Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/67/tarjama: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
No edit summary
Line 16: Line 16:
#Ku [[saurara]]! [[Shi]] [[ya]] [[san]] [[haƙiƙanin]] [[abinda]] [[ya]] [[halitta]], [[ya]] [[san]] [[halin]] [[su]] [[da]] [[ɗabi'ar]] [[su]]. [[Shi]] [[mai]] [[tausasawa]] [[bayinSa]] [[ne]] [[kuma]] [[mai]] [[basu]] [[labari]] [[dangane]] [[da]] [[abinda]] [[suke]] [[aikatawa]]. <small>--[[Quran/67/14]]</small>
#Ku [[saurara]]! [[Shi]] [[ya]] [[san]] [[haƙiƙanin]] [[abinda]] [[ya]] [[halitta]], [[ya]] [[san]] [[halin]] [[su]] [[da]] [[ɗabi'ar]] [[su]]. [[Shi]] [[mai]] [[tausasawa]] [[bayinSa]] [[ne]] [[kuma]] [[mai]] [[basu]] [[labari]] [[dangane]] [[da]] [[abinda]] [[suke]] [[aikatawa]]. <small>--[[Quran/67/14]]</small>
#Ubangiji Shi ne wanda ya halittar muku ƙasa mai sauƙi, don haka ku tafi a sasanninta da lungunanta da saqunanta. Ku ciyo daga arziƙinSa. Tattara bayi ya tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki. <small>--[[Quran/67/15]]</small>
#Ubangiji Shi ne wanda ya halittar muku ƙasa mai sauƙi, don haka ku tafi a sasanninta da lungunanta da saqunanta. Ku ciyo daga arziƙinSa. Tattara bayi ya tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki. <small>--[[Quran/67/15]]</small>
#Shin yanzu kun amince ga wanda yake sama shi ne Allah? Ya girgiza ƙasa a ƙarƙashin ƙafafuwan ku?  <small>--[[Quran/67/16]]</small>
#Shin yanzu kun amince ga wanda yake sama shi ne Allah? Ya girgiza ƙasa a ƙarƙashin ƙafafuwan ku, ta zo tana rorawa da ku?  <small>--[[Quran/67/16]]</small>
#   
#Shin yanzu kun amince ga wanda yake sama (Allah maɗaukakin sarki), Ya aiko muku da wata iska mai tsananin ƙarfi ta halakar da ku? Toh fa da sannu za ku sani yanda azabarSa take da uƙubarSa ga waɗanda suka saɓa masa.  <small>--[[Quran/67/16|Quran/67/17]]</small>  
[[Category:Quran/67]]
[[Category:Quran/67]]
[[Category:Quran]]
[[Category:Quran]]

Revision as of 12:51, 7 February 2022

Tarjamar Suratul Mulk da Hausa

  1. Albarkatun Allah da alheransa sun yawaita, mulki gabaɗaya a hannunSa yake, Shi mai iko ne a bisa dukkan komai. --Quran/67/1
  2. Shi ne wanda ya halicci mutuwa kuma ya halicci rayuwa, don ya gwada ku, wanene zai kyautata aiki a cikin ku. Shi Mabuwayi ne ƙaƙƙarfa, Mai gafara ga bayinSa waɗanda suka nemi tubanSa. --Quran/67/2
  3. Shi ne ya halicci sammai guda bakwai (7), wata kan wata, ba tare da wata ta taɓa jikin wata ba. Ba za ka gani ba a cikin halittun da Allah ya yi dangane da wani saɓani ko karkacewa ko illa. Ka mayar da ganin ka sama ka gani, ka duba ga gani, shin za ka samu wani huda ko wani tsaga a jikin sama? --Quran/67/3
  4. Sannan ka ƙara mayar da ganin ka sama a karo na biyu. Wallahi gani zai dawo gare ka a taɓe, kuma yana mai nadama (ma'ana duk yadda za ka kalli sama, ba za ka ga matsala a jikin ta ba. --Quran/67/4
  5. Haƙiƙa mun ƙawata saman duniya da fitilu na taurari. Kuma mun halicci taurari mun sanya su abin jifan sheɗanu masu hawa sama don sato zance. Haƙiƙa mun tanadawa shaiɗanu da kafirai azabar wata wuta mai tsananin ƙuna. --Quran/67/5
  6. Waɗanda suka kafirce wa Ubangijinsu, azabar wutar Jahannama ta tabbata akan su. Tir da makoma idan ta zama wutar jahannama ce. --Quran/67/6
  7. Idan an jefa wa'yannan kafirai da shaiɗanu cikin wutar jahannama, sai su ji wani sauti mai ƙarar gaske, mai tsoratarwa a cikin wannan wuta, tana zaɓalɓala, tana haɓaka. --Quran/67/7
  8. Wutar ta kusata ta fito daga inda take saboda tsananin fushin Allah da ya cika ta. Duk sanda aka zuba wani ayari na jama'a a cikin wannan wuta, masu gadin wannan wutar za su dinga tambayar wa'anda aka jefa a cikin ta... suna ce musu: Shin ko annabi mai gargaɗi bai zo muku bane? --Quran/67/8
  9. Sai su ce: Tabbas! Haƙiƙa mai gargaɗi a bi Allah ya zo mana. Muka ƙaryata shi, muka kuma ƙaryata dukkan wani manzo. Kuma ma muka ce musu "Ubangiji fa bai saukar da wani abu na littafi ba." Ku fa ba ku kasance a wani yanayi na gaskiya ba face sai a cikin ɓata mai girma. --Quran/67/9
  10. Kuma 'yan wuta za su ce: Ina ma a ce mun ji manzannin mu, mun ji abinda suke gaya mana. Ina ma mun hankalci abinda manzanni suke gaya mana. Da mun ji abinda suke gaya mana, wallahi da ba za mu zamo daga cikin 'yan wuta ba. --Quran/67/10
  11. Suma sai su amsa laifin su, su tabbatar da sun saɓi Allah a wannan lokaci. Tir da ma'abuta wuta, nesa-nesa da su. --Quran/67/11
  12. Lalle waɗanda suke jin tsoron Ubangijinsu a fake a duniya ba tare da sun gan Shi ba, gafara da yafiyar zunubi ta tabbata a gare su da kuma wani lada gwaggwaɓa mai girma - shi ne Aljanna. --Quran/67/12
  13. Ku ɓoye maganganun ku, ko ku bayyanar da su, lalle Ubangiji maɗaukakin sarki mai cikakken tsarki mai cikakken sani ne dangane da abinda ke cikin zuƙata.--Quran/67/13
  14. Ku saurara! Shi ya san haƙiƙanin abinda ya halitta, ya san halin su da ɗabi'ar su. Shi mai tausasawa bayinSa ne kuma mai basu labari dangane da abinda suke aikatawa. --Quran/67/14
  15. Ubangiji Shi ne wanda ya halittar muku ƙasa mai sauƙi, don haka ku tafi a sasanninta da lungunanta da saqunanta. Ku ciyo daga arziƙinSa. Tattara bayi ya tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki. --Quran/67/15
  16. Shin yanzu kun amince ga wanda yake sama shi ne Allah? Ya girgiza ƙasa a ƙarƙashin ƙafafuwan ku, ta zo tana rorawa da ku? --Quran/67/16
  17. Shin yanzu kun amince ga wanda yake sama (Allah maɗaukakin sarki), Ya aiko muku da wata iska mai tsananin ƙarfi ta halakar da ku? Toh fa da sannu za ku sani yanda azabarSa take da uƙubarSa ga waɗanda suka saɓa masa. --Quran/67/17