Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Category:99 names of Allah: Difference between revisions

Category page
Line 39: Line 39:
# '''Al Hakam (الحكم)''' The Judge, the Arbitrator; Allah Maɗaukaki shi ne wanda hukuncinsa yake zarcewa kan komai, babu mai juyar da shi. Mai hukunci. [https://www.facebook.com/161152733904794/videos/477980990077232]
# '''Al Hakam (الحكم)''' The Judge, the Arbitrator; Allah Maɗaukaki shi ne wanda hukuncinsa yake zarcewa kan komai, babu mai juyar da shi. Mai hukunci. [https://www.facebook.com/161152733904794/videos/477980990077232]
# '''Al 'Adl (العدل)''' The Utterly Just; Allah Maɗaukaki shi ne tsarkakakke ga barin zalunci ko danniya. Allah babu zalunci ko danniya a cikin lamarinSa. Mai adalci.  
# '''Al 'Adl (العدل)''' The Utterly Just; Allah Maɗaukaki shi ne tsarkakakke ga barin zalunci ko danniya. Allah babu zalunci ko danniya a cikin lamarinSa. Mai adalci.  
# '''Al Latif (اللطيف)''' The Subtly Kind; Allah Maɗaukaki shi ne Masani da abin da dukkan abubuwan da suke ɓoye, kuma shi ne wanda yake tausasawa bayinSa ta inda ba su sani ba. Shi yake tsare musu abubuwan da zai taimakesu da mas'alarsu ta rayuwa ta inda basa zato, kuma basa tsammani, kuma Shi ne wanda yake ɓoye ƙarshen al'amura a cikin afkuwar kishiyoyinsu lokacin da suke afkuwa. Mai tausasawa.
# '''[[99 names of Allah/Al-Lateef (The Subtle)|Al Latif (اللطيف)]]''' The Subtly Kind; Allah Maɗaukaki shi ne Masani da abin da dukkan abubuwan da suke ɓoye, kuma shi ne wanda yake tausasawa bayinSa ta inda ba su sani ba. Shi yake tsare musu abubuwan da zai taimakesu da mas'alarsu ta rayuwa ta inda basa zato, kuma basa tsammani, kuma Shi ne wanda yake ɓoye ƙarshen al'amura a cikin afkuwar kishiyoyinsu lokacin da suke afkuwa. Mai tausasawa.
# '''Al Khabir (الخبير)''' The All Aware; Allah Maɗaukaki shi ne wanda babu wani abu da yake iya ɓoye masa. Masanin halittarsa.
# '''Al Khabir (الخبير)''' The All Aware; Allah Maɗaukaki shi ne wanda babu wani abu da yake iya ɓoye masa. Masanin halittarsa.
# '''Al Halim (الحليم)''' The Forbearing, the Indulgent; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake yin gafara, bayan kuma ya suturta.  Kuma ba ya gaggawar kamu ga wanda ta saɓe shi, haka kuma baya gaggawar ukuba, sannan kuma yana kau da kai ga dukkanin kuskure da ɗan Adam zai yi, kuma yana yiwa mai yin saɓo jinkiri har sai lokacin da zai tuba. Mai juriya.
# '''Al Halim (الحليم)''' The Forbearing, the Indulgent; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake yin gafara, bayan kuma ya suturta.  Kuma ba ya gaggawar kamu ga wanda ta saɓe shi, haka kuma baya gaggawar ukuba, sannan kuma yana kau da kai ga dukkanin kuskure da ɗan Adam zai yi, kuma yana yiwa mai yin saɓo jinkiri har sai lokacin da zai tuba. Mai juriya.

Revision as of 08:45, 21 April 2022

Sunayen Allah Casa'in da Tara <> Ninety-nine names of Allah

Allah has ninety-nine names. Whoever memorizes them will enter Paradise. -Bukhari 2736 [1]
File:059 Hasr-Who is Allah.mp3 Quran/59/22, Quran/59/23, Quran/59/24
File:059 Hasr-Who is Allah Recited by Shaykh Nourin radi allahu anhu no translation.mp3
File:059017-24_in_Hausa.mp3

The 99 Names of God (أسماء الله الحسنى), ʾasmāʾu llāhi lḥusnā) also known as The 99 attributes of Allah, according to Islamic tradition, are the names of God revealed by the Creator(God) in the Qur'an.

The 99 Names of God (Allah) according to the tradition of Islam are:

  1. Ar Rahman (الرحمن) The All Merciful (mai jin ƙai); The Compassionate (mai tausayi, mai juyayialhini), The Beneficent (Mai rahama) The Infinitely (rashin iyaka, mai yawa) Good; Allah mai yalwar Rahama ne wacce ta game bayi gaba ɗayansu, Musulmi ko Kafiri, Me biyayya ko me saɓo. Mai jin kan muminai da kafirai a duniya.
  2. Ar Rahim(الرحيم) The Most Merciful; Mai jin ƙai, Allah ne mai madauwamiyar Rahama, wanda in ba a roƙe shi ba, sai yayi azaba. Wanda idan bala'i ya sami abin halitta sai ya bashi mafita. Mai jin kan muminai kadai a lahira.
  3. Al Malik (الملك) The King, The Sovereign Lord (mamallakin sarki ubangiji); Allah ne ma'abocin mulki isasshe wanda ba shi da buƙata a cikin halittarsa, kuma mulkin nasa ba ya karewa, kuma shi ne wanda makarfafar komai take ikonSa.
  4. Al Quddus (القدوس) The Most Holy, Pure (mai tsarki); Allah shi ne mai tsananin tsarkaka daga dukkan tawaya ko duk abin da mabarnata suke danganta masa. Tsarkakken sarki.
  5. As Salam (السلام) The Source (mafari, majiya, asali, tushe, salsala, masomi) of Peace (zaman lafiya, sulhu, kwanciyar hankali, amana, aminci, salama) and Blessing; The Flawless (babu/rashin aibi, marasa aibu); Allah shi ne wanda Zatinsa da aikinSa suke kuɓuta daga dukkan tawaya, shi ne kuma me kuɓatar da bayi daga dukkan wata halaka, shi ne me tabbatar da aminci tsakanin bayinSa. Mai amintarwa.
  6. Al Mu'min (المؤمن) The Guarantor; The Guardian (waliyi, mai kula da, majiɓinci, mutumin dake tsaran lafiyan wani mutum) of Faith (addini, amana/amanna, bangaskiya, tauhidi) The Faithful (amintacce, na Imani); Wanda ya amintar da bayinSa daga dukkanin abin tsoro, babu kwanciyar hankali sai daga Ubangiji, me gasgata kansa da kansa. Duk mai neman goyon baya a wajen Ubangiji to ya rinƙa yawaita karanta Ya Mu'minu! Amintaccen sarki.
  7. Al Muhaymin (المهيمن) The Guardian, the Preserver; Allah shi ne mahalicci mai gani ga duk aikin bayinSa. Mai shaida aikin bayi.
  8. Al Aziz (العزيز) The Almighty, the Self Sufficient; Allah shi ne Buwayayye shi ne mai ƙarfin da babu wanda zai iya tankwara shi, shi ne wanda ya kadaita da ɗaukakarsa. Mabuwayi.
  9. Al Jabbaar (الجبار) The Powerful, the Irresistible; Allah shi ne wanda komai dole ne ya ƙasƙanta a gabansa. Maɗaukaki akan dukkan halittarSa. Shi ne mai karya ƙashin bayan masu taurin kai. Shi ne wanda iradarSa ta ratsa komai. Amma Shi kuma ba wata Irada da take iya ratsa Shi. Komai mutum zai yi sai in ya dace da abin da yake so, in bai dace ba shi ke nan yayi asara. Mai gyara bayinsa. Mai gyara bayinsa.
  10. Al Mutakabbir (المتكبر) The Tremendous; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya kadaita da girma da ɗaukaka, ba wani girma ban da nasa. Mai girman girma.
  11. Al Khaaliq (الخالق) The Creator; Allah shi ne mai samar da komai daga babu. Abin da babu shi sai ya samar da shi ba tare da yaga samfu ba a gurin wani. Mahaliccin halitta.
  12. Al Baari (البارئ) The Maker; Allah Albari'u mai kagen halitta, wanda bai gani a gurin kowa ba. Shi ne wanda yake ba kowane abin halitta siffarsa. Tsawo ko gajarta, kauri ko sirintaka, a tsaye ko a kife, dunƙulalle ko miƙaƙƙe, mai motsi ko sandararre. Mahalicci.
  13. Al Musawwir (المصور) The Fashioner of Forms; Allah Maɗaukaki shi ne mai kayatar da siffar ababen halitta. Shi ne wanda zai suranta abu kuma ya kayatar da shi. Mai suranta mahaifa.
  14. Al Ghaffaar (الغفار) The Ever Forgiving; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake sutura zunubai na bayinSa. Kuma yake shafesu da tuba. Mai gafara.
  15. Al Qahhaar (القهار) The All Compelling Subduer; Allah Maɗaukaki shi ne mai rinjaye, wanda ba wanda zai iya jurewa ukubarsa. Duk wanda ya ɗorawa, bai isa yace yayi taurin kai ko yai jarunta ko dauriya akan abinda ya ɗora masa ba. Mai rinjaye.
  16. Al Wahhaab(الوهاب) The Bestower; Allah Maɗaukaki shi ne mai maɗauwamiyar baiwa, Shi kullum bayarwa yake, baya hanawa. Sannan yana bawa wanda yake da buƙata abinda yake buƙata. Amma ba dan wani buri da Allah yake da shi ba, ba kuma dan musaya da za ayi masa ba, kawai shi bayarwa yake. Mai kyauta.
  17. Ar Razzaaq (الرزاق) The Ever Providing; Allah Maɗaukaki shi ne mai arzurtawa, kuma shi ne me halittar arzikin gaba ɗaya, Shi ne mai arzurta jiki da abinci, Shi ne kuma yake arzurta rayuka ko ruhi da sani na Allah Subhanahu Wata'ala. Mai azurtawa.
  18. Al Fattaah(الفتاح) The Opener, the Victory Giver; Allah Maɗaukaki shi ne mai buɗe taskokin rahama ga halittarsa, kuma Shi ne wanda ya buɗe zukatan bayi muminai, da sani kuma ya buɗewa masu saɓo ƙofa ta gafara in sun nemi gafara zai gafarta musu. Mai budawa bayi.
  19. Al Alim (العليم) The All Knowing, the Omniscient; Masani wanda babu abin da yake ɓoye a gare shi, na nesa ko kusa. Shi ne wanda Ya san abin da ya kasance da abin da yake kasancewa da abin da ba zai kasance ba. See: dua/Al-Alim The Knower
  20. Al Qaabid (القابض) The Restrainer, the Straightener; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake miƙa mulki hannun wanda yaso. Shi ne wanda yake karɓar rawuka yayin mutuwa, kuma shi yake tashinta gobe Alƙiyama. Mai damkewa.
  21. Al Baasit (الباسط) The Expander, the Munificent; Allah Maɗaukaki shi ne mai shimfiɗawa, wato wanda yake yalwata arziki ga wanda yaso daga cikin bayinSa. Mai shimfida arziki.
  22. Al Khaafid (الخافض) The Abaser; Allah Maɗaukaki shi ne yake ƙasƙantar da wanda ya so. Musamman ma wanda yake da jin ƙai, mai alfahari, to sai ya yadda shi ba wani ba ne. Mai sunkuyarwa.
  23. Ar Raafi' (الرافع) The Exalter; Allah Maɗaukaki shi ne yake ɗaga darajar muminai ya basu rinjaye akan maƙiyansu, kuma shi ne yake ɗaga darajar wanda yaso ya kuma ɗaukaka shi duk duniya aso shi. Mai daukakawa.
  24. Al Mu'izz (المعز) The Giver of Honor; Allah Maɗaukaki shi ne me buwayar da wanda ya bi shi, shi ne kuma yake bada mulki ga wanda ya so. Mabuwayin sarki.
  25. Al Muzil (المذل) The Giver of Dishonor; Allah Maɗaukaki shi ne mai ƙasƙantarwa. Shi yake ƙasƙantar da maƙiyansa ta hanyar hanasu gane Ubangiji, kuma yake jifan waɗanda suka saɓe shi da ƙasƙanci da wulaƙanci. Mai kaskantarwa.
  26. Al Sami' (السميع) The All Hearing; Allah Maɗaukaki shi ne mai riskar dukkan abin ji, sannan babu wani abu na ji da yake tsere masa. Jin roƙon wani ko tasbihin wani ko zikirin wani ba ya shagalar da shi ga barin jin kira ko zikiri ko tasbihin sauran bayinsa. Mai ji.
  27. Al Basir (البصير) The All Seeing; Allah Maɗaukaki shi ne yake Mahalicci, kuma yana ganin komai. Duka abin da suke cikin Sammai Maɗaukaka da abinda yake cikin Ƙasa da abinda yake tsakanin Sama da Kasa da abinda yake ƙarƙashin Ƙasa duk ba wanda yake ɓuya a gare shi. Mai gani.
  28. Al Hakam (الحكم) The Judge, the Arbitrator; Allah Maɗaukaki shi ne wanda hukuncinsa yake zarcewa kan komai, babu mai juyar da shi. Mai hukunci. [2]
  29. Al 'Adl (العدل) The Utterly Just; Allah Maɗaukaki shi ne tsarkakakke ga barin zalunci ko danniya. Allah babu zalunci ko danniya a cikin lamarinSa. Mai adalci.
  30. Al Latif (اللطيف) The Subtly Kind; Allah Maɗaukaki shi ne Masani da abin da dukkan abubuwan da suke ɓoye, kuma shi ne wanda yake tausasawa bayinSa ta inda ba su sani ba. Shi yake tsare musu abubuwan da zai taimakesu da mas'alarsu ta rayuwa ta inda basa zato, kuma basa tsammani, kuma Shi ne wanda yake ɓoye ƙarshen al'amura a cikin afkuwar kishiyoyinsu lokacin da suke afkuwa. Mai tausasawa.
  31. Al Khabir (الخبير) The All Aware; Allah Maɗaukaki shi ne wanda babu wani abu da yake iya ɓoye masa. Masanin halittarsa.
  32. Al Halim (الحليم) The Forbearing, the Indulgent; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake yin gafara, bayan kuma ya suturta. Kuma ba ya gaggawar kamu ga wanda ta saɓe shi, haka kuma baya gaggawar ukuba, sannan kuma yana kau da kai ga dukkanin kuskure da ɗan Adam zai yi, kuma yana yiwa mai yin saɓo jinkiri har sai lokacin da zai tuba. Mai juriya.
  33. Al 'Azim (العظيم) The Magnificent, the Infinite; Allah Maɗaukaki shi ne mai girman da babu wanda ya kai shi, bare ya fi shi girma, sannan hankali bai isa ya siffanta shi ba. Haka ma gani ko basira ta ƙwaƙwalwa bata isa ta faɗi hakikaninsa ba. Mai girman daraja.
  34. Al Ghafur (الغفور) The All Forgiving; Allah Maɗaukaki mai yawan gafara ne, kuma mai karɓar hanzari ne. Mai gafartawa bayinsa.
  35. Ash Shakur (الشكور) The Grateful or The Ever-Thankful [3]; Allah Maɗaukaki shi ne mai yiwa bayinsa muwafuka su godewa irin ni'imar da yayi musu, sannan kuma shi ne wanda yake sakamako akan 'yar ƙanƙanuwar ɗa'a, ya bada gwaggwaɓar daraja. Sannan kuma shi ne zaka yi ƙanƙanin aiki sai ya baka ni'imar da bata da iyaka. Sarki abin godewa.
  36. Al Ali (العلي) The Most High, The Sublimely Exalted; Allah Maɗaukaki shi ne mai ɗaukaka daraja ta bayinsa. Shi ne Maɗaukaki a irin darajar da yake da ita, babu wani mai darajar da zai kai tasa.
  37. Al Kabir (الكبير) The Great; Allah Maɗaukaki shi ne mai girma a cikin girman nasa. Yafi gaban wata gaba wacce take ji ko gani ko shaka ko dadado ko shafa ko hankali su riske shi. Mai girman lamari.
  38. Al Hafiz (الحفيظ) The Preserver; Allah Maɗaukaki shi ne mai kiyayewa, kuma mai sanin dukkan ayyukan bayi. Shi ne mai tantance dukkan ayyukan bayi, baya barin sa ya ɓata. Mai kiyayewa.
  39. Al Muqit (المقيت) The Nourisher; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake bawa halitta gaba ɗayanta abinci. Mai ciyarwa.
  40. Al Hasib (الحسيب) The Reckoner; Allah Maɗaukaki shi ne mai yiwa bayinsa hisabi akan dukkanin ayyukan da suke yi, babba da ƙarami. Mai iyakancewa.
  41. Al Jalil (الجليل) The Majestic; Allah Subhanahu wata'ala shi ne Maɗaukaki wanda yake da girma, ya ɗaukaka a bisa abin da bai dace da shi ba. Shi ne wanda yake cikakke a zatinsa da siffarsa da ayyukansa, babu tawaya a gare shi. Mai girman girma.
  42. Al Karim (الكريم) The Bountiful, the Generous; Allah Maɗaukaki shi ne mai yawan baiwa, me madauwamiyar kyautatawa. Mai madaukakin girma.
  43. Ar Raqib (الرقيب) The Watchful; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake kiyaye ayyukan bayinsa gaba ɗaya, me rubuta aikin da ɗan Adam yayi kafin ya mutu da bayan ya mutu. Mai tsinkayarwa.
  44. Al Mujib (المجيب) The Responsive, the Answerer; Allah Maɗaukaki shi ne me amsawa wanda ya roƙe shi. Mai amsawa.
  45. Al Wasi' (الواسع) The Vast, the All Encompassing; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ma'anoni da sunansa da siffofinsa suke ƙunshe basu da iyaka. Mai yalwatawa.
  46. Al Hakim (الحكيم) The Wise; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake da adalci wajen ƙaddara abu da kuma gwada shi. Mai hikima.
  47. Al Wadud (الودود) The Loving, the Kind One; Allah Maɗaukaki shi ne me tsananin ƙauna ga bayaninsa. Masoyi.
  48. Al Majid (المجيد) The All Glorious; Allah Maɗaukaki shi ne mai girma, wanda ya kaɗaita da maɗaukakiyar daraja, wadda take cikakkiya. Mai cikakkiyar siffa.
  49. Al Ba'ith (الباعث) The Raiser of the Dead; Allah Maɗaukaki shi ne me aiko Manzanni da hukunce-hukunce, shi ne me tashin tayuka bayan an yi bacci, shi ne mai tashin halitta bayan an mutu kuma ya yiwa kowa hisabi. Mai aiko Manzanni.
  50. Ash Shahid (الشهيد) The Witness; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake mahalicci wanda baya ɓuya ga barin wani abu, babu kuma wani abu da yake ɓoye masa a cikin mulkinsa. Mai shaida komai.
  51. Al Haqq (الحق) The Truth, the Real; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya cancanci a bauta masa, kuma tabbataccen da ba ya gushewa. Matabbacin gaskiya.
  52. Al Wakil (الوكيل) The Trustee, the Dependable; Allah Maɗaukaki shi ne me jiɓintar lamarin bayinsa gaba ɗaya. Shi ne wanda ake jiɓinta masa kowanne irin al'amari. Shi ya fi kowa ƙarfi, ya fi kowa sani, kuma ya fi kowa jin ƙai. Mai isarwa.
  53. Al Qawiyy (القوي) The Strong; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya ke da cikakkiyar ƙudura iko da kuma cikakkiyar daraja, shi ne mai rinjaye ba'a rinjayarsa, shi yake bada mafaka, shi kuma babu wanda ya isa ya ba Shi. Mai karfi.
  54. Al Matin (المتين) The Firm, the Steadfast; Allah Maɗaukakin Sarki shi ne wanda ba abinda ya gagare shi a cikin mulkinsa gaba ɗaya. Sannan halittu gabaki ɗaya ba wanda yake da tasiri akan su in ban da Shi. Matabbaci.
  55. Al Wali (الولي) The Protecting Friend, Patron, and Helper; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake jiɓintar lamarin bayinsa, ta hanyar kiyaye su da tattalinsu da kuma riritasu. Shi ne yake jiɓintar lamarin masoyansa ya dinga taimakonsu, kuma ya karya musu abokan gaba. Mai jibintarwa. See tdl/2021-06-12 for more.
  56. Al Hamid (الحميد) The All Praiseworthy; Allah maɗaukaki shi ne abin yabo a kowane irin hali mutum ya kasance. Sannan shi ne wanda ya ke abin yabo ga kowa da kansa. Macancancin yabo
  57. Al Muhsi (المحصي) The Accounter, the Numberer of All, Knower of each and every separate thing; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya kewaye da sanin dukkan abinda ya ke samamme ne. Mai iyakancewa.
  58. Al Mubdi (المبدئ) The Producer, Originator, and Initiator of all, The Beginner and Cause; Allah Maɗaukaki shi ne mai samar da kasantattu da kuma tabbatar da su bayan da ba su. Mai bayyanawa.
  59. Al Mu'id (المعيد) The Reinstater Who Brings Back All, The Restorer; Allah Maɗaukaki shi ne mai mayarwa, wato mai maida halitta bayan da ya rasar da ita. Mai komarwa.
  60. Al Muhyi (المحيي) The Giver of Life, Life Giver; Allah Maɗaukaki shi ne mai halittar rayuwa a cikin komai, Shi ne wanda ya halicci mutane bayan da babu su. Sannan Shi ne mai raya garurruka, Shi ne ya ke raya zuciyar masoyanSa da sani. Mai rayawa.
  61. Al Mumit (المميت) The Bringer of Death, the Destroyer, the Slayer; Allah Maɗaukaki shi ne mai kashewa, wato shi ne wanda ya ke kaddara mutuwa akan dukkan wanda ya mutu. Mai kashewa.
  62. Al Hayy (الحي) The Ever Living; Allah Maɗaukaki shi ne mai dauwamammiyar rayuwa, shi ne wanda yake da wanzuwa tabbatacciya wadda babu abinda zai mata iyaka. Rayayyen Sarki.
  63. Al Qayyum (القيوم) The Self Subsisting Sustainer of All, the Self-Existing; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya ke tsaye da zatinsa ya wadatu da shi, Shi ba ya danfare da komai, amma a damfare yake da Ubangiji. Madawwami.
  64. Al Waajid (الواجد) The Perceiver, the Finder, the Unfailing, the Resourceful; Allah shine madawaci me samun duk abinda yake so, me riskar duk abinda ya nema, wanda mulkinsa yake zartuwa kan komai. Mai bayarwa.
  65. Al Maajid (الماجد) The Illustrious, the Magnificent; Allah shine me wadatarwa, me arzurtawa. Mai daukakawa.
  66. Al Waahid (الواحد) The One, the All Inclusive, the Indivisible, the Unique One; Allah Madaukaki shi kaɗai ne wanda ba shi da abokin tarayya, Shine wanda yake da iko wajen zartar da nufinsa. Makadaici.
  67. Al Ahad (الاحد) The Unity, The indivisible
  68. As Samad (الصمد) The Long, the Impregnable, the Everlasting, the Eternal; Allah Maɗaukaki shine abin nufi da bukata. Duk wanda yake da bukata wajansa zai nufa da ita. Abin nafi da bukata.
  69. Al Qaadir (القادر) The All Able, The All-Powerful; Allah Maɗaukaki shine me iko cikakke akan dukkan komai ba tare da sanadi ba. Mai iko.
  70. Al Muqtadir (المقتدر) The All Determiner, the Dominant; Allah Maɗaukaki shine wanda yake da ragama gaba daya a hannunsa, babu wani wanda ya kuɓuce a cikin ikonsa. Mai iko da komai.
  71. Al Muqaddim (المقدم) The Expediter, He who brings forward, The Promoter, One Who Causes Advancement; Mai gabatarwa. Allah Maɗaukaki shine wanda yake gabatar da sashen wandansu abubuwa akan wadansu, kuma shine wanda yake gabatar da dalilai da sanadi akan abinda sanadin yake faruwa. Shine wanda yake gabatar da wanda yaso daga cikin bayinsa, ya fifita shi ya daukaka shi da bin Allah ko da tsoronsa da wata daukaka ta Duniya.
  72. Al Mu'akhkhir (المؤخر) The Delayer, He who puts far away, The Postponer; Mai jinkirtawa. Allah Maɗaukaki shine me jinkirtar da samar da wani abu akan wani abu da nufinsa.
  73. Al Awwal (الأول) The First; Na farko. Allah Maɗaukaki shine farko, amma ba tare da faruwa ba, kuma shine yake nan da zatinsa ba tare da wani daga cikin halittarsa ya samu ba.
  74. Al Aakhir (الآخر) The Last; Marashin karshe. Allah Maɗaukaki shine me wanzuwa, Shi kadai ba tare da karewa ba.
  75. Az Zaahir (الظاهر) The Manifest; the All Victorious; Mabayyani. Allah Maɗaukaki shine wanda yake a fili ga kowane irin abu ta hanyar dalili da hankali da talikai da ake iya gani.
  76. Al Baatin (الباطن) The Hidden; the All Encompassing; Boyayye. Allah Maɗaukaki shine wanda ba yanda za ayi hankali ko wata fahimta ta iya riskar zatinsa, don haka ya zama boyayye a gurin hankula da kuma fahimta, duk inda suka kai ba zasu iya fahimtar zatin Allah ba.
  77. Al Waali (الوالي) The Patron, The Ruler; Allah Maɗaukaki shine wanda yake jiɓintar lamarin bayinsa ta hanyar riritasu da kuma tattalinsu da kuma gwargwadasu da kuma yin aiki a kansu.
  78. Al Muta'al (المتعالي) The Self Exalted; Madaukaki. Allah Maɗaukaki shine wanda ya kai matuƙa a wajen ɗaukakar daraja da girma a wajen siffarsa da zatinsa da ayyujansa. [4]
  79. Al Barr (البر) The Most Loyal [5], The Most Kind and Righteous, The Doer of Good; Mai kyautatawa. Allah Maɗaukaki shine me yalwar kyautayi, kuma mai cika alƙawarinsa.
  80. At Tawwaab (التواب) The Ever Returning, Ever Relenting; Mai karbar tuba. Allah Maɗaukaki shine wanda yake samar da sababan tuba ga bayinsa. Mai in tausayi maimakon fushi.
  81. Al Muntaqim (المنتقم) The Avenger; Mai ukuba. Allah Maɗaukaki shine me karya ƙashin bayan azzalumi me kuma tsaurara ukuba ga masu sabonsa.
  82. Al 'Afuww (العفو) The Pardoner, the Effacer of Sins; Mai rangame. Allah Maɗaukaki shine me kankare zunubai da kura-kurai. In yaso yakan cike gurbinta da kyakyawan aiki.
  83. Ar Ra'uf (الرؤوف) The Compassionate, the All Pitying; Mai tausasawa. Allah Maɗaukaki shine yawan jinƙai me rangwame ga bayinsa. Me saurin fushi (high-tempered) a tsakaninsa da iyalinsa ko me saurin fushi a karkokin sana'o'insa ko me saurin fushi a kowane lokaci sai ya dinga karanta "YA ALLAHU YA RA'UFU" bayan sallar asuba kafin rana ta huɗo, Allah sai ya raba shi da saurin fushi.
  84. Malik al Mulk (مالك الملك) The Owner of All Sovereignty, The King of Absolute Sovereignty ; Mamallakin mulki. Allah Maɗaukaki shine wanda yake da tasarrufi Mudliki, cikin masarautarsa gaba daya a duniya da lahira. Shi ne yake naɗa wanda yaso kuma ya tuɓe wanda yaso daga mulki.
  85. Dhu al Jalal wa al Ikram (ذو الجلال و الإكرام) The Lord of Majesty and Generosity; Ma'abocin girma da girmame-girmame. Allah Maɗaukaki shine wanda ya kaɗaita da siffar girma da buwaya da kuma ɗaukaka.
  86. Al Muqsit (المقسط) The Equitable, the Requiter; Mai adalci. Allah Maɗaukaki shine wanda yake ɗ karwa wanda aka zalumta fansa, ya karɓar masa hakkinsa daga wajen azzalumi, sannan kuma yana taimakon wanda ake raunanawa akan wadanda suke raunana shi ɗin.
  87. Al Jaami' (الجامع) The Gatherer, the Unifier, the Uniter; Mai tara kowa. Allah Maɗaukaki shine wanda yake haɗa jiki da rai. Kuma shine wanda yake hada bayin Allah gabaki ɗaya a filin Alƙiyama. Shine wanda yake hada zukatan masoyansa guri daya a samesu da kaunar juna.
  88. Al Ghani (الغني) The All Rich, the Independent; Mawadaci. Allah Maɗaukaki shine wanda ya wadata ga barin duk abinda ba shi ba, amma shi komai yana da bukata a gurinsa.
  89. Al Mughni (المغني) The Enricher, the Emancipator; Mai wadatarwa. Allah Maɗaukaki shine wandayake wadata yake wadatarwa, ya wadata wanda ya so daga cikin bayinsa, kuma da abinda yaso na daga dangogin baiwa.
  90. Al Mani' (المانع) The Withholder, the Shielder, the Defender, the Protector; Mai hanawa. Allah Maɗaukaki shine wanda yake bawa komai abinda akwai masalaharsa a ciki, kuma yake hana abinda zai iya halaka shi, shine wanda yake hanawa domin hanawar ita tafi masalahar agare shi. Ana karanta YA MANI'U domin neman tsari.
  91. Ad Dharr (الضآر) The Distresser, the Punisher; Mai cutar da mai cutarwa. Allah Maɗaukaki shine wanda yake ƙaddara cuta da sharri ga wanda yaso, kuma ta duk inda ya so, Shine yake talautarwa, yake ɗora rashin lafiya, shi yake tsiyatarwa, shi yake hana abinci. Imma don ya kankare maka zunubi, imma don ya daukaka darajarka. Duk abinda Allah ya dorawa mutum domin yai masa wani alheri ne ba don ya cutar da shi ba.
  92. An Nafi' (النافع) The Propitious, the Benefactor, He Who Benefits; Mai amfanarwa. Allah Maɗaukaki shine wanda alheri da amfani na Lahira da Duniya daga gurinsa yake bubbugowa. Shine mai bada alfarma da kuma daukaka, mai bada shiriya, mai bada tsoron Allah.
  93. An Nur (النور) The Light; Mai haskakawa. Allah Maɗaukaki shine wanda haske yake mabayyani, wanda yake fitar da waninsa daga cikin duhu, babu izuwa hasken samuwa, ya fitar da wanda yaso daga cikin duhun jahilci izuwa hasken ilimi, ya fitar da wanda yaso daga cikin duhun jahilci izuwa hasken ilimi, ya fitar da wanda yaso daga cikin duhun kafirci zuwa hasken imani.
  94. Al Hadi (الهادي) The Guide, the One Who Gives Guidance; Mai shiryawa. Allah Maɗaukaki shine me shiryar da dukkanin halitta izuwa abinda yake shine mafi maslaha a gare su. Kuma mai shiryar da su ga barin abinda zai kauda su daga cutar rayuwa, shine mai shiryarwa izuwa tafarkin alheri baki ɗaya.
  95. Al Badi (البديع) Incomparable, the Originator, the Absolute Cause; Makagi. Allah Maɗaukaki shine me kayatar da halitta ya yita kyakkyawa, wanda duk ya ganta sai ya yaba.
  96. Al Baaqi (الباقي) The Ever Enduring and Immutable, the Everlasting; Wanzajje. Allah Maɗaukaki shine wanzajje bayan karewar halitta, wanda ba zai kar rasuwa ba har abada.
  97. Al Waarith (الوارث) The Heir, the Inheritor of All; Magaji. Allah Maɗaukaki shine zai gaje komai bayan karewar halitta.
  98. Ar Rashid (الرشيد) The Guide, Infallible Teacher, and Knower, the Right Guidance; Mai shiryawa. Allah Maɗaukaki shine wanda ya siffanta da cikar cika, duk abinda ake kira cika, to ta Allah ita ce cika ta haƙiƙa. Shine wanda yake shiryar da halittarsa izuwa abinda akwai masalaharsu a ciki, kuma shi yake fuskantar dasu izuwa abinda akwai alheri a cikinsa a Duniya da Lahira.
  99. As Sabur (الصبور) The Patient, the Timeless; Mai hakuri. Allah Maɗaukaki shine mai haƙuri akan abinda bai yarda da shi ba, kuma ya ƙyale shi ba zai fusata nan da nan ya halaka shi ba. Kuma shine wanda yake kimsa haƙuri a cikin zukatan bayinsa. Idan mutum yana wata harka yana neman ya sare, ya karaya a zuci ya bari, to sai ya yawaita ambaton YA SABURU domin Allah ya ba shi juriya akan wannan al'amari har ya cimma nasara.

Allah is the personal name of God and Muslims worship God mostly by this name. The names refer to "characteristics" and "attributes" of God (Allah).

The English translation of names may have a slightly different meaning than the original Arabic word due to the words available in each language.

Hadith (Hadisi) on memorizing the 99 names of Allah

Al-Bukhari (2736) and Muslim (2677) narrated from Abu Hurayrah (RA) that the Prophet Muhammad (S) said:

“Allah has ninety-nine names. Whoever memorizes them will enter Paradise.” [6] 
Allah Yana da sunaye guda 99. Duk wanda ya haddace su zai shiga Aljannah.

Saying that, you cannot simply memorize the names of Allah without understanding their meanings. The word translated as “memorized” in this hadith includes the following:

  1. Memorizing the 99 names.
    Haddace wadannan sunayen guda 99
  2. Understanding their meanings.
    Fahimtar ma'anoninsu
  3. Acting upon what they imply.
    Aikata rayuwa bisa ga su.

Duk wanda ya haddace wadannan sunayen guda 99, ya sansu, ya haddace su, ya fahimci ma'anoninsu, yai rayuwa bisa ga su, sannan yai amfani dasu wajen kira zuwa ga Allah, duk wanda yai haka, yace: dakalal jannah, zai shiga aljannah saboda ya gane waye Allah. [7]

99 Beautiful Names - Spoken Word by Boonaa Mohammed

File:99_Beautiful_Names_-_Spoken_Word_by_Boonaa_Mohammed.mp3


The Glorified Names (99 Names of Allah) - Benammi (Lyric Video)

File:The Glorified Names (99 Names of Allah) - Benammi (Lyric Video).mp3


References/Links

  1. https://en.wikipedia.org/wiki/Names_of_God_in_Islam
  2. https://simple.wikipedia.org/wiki/Names_of_God_in_Islam
  3. http://www.qul.org.au/the-holy-quran/asma-ul-husna
  4. 3:30 video of Asma ul Husna 99 Names of Allah recited nasheed-style: http://youtu.be/0UTXlpZlOEM?a
  5. His Majesty Live | Ammar AlShukry
  6. English_Explanation_to_the_Beautiful_and_Perfect_Names_of_Allah via https://www.clubhouse.com/room/xVlR2vBz
  7. 99 Names Of Allah ᴴᴰ ┇ #AsmaUlHusna ┇ by Sheikh Ibraheem Menk ┇ TDR Production https://www.youtube.com/watch?v=FJSuyz-vQVo
  8. 99 Beautiful Names - Spoken Word by Boonaa Mohammed https://youtu.be/r5fC9QlPCW8
  9. The Ninety Nine 99 Names of Allah - A Memorisation Tool w/Transliteration and Meanings by Sheikh Ibn Uthaymeen [8] (via Jamila)
  10. The Names and Attributes of Allah [9]
  11. The Ninety Nine Attributes of Allah [10]
  12. Names of Allah on http://islam.about.com/od/godallah/a/asma_husna.htm
  13. The 99 names of Allah; the ‘Most Beautiful Names’
  14. To Know Him is to Love Him Yaqeen Institute YouTube Playlist Last updated on Oct 3, 2019
    Who is God? Why does He do the things He does? Why are we who we are? The answers to so many contemporary questions about God lie within His Attributes. Discover the beautiful mysteries of Allah and the creation through His Names and Attributes.
  15. 99 gods vs 99 names of one God | Yaqeen Institute Daily Reminders
  16. Razia Hamidi's reflections on Al-Tawab and Al-Akram
  17. A dua list using the 99 names of Allah - May 14, 2020 Tweet (see also: [11] [12])
  18. With-Allah.com in both Hausa and English
    1. Know Allah through His Names and Attributes [13][14]
    2. Ka San Allah Da Sunayensa Da Siffofinsa [15]
  19. https://theazharis.com/products/names-of-allah-workbook - This has been made available as a physical workbook due to popular demand. Purchase your workbook now and follow along with the ‘Names of Allah’ series (YouTube playlist). Great resource for kids!
  20. Relation with Allah PDF compiled by Abu Sahl Al Ansari [16]
  21. Sunayen Allah (99) Tare Da Fa’idar Kowane Suna Da Kuma Yadda Za A Yi Amfani Da Shi [17]
  22. Beautiful Names of Allah - Encyclopedia of Translated Islamic Terms [18]
  23. 30 Heartfelt Conversations - Know Him to Invoke Him SWT 1441 2.pdf - Google Drive
  24. Reflections on the Names of Allah - Shaykh Mokhtar Maghraoui [19]

Subcategories

This category has only the following subcategory.

Media in category "99 names of Allah"

The following 10 files are in this category, out of 10 total.