Tarjamar Suratul Mulk da Hausa
- Albarkatun Allah da alheransa sun yawaita, mulki gabaɗaya a hannunSa yake, Shi mai iko ne a bisa dukkan komai. --Quran/67/1
- Shi ne wanda ya halicci mutuwa kuma ya halicci rayuwa, don ya gwada ku, wanene zai kyautata aiki a cikin ku. Shi Mabuwayi ne ƙaƙƙarfa, Mai gafara ga bayinSa waɗanda suka nemi tubanSa. --Quran/67/2
- Shi ne ya halicci sammai guda bakwai (7), wata kan wata, ba tare da wata ta taɓa jikin wata ba. Ba za ka gani ba a cikin halittun da Allah ya yi dangane da wani saɓani ko karkacewa ko illa. Ka mayar da ganin ka sama ka gani, ka duba ga gani, shin za ka samu wani huda ko wani tsaga a jikin sama? --Quran/67/3
- Sannan ka ƙara mayar da ganin ka sama a karo na biyu. Wallahi gani zai dawo gare ka a taɓe, kuma yana mai nadama (ma'ana duk yadda za ka kalli sama, ba za ka ga matsala a jikin ta ba. --Quran/67/4
- Haƙiƙa mun ƙawata saman duniya da fitilu na taurari. Kuma mun halicci taurari mun sanya su abin jifan sheɗanu masu hawa sama don sato zance. Haƙiƙa mun tanadawa shaiɗanu da kafirai azabar wata wuta mai tsananin ƙuna. --Quran/67/5
- Waɗanda suka kafirce wa Ubangijinsu, azabar wutar Jahannama ta tabbata akan su. Tir da makoma idan ta zama wutar jahannama ce. --Quran/67/6
- Idan an jefa wa'yannan kafirai da shaiɗanu cikin wutar jahannama, sai su ji wani sauti mai ƙarar gaske, mai tsoratarwa a cikin wannan wuta, tana zaɓalɓala, tana haɓaka. --Quran/67/7
- Wutar ta kusata ta fito daga inda take saboda tsananin fushin Allah da ya cika ta. Duk sanda aka zuba wani ayari na jama'a a cikin wannan wuta, masu gadin wannan wutar za su dinga tambayar wa'anda aka jefa a cikin ta... suna ce musu: Shin ko annabi mai gargaɗi bai zo muku bane? (4:53) --Quran/67/8