were exceedingly white and whose hair was exceedingly black; Wata rana muna wurin Manzon Allah ﷺََ, Sai wani mutum ya zo mana mai tsananin farin tufafi kuma mai tsananin baqin gashi;
3 no signs of journey were to be seen on him and none of us knew him. He walked up and sat down in front of the Prophet ﷺََ, babu wata alamar tafiya a tattare da shi, har ya zauna kusa da Annabi ﷺََ.
4 with his knees touching against the Prophets ﷺََ and placing the palms of his hands on his thighs he said: Sai ya jingina guiwoyinsa zuwa guiwoyinsa, ya kuma ɗora tafukansa akan cinyoyinsa, yace:
5 “O Muhammad, tell me about Islam. Ya Muhammadu ﷺََ , bani labari akan Musulunci?
6 The Messenger of Allaah ﷺََ said: Islaam is to testify that there is no deity worthy of worship but Allaah and Muhammad is the Messenger of Allaah, manzon allah ﷺََ Yace :Ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne,
7 to perform prayers, to give zakaah, to fast in Ramadaan, and to make the pilgrimage to the House if you are able to do so. kuma ka tsayar da salla, kuma ka bada zakka, kuma ka yi azumin watan ramadana, kuma ka yi hajjin ɗaki; idan ka samu hanyar zuwa gare shi.
8 He said: “You have spoken rightly”; and we were amazed at him asking him and saying that he had spoken rightly. He (the man) said: “Tell me about Eemaan. Sai yace: ka yi gaskiya Sai muka yi mamakinsa yana tambayarsa kuma yana gaskata shi! Sai yace: ka bani labari akan imani?
9 He (the Prophet, ﷺََ ) said: “It is to believe in Allaah, His Angels, His Books, His Messengers, and the Last Day, and to believe in divine destiny (qadr), both the good and the evil of it. Yace: Ka yi Imani da Allah da Mala’ikunsa da littatafansa da Manzanninsa da ranar ƙarshe, kuma ka yi imani da qaddara na alkhairinsa da na sharrinsa.
10 He said: “You have spoken rightly.” He (the man) said: “Then tell me about Ihsaan.” Yace: Kayi gaskiya. Yace: To ka bani labari akan “ihsani”?
11 He (the Prophet, ﷺََ ) said: “It is to worship Allaah as though you see Him, and if you do not see Him, then (knowing that) truly He sees you.” Sai yace: Shine ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa to shi yana ganinka.
12 He said: “Then tell me about the Hour.” He said: “The one questioned about it knows no better than the questioner.” Yace: To ka bani labari akan qiyamah? Sai yace: Wanda ake tambayarsa akanta bai fi wanda yayi tambayar sanin lokacinta ba.
13 He said: “Then tell me about its signs.” Sai yace: To ka bani labara kan alamominta?
14 He said: “That the slave-girl will give birth to her mistress, and that you will see barefooted, naked destitute shepherds competing in constructing lofty buildings.” Sai yace: Baiwa ta haifi uwar gijiyarta, kuma zaku ga marasa takalma tsiraru masu kiyon dabbobi suna yin gini masu tsayi.

Source

Pages in category "40 Hadiths"

The following 10 pages are in this category, out of 10 total.