Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

parallel text/proz tm-town

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 16:29, 25 May 2022 by Admin (talk | contribs) (Created page with "via https://www.tm-town.com/translators/jemy09 {| class="wikitable" |- !source (english) !target (hausa) |- |the quiet game is a children...")
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

via https://www.tm-town.com/translators/jemy09

source (english) target (hausa)
the quiet game is a children's game where children must stay quiet. wasan shiru wani wasan yara ne da ake bukatar yara su yi shiru
stillness is sometimes a rule but in most cases not. wani lokacin nutsuwa kan kasance a cikin dokokin wasan, amma wasu lokuta, ba haka ba ne.
the last child or team to make noise wins the game. wanda ke nasara a wasan shi ne yaro ko tawagar karshe da ta yi kara ko magana.
it is usually acceptable for players to make sounds they cannot control, such as sneezing whereas talking would cause a player to get out. yawancin lokuta an yarda masu wasa su yi kararrakin da ba za su iya dakilewa ba, kamar su atishawa, amma idan dan wasa ya yi magana, ya fita kenan.
the game is often played indoors, typically in classrooms. yawanci ana wasan ne a cikin daki, musamman ma kamar ajujuwa.
it can also be played outdoors, for instance, at summer camps. amma ana iya yin wasan ma a waje, misali a sansanonin bazara.
one application of the game is for parents to keep their loud children quiet for a long journey. daya daga cikin muhimmancin wasan shi ne domin iyaye su iya sanya 'ya'yan su masu surutu su kasance sun yi shiru a yayin tafiya mai nisa.
it is often used as a social discipline. yawanci ana amfani da shi a matsayin hanyar horo a cikin jama'a.
there is no writing to others in the silent game because it would count as talking to others. ba a yi wa juna rubutu a wannan wasan shiru saboda ana daukan hakan a matsayin magana.
the objective of the game is to get opponents to giggle or talk by any means necessary. manufar wasan shine a sanya abokan hamayya su yi dariya ko magana ta kowacce hanya
this can include but is not limited to making funny faces and gentle tickling. wannan ya kunshi amma bai tsaya akan yin fuskokin abun dariya da cakulkuli.
a person cannot make another make noise by inflicting bodily harm. mutum ba zai iya sanya wani ya yi kara ko magana ba ta hanyar jikkata shi
there are many versions of this game, but nonetheless follow the same general rules: one who talks is immediately eliminated (laughing included), eventually isolating the winner at the end. akwai salo daban daban da ake yin wannan wasa, amma duk da haka dokar daya ce:duk wanda ya yi magana ya fita (har da dariya), ta haka za a fitar da wanda ya ci nasara a karshe.
sometimes it is played with the words in the dictionary instead of all sounds. wani lokacin ana amfani da kalmomin da ke cikin kamus a maimakon kowacce irin kara.