Chad: Rundunar sojin Cadi kuwa, ta ce ta kama 'yan tawaye da dama da suka tsallaka cikin ƙasar daga kudancin Libya bayan artabun da aka yi da su a arewacin ƙasar.
Ethiopia: Tsofaffin 'yan tawaye ne sama da dubu guda suka miƙa da makamansu bayan wata yarjejeniya da aka ƙulla da su da gwamnatin ƙasar.
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin
Nigeria Elections 2019 / Zaɓe 2019: APC! APC! Today I want to teach Atiku a lesson.--Uban jam'iyyar APC Bola Ahmed Tunibu a yayin yaƙin neman zaɓen jihar Lagos ya ke cewa yau zan koyawa Atiku darasi. Za mu ji me yayi zafi da kuma yadda yaƙin neman zaɓen ya kasance.
Sokoto Governor Debate: A yau BBC ke cika alƙawarinta na kawo muku mahawara tsakanin 'yan takaran gwamnan Sokoto.
Africa: Shugwabannin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afrika za su soma wani taro da zai mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi nahiyar su.
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin
Turkey, China: Turkiyya ta buƙaci ƙasar Sin da ta gaggauta ta rufe sansanonin da take tsare musulmi 'yan ƙabilar Uyghur.
UK: Yarima Philip na Birtaniya ya ajiye lasisinsa na tuƙi.
Nigeria's corn farmers: Manoma masara sun bayyana irin yabon da suka ce sun samu a noman bara.
Mun samu cigaba wajen bunƙasuwan masara daga shekara ta dubu biyar da sha biyar zuwa yanzu (2015-present). Da, masarar da ake nomawa a wannan lokaci ba ta wuce tonne miliyan sha biyar ba. Amma yanzu zuwa bana, noman da aka yi na bara shekara ta dubu biyu da sha takwas (2018), an noma ta miliyan ashirin.
Za ku ji cewar kasar Turkiya tayi Allah wadai da irin cin zarafin da kabilar Uighur ke fuskanta a kasar Chaina
Host: Zulaiha Abubakar Kibiya
African Union: Ƙungiyar tarayyar Afika ta AU, za ta gudanar da babban taron ta na kwanaki biyu a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha (Ethiopia) inda shugwabannin ƙasashen Afrika za su tattauna batun kwararar baƙin haure daga nahiyar zuwa ƙasashen turai.
Daidai lokacin da a cigaba da lalubo dabarun warware rikicin addini da ƙabilanci da ke barazana da rayuwar al'umar Filato.
Cibiyar sasanta tsakanin addinai mai ofishi a Kaduna, ya ƙaddamar da shirin yafewa juna tsakanin al'ummomin jihar bayan shafe sama da shekaru goma sha bakwai ana tashin hankali.
Shugaba Paul Kagame zai sauka daga muƙaminsa a ƙungiyar AU.
An shawarci sojojin ƙasar Venezuela a kan kayan agaji.
Turkiyya ta yi Allah-wadai da cin zarafin da ƙabilar Uighur ke fuskanta China.
11
VOA Hausa Shirin Rana 0500 UTC (30:00) na 2019-2-10 [18]
Hosts: Zahara Aminu Fagge da Baba Yakubu Maƙeri
Syria: Rundunar SDF ta k'asar Syria ta na samun goyon bayan Amurka, ta fatattaki 'yan k'ungiyar ISIS domin k'wace yankin k'arshe da ya rage a hannun k'ungiyar a gabashin Syria.
Turkey: K'asar Turkiyya ta kira ga Cadi ta rufe wasu sansanoni da gidajen yari, inda ta kama 'yan Turkawa 'yan k'abilar Ogo miliyan d'aya. Wacce ta ayyana su abin kunya ga bil Adama.
USA: Wakilan jam'iyyun demokurat da republican a Amurka suna ganawa a yau Litinin don ƙoƙarin cimma yarjejeniya a kan tsaron iyakar kasar don kauce ma a sake durk'usar ma ayyukan gwamnati.
Kenya: Ana ta k'ara nuna damuwa a Kenya game da inda wata mai kare hakkin bil Adama take tun bayan da ta b'ata a ranar Laraba.
Nigeria: Ana nuna fargaba gama da gobarar da tashi a ofisoshin hukumar zab'e na wasu k'ananan hukumomi.
Abinda gobarar ta shafa a ofisoshin guda biyu na k'ananan hukumomi ɗin, ba fa zai yi wani illa a zab'en da ke gaba ba. Domin a halin dai yanzun, ba a kai ma kayan zab'e ofisoshin k'ananan hukumomi da su ke wadannan wurare ba.--INEC
Nigeria: Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta bayyana damuwa ne a kan k'aruwar ayyukan galatsi da d'aukar doka a hannu da wasu 'yan k'asar ke yi.
Hosts: *Unintelligible - sounds like "Munshaba Adabu"
Labaran duniya da rahotanni daga Niger da Ghana.
China, Turkey: Za mu ji mahangar wasu ƙwararru akan abinda ke faruwa a ƙasar China na tsare da kuma killace musulmai kusan miliyan ɗaya da mahukuntan ƙasar suka yi tare kuma da kiran da ƙasar Turkiyya ta yi na ganin cewa an kawo ƙarshen wannan killacewar da aka yi musu.
Nigerian Newspaper Headlines: Muna ɗauke da wasu daga kanun jaridun Najeria.
Shirin Ko Kun San: Shirin kullun da ke bijiro da abubuwan da suka faru a tsawon tarihi.
Labaran da suka faru a jamhuriyar musulunci ta Iran da nahiyar Africa a cikin mako guda.
USA: 'Yan jam'iyyun Democrat da Republican, sun cimmawa matsayar kaucewa sake dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka.
Nigeria: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar PDP, ya ce rashin kayan aiki ne ke dawo da hannun agogo baya a yaƙi da ta'addanci a ƙasar.
"I beleive our military are not getting the best of equipment... <> Na yi imani sojojin mu basa samun ingantattun kayan yaƙi. Wasu lokuta ma, za ka ga makaman da 'yan ta'adda ke amfani da su, sun fi na sojoji inganci da zamunanci."
Election special: Sashen Hausa na BBC sun yi tanadi na musamman a lokacin zaɓen.
"Saboda idan ka fara shiri, ba za ka tsaya ba, tun ƙarfe shida na safe (6 AM), har zuwa ƙarfe goma sha ɗaya na dare. Ɗanɗanon shirin da sauran shirin zai sauya, kamar yadda muka sauya shi a lokacin da muka yi bakukuwan cika shekaru sittin da kafuwa.
BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG) [29]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
India: 'Yan sanda Indiya sun ce mutane sha bakwai ne suka mutu, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani otel da ke birnin Delhi.
Haiti: Masu zanga-zanga sun yi ta ƙona tayoyi a titunan ƙasar Haite tare da jefan jami'an tsaro da duwatsu.
Nigeria: Wasu 'yan Najeriya sun ce sun gaji da alƙawarin da gwamnati ke musu na bunƙasa harkar sufurin jirgin ƙasa a sassan ƙasar.
"Muna jin daɗin yanda aikin kasancewa. Amma kuma abinda muke gude shine, kada yazo ya kasance kamar aikin bayan ya fara kuma a tsaya. Sabida, sun san abu kamar za su yi, za su yaudari mutane. Can kuma, su yi amfani da kuɗin su yi wani abu."
Labarin wasanni <> sports.
Nigeria Elections 2019: Za ku ji zargin da jam'iyyar APC da PDP ke yi kan kawowa juna hare-hare gabannin zaɓen da ke tafe a Najeriya.
BBC Hausa Shirin Rana (Tue Feb 12th 2019 - 3pm NG) [31]
Hosts: Aminu Abdulkadir
Spain: An soma wata muhimmiyar shari'a ta wani fitaccen d'an awaren yankin Catalonia a Madrid, babban birnin Spain.
Nigeria: Wasu mata biyu 'yan yankin Ogoni a Najeriya, sun bayyana a wata kotu kan wata k'ara da aka shigar a k'asar Holland kan kamfanin mai na Shell.
Nigeria 2019 Elections: A Najeriyar, yayin da ake k'aratar zab'e a k'asar, ko matasa za su yi wannan zab'e kuwa.
"Zan yi zab'e inshaAllah. Kuma farkon lokaci na ne na yin zab'e a duniya. A zuciya na, ina tunanin zai yi amfani, inshaAllah."
"Ban sama kati na ba. Na je in anshi kati na sai suka ce mun wai ba su yi printing d'in shi ba. Saboda haka, ina tunanin wannan karo ba zan samu in yi zab'e ba."
BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT) [38]
Hosts: Aminu Abdulkadir
Sudan: Jami'an tsaron ƙasar Sudan sun tsare wani rukunnin shegunnan malamai na jami'o'i. Da suka yi zanga-zangar ƙin jinin shugaba Umar Al-Bashir a Khartoum - babban birnin ƙasar.
Nigeria: Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wasu mutane dangane da gobarar da tashi a wani ofishin hukumar zaɓe, yau a jihar Anambara. Gobarar ta haddasa ɓarna.
"Toh, har yanzu dai ba mu kai ga tantance yawan adadin wannan na'uran, ko guda nawa ne suka ƙone ba. Amma dai sun kashe tamanin da biyar cikin ɗari (85/100) sun ƙone.
DRC: 'Yan sanda sun tabbatar da kama mutane goma sha biyar dangane da rikicin ƙabilancin da ya haddasa mutuwar ɗarurwan mutane.
BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT) [42]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
Venezuela: Shugaban 'Yan adawa a Venezuela, ya sha alwashin shigar da kayan agaji. Duk kuwa da cewa shugaba Maduro ya ƙi amincewa da hakan.
Nigeria: Ana cigaba da cece-kuce kan shugaba Muhammadu Buhari a jihar Zamfara. Da ake cewa hakan zai iya haddasa fitina. Toh sai dai kuma magoya bayanshi sun ce an yi masa mummunar fahimta.
Shin kuma ko wace rawa ce rediyo ke takawa a rayuwar al'umma? Muna ɗauke da ƙarin bayani a cikin shirin.
South Korea: Hukumomin Koriya ta Kudu, sun musunta iƙirarin shugaba Trump kan ƙara yawan kuɗaɗen da take baiwa sojin Amurka a ƙasar ta.
Sudan: Jami'an tsaro sun cafke wasu daga cikin farfesoshin jami'o'i a birnin Khartoum.
Nigeria: Kwanaki uku kafin a yi zaɓen shugaban ƙasa, matasa da suka fito takaran muƙamai sun ce salon mulkin su zai banbanta da na 'yan baya.
"Almazaranci da kuɗin mutane, da rashin tsaro da ya addabi mutane, da yaudara, da sauransu... da aka saba ganin 'yan siyasa suna yi. Wanda mu ba mu fito ba da wannan..."
Cameroon: Za kuma ku ji kiraye-kirayen da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ke yi wa hukumomin Kamaru domin su sako wata ɗaliba da ake tsare ita.