Daga Baƙonmu na mako: Hankalin matan Hausawa ya koma kan karatun 'labaran soyayya' ta intanet
Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙuwarmu ta wannan makon Safiyya Jibril, Marubuciyar littattafan Hausa kuma gwarzuwa Gasar Hikayata ta 2018. Dukkan abubuwan da ke cikin maƙalar ra'ayin Safiyya ne ba na BBC ba.
Yana daga cikin ɗabi'un mata son jin labari, hakan ya sanya su ɗabi'antuwa da karance-karancen littafai wanda zai haska musu duniyar da su ke gani a mafarkansu na ido biyu.
Matan aure da ƴan mata a arewacin Najeriya na matuƙar son karanta littattafan adabi da ake rubuta su da Hausa waɗanda aka fi sani da Littattafan Soyayya ko Hadisan Kano. Wanda ma fi akasarinsu aka gina su a kan jigon soyayya da zamantakewar gidan aure da mu'amala tsakanin kishiyoyi da sauran su.
Hakan ya sanya wasu matan suka zama masu bayar da hayar littafan, ga waɗanda ba za su iya saya ba. Sannan maza da dama sun mayar da siyar da wa'ɗannan littattafan a matsayin sana'ar da ke ciyar da su har ma da iyalansu.
Haka zalika a kan karanta littafan nan a Gidajen rediyo tun da daɗewa kamar shirin "Shafi Labari Shuni" na gidan rediyon tarraya Kaduna, "Rai Dangin Goro" da saura su.
Yalwatuwan yanar gizo a wannan ƙarni da muke ciki na 21 ya sanya mutane samun abubuwa cikin sauƙi kama da ga ilimi, labaran duniya, saƙonni har ma da littafan hikayoyi cikin sauƙi.
Daga baƙonmu na mako: Shin kwalliya na biyan kuɗin sabulu game da fina-finai masu dogon zango? Daga baƙonmu na mako: Dimokraɗiyya ta zubar da ƙimar masarutun gargajiya a Najeriya' Daga baƙonmu na mako: Shin aure nasara ce ga mutane? Wannan layi ne Buɗewar idon matan Hausawa da intanet
A shekarar 2012, matan Arewacin Najeriya da dama sun waye da manhajar Facebook, a lokacin ne aka samu wasu zauruka da suka fara kwafe littattafan Hausa da aka buga su suna wallafa su a shafukansu na Facebook mutane na tururuwar karantawa tare da yin sharhi akan labaran.
Hakan ya sanya wasu littattafan yaɗuwa ga waɗanda ke amfani da manhajar har ta kai wasu da ba su taɓa ɗaukar littafin Hausa sun karanta ba suka fara bin na shafukan Facebook suna karantawa domin a yi sharhin tare da su.
Shekarar 2013 ta haifar da sabbin marubuta waɗanda su littafan nasu a iya manhajojin sadarwa suke wallafawa kamar Facebook da WhatsApp da blogs.
Cikin su akwai irin su Rufaida Umar da Hauwa Jabo da Benazir Umar da wasu ƙalilan.
Wannan sabon salon ya sa mutane jinjinawa ƙoƙarinsu tare da bibiyar rubutunsu waɗanda su ke saki shafi-shafi, a hankali aka fara gane rubutu a mahajojin sadarwa, marubuta a wannan fannin suka ƙara yawa kowa na neman samun mabiya rubutunsa.
Rayuwa na tafiya ana ta samun ci gaba, hakan take a wajen narubuta yanar gizo (online writers) kamar yadda ake kiransu har ya kai ga duk wacce ko wanda ke ganin yana da abin rubutu zai samu wayarsa ya rubuta ya wallafa a kafar sadarwa.
Yawan marubuta da neman shahara a wajen marubuta ya cire tsaron da ke harkar rubutun Hausa, don wasu suna amfani da damar su saci rubutun wasu (plagiarism) wasu kuma na amfani da damar su yaɗa alfasha ta hanyar yin rubutun batsa, wasu na wanke fina-finai ne duk a son a kira su da marubuta.
Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce sosai tsakanin marubuta yanar gizo da marubuta littattafan kasuwar Kano, saboda suna zargin wasu marubuta yanar gizo da satar basirarsu ko amfani da littattafansu a matsayin su suka rubuta, sannan kuma suna ganin sun kashe musu kasuwarsu ta littattafai.
Ƙarin labaran da za ku so ku karanta 'Na cika burina na tallafa wa marayu dalilin gasar Hikayata' Hikayata: Ku saurari labarin 'Ya Mace Wannan layi ne
Sabuwar Wattpad [1] a duniyar rubutu
Samuwar Manhajar Wattpad ya sanya marubuta wallafa littattafan su a can saboda a can ba kasafai ake sace musu labarai ba. Da fari makaranta ba su waye da manhajar ba amma a zuwa yanzu mata da yawa har ma da maza sun fi gane wa karatu a manhajar saboda sauƙin karatu.
Kuma matuƙar mutum ya adana labari a library ɗinsa zai sami labarin a duk lokacin da ya shiga shafinsa a manhajar ko da bayan ya canza waya.
Karatu a manhajojin sadarwa ya ɗebe kewar mata da yawa, ya ilimantar da mata da dama akan sirrorin rayuwa da zamantakewa duk da cewa wasu ƙalilan daga ciki suna ƙunshe da alfasha da ɓata tarbiyya.
Sau da yawa shafuka a manhajar WhatsApp (groups) kan zama dandalin sharhi a kan littafan da aka karanta online, a dinga tafka muhawara a kan taurarin labarin kowa na ƙoƙarin bayyana raayinsa akai, wannan ma wani babban dalili ne da ya sanya mata ƙara shiga har kan karatun littattafin duk don kar babu su.
Rubutu a manhajar sadarwa ya zama wani takobi da ya sassari Adabin Hausa tun daga ƙa'idojin rubutun Hausa har zuwa ita kanta yaren.
Ba kamar Turanci da sai mutum ya goge a yaren zai iya tunanin fara rubuta littafi da harshen Turanci shi rubutun Hausa sai ya zama cewa duk wanda ya ji yaren zai yi rubutu har ma a karanta.
Hakan ya sanya mafi yawan littattafan suke kara zube, wasu cakuɗe da Turanci (ingausa), babu wani tsari.
Wasu kuma suka ɗauki rubutu a manhajar yanar gizo a matsayin wata hanyar yaɗa manufofinsu na sharri da ɓata tarbiyya wanda hakan na da matuƙar illa kasancewa littafi a yanar gizo yana nesa da mutum ne matukar baya tare da waya mai ɗauke da data.