Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

misc/TikTok Most Downloaded

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 19:56, 10 August 2021 by Admin (talk | contribs)
  1. TikTok named as the most downloaded app of 2020 [1]
    An bayyana TikTok a matsayin manhajar da aka fi saukewa a 2020 [2]

    1. TikTok was the world's most downloaded app in 2020 as it took the top spot from Facebook Messenger, according to digital analytics company App Annie.
      TikTok ce manhajar da aka fi saukewa a 2020 a yayin da ta kwace kambun da Facebook Messenger yake rike da ita, a cewar kamfanin bin diddigin alkaluman shafukan intanet Annie.

    2. The Chinese video-sharing platform is the only app not owned by Facebook to make the global top five of downloads.
      Manhajar ta kasar China ita ce kadai manhaja da ba mallakin Facebook ba da ta kasance cikin manyan manhajoji biyar da aka fi saukewa a duniya.

    3. In its home country, TikTok's owner ByteDance also holds the top spot with the Chinese language video app Douyin.
      A kasar ta China, kamfanin ByteDance da ya mallaki TikTok shi aka fi amfani da shi tare da wata manhajar bidiyo da ke amfani da harshen China Douyin.

    4. TikTok's continued popularity emerged even after former US President Donald Trump tried to ban it in America.
      Manhajar ta TikTok ta samu karbuwa duk da yunkurin da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi haramta ta.

    5. Facebook-owned apps have held the top spot since the survey started in 2018 and the company still dominated the chart.
      Tun shekarar 2018 lokacin da aka soma bin diddigi kan shafukan intanet, manhajoji mallakin Facebook suke kan gaba a jerin wadanda aka fi saukewa kuma har yanzu su ne aka fi mu'amala da su.

    6. Mark Zuckerberg's social media giant accounted for the rest of the top five with Facebook's flagship app as well as WhatsApp, Instagram and Facebook Messenger all making an appearance.
      Manhajojin kamfanin sada zumunta na Mark Zuckerberg su ne suka kasance sauran manhajoji hudu da suke a jerin wadanda aka fi saukewa - wato Facebook, WhatsApp, Instagram da Facebook Messenger.

    7. Last year, then-President Donald Trump issued an executive order to ban new downloads of the TikTok app in the US.
      A shekarar da ta gabata, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan dokar haramta sauke manhajar TikTok a Amurka.

    8. The Trump administration claimed that TikTok posed a national security risk as the Chinese government had access to its user data. The company repeatedly denied the allegations.
      Gwamnatin Trump ta yi zargin cewa TikTok yana bazarana ga tsaron kasar saboda China tana karbar bayanai daga wurinsa. Sai dai kamfanin ya sha musanta zargin.

    9. Former President Donald Trump wanted to ban new downloads of TikTok in the US
      Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya so yana sauke manhajar TikTok a kasar

    10. Since becoming US President in January this year Joe Biden has withdrawn Mr Trump's executive order. As well as seeing off that challenge in the US the company has been exploring new ways to attract users. Last week, it emerged that TikTok is trialling a new vanishing clips feature similar to functions on Snapchat, Facebook and Instagram. TikTok Stories will allow users to see content posted by accounts they follow for 24 hours before they are deleted.
      Tun da ya zama shgaban kasa a watan Janairun wannan shekarar Joe Biden ya soke dokokin da Mr Trump ya kafa. A makon jiya, an bayyana cewa TikTok yana gwada wani tsari da zai sa bayanan da aka wallafa a cikinsa su rika bacewa kamar yadda yake faruwa a Snapchat, Facebook da Instagram. TikTok zai bar masu amfani da manhajar damar ganin abubuwan da mutanen da suke bi suka wallafa a shafukansu tsawon sa'a ashirin da hudu kafin su goge.