Chad: Rundunar sojin Cadi kuwa, ta ce ta kama 'yan tawaye da dama da suka tsallaka cikin ƙasar daga kudancin Libya bayan artabun da aka yi da su a arewacin ƙasar.
Ethiopia: Tsofaffin 'yan tawaye ne sama da dubu guda suka miƙa da makamansu bayan wata yarjejeniya da aka ƙulla da su da gwamnatin ƙasar.
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin
Nigeria Elections 2019 / Zaɓe 2019: APC! APC! Today I want to teach Atiku a lesson.--Uban jam'iyyar APC Bola Ahmed Tunibu a yayin yaƙin neman zaɓen jihar Lagos ya ke cewa yau zan koyawa Atiku darasi. Za mu ji me yayi zafi da kuma yadda yaƙin neman zaɓen ya kasance.
Sokoto Governor Debate: A yau BBC ke cika alƙawarinta na kawo muku mahawara tsakanin 'yan takaran gwamnan Sokoto.
Africa: Shugwabannin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afrika za su soma wani taro da zai mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi nahiyar su.
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin
Turkey, China: Turkiyya ta buƙaci ƙasar Sin da ta gaggauta ta rufe sansanonin da take tsare musulmi 'yan ƙabilar Uyghur.
UK: Yarima Philip na Birtaniya ya ajiye lasisinsa na tuƙi.
Nigeria's corn farmers: Manoma masara sun bayyana irin yabon da suka ce sun samu a noman bara.
Mun samu cigaba wajen bunƙasuwan masara daga shekara ta dubu biyar da sha biyar zuwa yanzu (2015-present). Da, masarar da ake nomawa a wannan lokaci ba ta wuce tonne miliyan sha biyar ba. Amma yanzu zuwa bana, noman da aka yi na bara shekara ta dubu biyu da sha takwas (2018), an noma ta miliyan ashirin.
Za ku ji cewar kasar Turkiya tayi Allah wadai da irin cin zarafin da kabilar Uighur ke fuskanta a kasar Chaina
Host: Zulaiha Abubakar Kibiya
African Union: Ƙungiyar tarayyar Afika ta AU, za ta gudanar da babban taron ta na kwanaki biyu a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha (Ethiopia) inda shugwabannin ƙasashen Afrika za su tattauna batun kwararar baƙin haure daga nahiyar zuwa ƙasashen turai.
Daidai lokacin da a cigaba da lalubo dabarun warware rikicin addini da ƙabilanci da ke barazana da rayuwar al'umar Filato.
Cibiyar sasanta tsakanin addinai mai ofishi a Kaduna, ya ƙaddamar da shirin yafewa juna tsakanin al'ummomin jihar bayan shafe sama da shekaru goma sha bakwai ana tashin hankali.
Shugaba Paul Kagame zai sauka daga muƙaminsa a ƙungiyar AU.
An shawarci sojojin ƙasar Venezuela a kan kayan agaji.
Turkiyya ta yi Allah-wadai da cin zarafin da ƙabilar Uighur ke fuskanta China.
11
VOA Hausa Shirin Rana 0500 UTC (30:00) na 2019-2-10 [18]
Hosts: Zahara Aminu Fagge da Baba Yakubu Maƙeri
Syria: Rundunar SDF ta k'asar Syria ta na samun goyon bayan Amurka, ta fatattaki 'yan k'ungiyar ISIS domin k'wace yankin k'arshe da ya rage a hannun k'ungiyar a gabashin Syria.
Turkey: K'asar Turkiyya ta kira ga Cadi ta rufe wasu sansanoni da gidajen yari, inda ta kama 'yan Turkawa 'yan k'abilar Ogo miliyan d'aya. Wacce ta ayyana su abin kunya ga bil Adama.
USA: Wakilan jam'iyyun demokurat da republican a Amurka suna ganawa a yau Litinin don ƙoƙarin cimma yarjejeniya a kan tsaron iyakar kasar don kauce ma a sake durk'usar ma ayyukan gwamnati.
Kenya: Ana ta k'ara nuna damuwa a Kenya game da inda wata mai kare hakkin bil Adama take tun bayan da ta b'ata a ranar Laraba.
Nigeria: Ana nuna fargaba gama da gobarar da tashi a ofisoshin hukumar zab'e na wasu k'ananan hukumomi.
Abinda gobarar ta shafa a ofisoshin guda biyu na k'ananan hukumomi ɗin, ba fa zai yi wani illa a zab'en da ke gaba ba. Domin a halin dai yanzun, ba a kai ma kayan zab'e ofisoshin k'ananan hukumomi da su ke wadannan wurare ba.--INEC
Nigeria: Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta bayyana damuwa ne a kan k'aruwar ayyukan galatsi da d'aukar doka a hannu da wasu 'yan k'asar ke yi.
Hosts: *Unintelligible - sounds like "Munshaba Adabu"
Labaran duniya da rahotanni daga Niger da Ghana.
China, Turkey: Za mu ji mahangar wasu ƙwararru akan abinda ke faruwa a ƙasar China na tsare da kuma killace musulmai kusan miliyan ɗaya da mahukuntan ƙasar suka yi tare kuma da kiran da ƙasar Turkiyya ta yi na ganin cewa an kawo ƙarshen wannan killacewar da aka yi musu.
Nigerian Newspaper Headlines: Muna ɗauke da wasu daga kanun jaridun Najeria.
Shirin Ko Kun San: Shirin kullun da ke bijiro da abubuwan da suka faru a tsawon tarihi.
Labaran da suka faru a jamhuriyar musulunci ta Iran da nahiyar Africa a cikin mako guda.
USA: 'Yan jam'iyyun Democrat da Republican, sun cimmawa matsayar kaucewa sake dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka.
Nigeria: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar PDP, ya ce rashin kayan aiki ne ke dawo da hannun agogo baya a yaƙi da ta'addanci a ƙasar.
"I beleive our military are not getting the best of equipment... <> Na yi imani sojojin mu basa samun ingantattun kayan yaƙi. Wasu lokuta ma, za ka ga makaman da 'yan ta'adda ke amfani da su, sun fi na sojoji inganci da zamunanci."
Election special: Sashen Hausa na BBC sun yi tanadi na musamman a lokacin zaɓen.
"Saboda idan ka fara shiri, ba za ka tsaya ba, tun ƙarfe shida na safe (6 AM), har zuwa ƙarfe goma sha ɗaya na dare. Ɗanɗanon shirin da sauran shirin zai sauya, kamar yadda muka sauya shi a lokacin da muka yi bakukuwan cika shekaru sittin da kafuwa.
BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG) [29]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
India: 'Yan sanda Indiya sun ce mutane sha bakwai ne suka mutu, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani otel da ke birnin Delhi.
Haiti: Masu zanga-zanga sun yi ta ƙona tayoyi a titunan ƙasar Haite tare da jefan jami'an tsaro da duwatsu.
Nigeria: Wasu 'yan Najeriya sun ce sun gaji da alƙawarin da gwamnati ke musu na bunƙasa harkar sufurin jirgin ƙasa a sassan ƙasar.
"Muna jin daɗin yanda aikin kasancewa. Amma kuma abinda muke gude shine, kada yazo ya kasance kamar aikin bayan ya fara kuma a tsaya. Sabida, sun san abu kamar za su yi, za su yaudari mutane. Can kuma, su yi amfani da kuɗin su yi wani abu."
Labarin wasanni <> sports.
Nigeria Elections 2019: Za ku ji zargin da jam'iyyar APC da PDP ke yi kan kawowa juna hare-hare gabannin zaɓen da ke tafe a Najeriya.
BBC Hausa Shirin Rana (Tue Feb 12th 2019 - 3pm NG) [31]
Hosts: Aminu Abdulkadir
Spain: An soma wata muhimmiyar shari'a ta wani fitaccen d'an awaren yankin Catalonia a Madrid, babban birnin Spain.
Nigeria: Wasu mata biyu 'yan yankin Ogoni a Najeriya, sun bayyana a wata kotu kan wata k'ara da aka shigar a k'asar Holland kan kamfanin mai na Shell.
Nigeria 2019 Elections: A Najeriyar, yayin da ake k'aratar zab'e a k'asar, ko matasa za su yi wannan zab'e kuwa.
"Zan yi zab'e inshaAllah. Kuma farkon lokaci na ne na yin zab'e a duniya. A zuciya na, ina tunanin zai yi amfani, inshaAllah."
"Ban sama kati na ba. Na je in anshi kati na sai suka ce mun wai ba su yi printing d'in shi ba. Saboda haka, ina tunanin wannan karo ba zan samu in yi zab'e ba."
BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT) [38]
Hosts: Aminu Abdulkadir
Sudan: Jami'an tsaron ƙasar Sudan sun tsare wani rukunnin shegunnan malamai na jami'o'i. Da suka yi zanga-zangar ƙin jinin shugaba Umar Al-Bashir a Khartoum - babban birnin ƙasar.
Nigeria: Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wasu mutane dangane da gobarar da tashi a wani ofishin hukumar zaɓe, yau a jihar Anambara. Gobarar ta haddasa ɓarna.
"Toh, har yanzu dai ba mu kai ga tantance yawan adadin wannan na'uran, ko guda nawa ne suka ƙone ba. Amma dai sun kashe tamanin da biyar cikin ɗari (85/100) sun ƙone.
DRC: 'Yan sanda sun tabbatar da kama mutane goma sha biyar dangane da rikicin ƙabilancin da ya haddasa mutuwar ɗarurwan mutane.
BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT) [42]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
Venezuela: Shugaban 'Yan adawa a Venezuela, ya sha alwashin shigar da kayan agaji. Duk kuwa da cewa shugaba Maduro ya ƙi amincewa da hakan.
Nigeria: Ana cigaba da cece-kuce kan shugaba Muhammadu Buhari a jihar Zamfara. Da ake cewa hakan zai iya haddasa fitina. Toh sai dai kuma magoya bayanshi sun ce an yi masa mummunar fahimta.
World Radio Day 2019: Shin kuma ko wace rawa ce rediyo ke takawa a rayuwar al'umma? Muna ɗauke da ƙarin bayani a cikin shirin. (20:51-24:41)[43][44][45]
South Korea: Hukumomin Koriya ta Kudu, sun musunta iƙirarin shugaba Trump kan ƙara yawan kuɗaɗen da take baiwa sojin Amurka a ƙasar ta.
Sudan: Jami'an tsaro sun cafke wasu daga cikin farfesoshin jami'o'i a birnin Khartoum.
Nigeria: Kwanaki uku kafin a yi zaɓen shugaban ƙasa, matasa da suka fito takaran muƙamai sun ce salon mulkin su zai banbanta da na 'yan baya.
"Almazaranci da kuɗin mutane, da rashin tsaro da ya addabi mutane, da yaudara, da sauransu... da aka saba ganin 'yan siyasa suna yi. Wanda mu ba mu fito ba da wannan..."
Cameroon: Za kuma ku ji kiraye-kirayen da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ke yi wa hukumomin Kamaru domin su sako wata ɗaliba da ake tsare ita.
Cikin shirin za a ji yadda wasu al'umomi ke bayyana muhimmancin kafar sadarwar rediyo a rayuwarsu ta yau da kullum, dai lokacin da ake ranar rediyo ta duniya. A Najeriya kuwa mazauna yankunan karkara ne ke damuwa da yawan alkawura da 'yan siyasa ke dauka ba tare da cikawa ba.
Host: Munta Gayuwa*
Nigeria: Za mu ji yadda mazauna yankunan karkara a Najeria suke cewa suna cikin halin taƙaici na roman baka da 'yan siyasar ƙasar ke yi musu, tsawon shekaru da ƙasar ta kama mulki irin na demokraɗiya. Toh wane irin alƙauran ne wadannan 'yan siyasa ke yi wa wadannan mutane na karkara?
"In mun ci zaɓe, za mu yi muku hanya. In mun ci zaɓe, za mu kawo muku wuta, asibiti, da sauran abubuwa. Amma ko ɗaya, ba wanda ya taɓa cika mana. Wani pole-waya an kafa a nan ya kai har shekara goma sha biyu (12), amma wallahi ba a zo yin komai ba!"
Nigeria: Muna tafe da rahoto kan wannan matsala. Hakannan kuma za'a ji al'ummar Fulani da dokar hana kiwo ta shafa a jihar Benue da ke tsakiyar Najeriyar. Sun buƙaci kariya ne daga jami'an tsaro a duk inda suke don basu damar zaɓe kamar sauran 'yan ƙasar Najeriyar.
World Radio Day 2019: Yayin kuma da ake ranar rediyo ta duniya, za mu ji yadda wasu al'ummomi ke bayyana mahimmancin kafarta sadarwa a garesu. (14:44-18:15)[54][55][56]
Morocco: Hukumomi a ƙasar Morocco, sun kama wasu Faransawa da suka ce suna ɗaukar nauyin ƙungiyar nan ta IS.
Nigeria: Mutane da dama sun mutu lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe na shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya.
Thailand: Wasu fursunoni, wato 'yan ƙabilar Uyghir, sun tsere daga hannun jami'an tsaro a ƙasar Thailand.
A cikin shirin za a sha labaran duniya da kuma rahotanni kan zaben Najeriya da rikicin kasar Kamaru na 'yan aware da ke kara kamari. [5]
Hosts: Ramatu Garba Baba, Ahmed Salisu
Nigeria Elections 2019:
'Yan takara kusan saba'in (nearly 70) suka sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya, don tabbatar da zaman lafiya a yanzu da ma bayan zab'e.
Jam'iyya da ke mulki (the incumbent party APC) a Najeriyar ta APC kuwa, ta gudanar ko kammala yak'in neman zab'enta a Abuja.
Yayin da ita kuma jam'iyyar adawa ta PDP ta ce a karo na biyu, gwamnati ta hana ta gudanar da nata gangamin. Za mu ji mai hakan ke nufi da demokradiyyan Najeriya.
Mali: Za'a ji yanda k'ungiyoyi na addinin Islama suka k'addamar da gangami don nuna adawa ga halayyar 'yan siyasa.
Venezuela: Shugaba Maduro na Venezuela ya ce dole Juan Guaidó ya gurfana gaban kotu saboda k'eta dokokin k'asa.
Iran: Har kunar bak'in wake ya yi sanadiyyar rasuwar jami'an tsaron Iran ashirin (20).
Nigeria: 'Yan bindiga sun afkawa jerin gwanon motoci na gwamnan jihar Borno.
Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba.
USA, Iran: Amurka tana tuhumar wata tsohuwar jami'ar sojan samanta wadda ta canja sheƙa zuwa ɓangaren Iran da yin mata leƙan asiri.
USA: Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu bai tsaida shawarar rattaba hannu ko a'a kan ƙudurin bai ɗaya da jam'iyyu suka cimma ba wanda ya tanadi kuɗin gina katanga.
USA, Yemen: Majalisar wakilan Amurka mai rinjayin 'yan Democrats, ta kaɗa kuri'ar rage tallafin soji da Amurka ke baiwa gamayyar sojojin da Saudiya ke jagoranta a yaƙin Yemen.
Nigeria Elections 2019: Manyan 'yan takarar shugabancin Najeriya, sun sake jaddada yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla.
Nigeria: Gwamnar jihar Borno, Kashim Shettima, ya tsallake rijiya da baya a ƙauyen Lugumanu*.
"Mu mun ɗauka sojoji ne, ashe ba sojoji ba ne. Suna da kayan sarki kuma dukansu sun more..."
Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba.
Nigeria: Ministan tsaron Najeriya, Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya ƙaryata jita-jita da ake yi na cewa jami'an ƙasar basu da kayan aiki.
"Ko ƙasar America, ko ƙasar Ingila (England), ko ƙasar Russia, ba za su ce suna da isasshun kaya da suka ishe su ba.
Muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, wato EFCC, Ibrahim Mago, ya ce za su gurfanar da masu siyan da ƙuri'a da masu tada fitina lokacin zaɓr a gaban kotu.
Nigeria: A Najeriya, an kai wa waɗansu tagwayen hare-hare kan ayarin gwamnan jihar Borno a lokacin yaƙin neman zaɓe a garin Gamboru.
Nigeria Elections 2019: Jam'iyar PDP ta zargi gwamnatin APC da yi mata kwitingila na hana ta yin filin yin taro a Abuja: "Gashi bayan mun yi gangamin mutane, daga ko'ina sun taho, har da masu hawan jakuna da dawakai. Da muka je, muka tarar an sa kwaɗo, an hana." Sai dai kuma, ana ta ɓangaren, APC ta musanta wannan zargin: "Na farko dai, fili na gwamnati ne kuma na tabbata akwai ƙa'idoji wadda ake bi. Maganar cewa wai yau an hana su taro domin wani abu... tsoron faɗuwa ne, shi ya sa suke neman duk ta hanyar da za'a bi a tayar da hankali."
Sudan: BBC ta bankaɗo wani wuri da ake tsare masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati tare da azabtar da su a ƙasar Sudan.
Liberia: In gano gawar mutane biyar amma a mahaƙar ma'adinai ta gwal wadda ta rifta a arewacin Liberia a makon da ya wuce.
USA, Yemen: 'Yan majalisar Amurka sun gabatar da uzurin da zai janyowa dakarun ƙasar su janye daga Yemen.
Nigeria Elections 2019: Yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da zaɓe a Najeriya, masu larura ta musamman na ƙorafi kan jami'an tsaro a rumfunan zaɓe.
"Dubu biyu da sha biyar (2015), na je zan jefa ƙuri'a na, aka ce min ni in bi layi domin ban fi kowa ba. A bisa ga kundin tsarin dokoki na hukumar zaɓe. Mu akwai kulawa ta musamman. Idan muka zo, ba za mu bi layi ba.
Sports: Real Madrid ta doke Ajax (Ayax) da ci biyu da ɗaya (2-1). Wasan farko, zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarin Turai. Sai kuma ana fara yabawa mai horasda Madrid ɗin.
A yau ne a Najeriya aka shirya soma rarraba kayan aiki don zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe ranar Asabar.
Suma masu sa ido, sun buɗe sansaninsu a yau.
Wani kuma, wanda da alama ya fi kowa niyar zaɓen, tun jiya ya isa rumfar zaɓen. Inda yake shirin yin kwanaki uku yana jira kafin a soma kaɗa ƙuri'a.
"Tun jiya, ƙarfe goma sha ɗaya da rabi (10:30) na bar gida na. Na tattara kayana, na zo na zauna. Zan yi alƙawari kwana uku.
EU: Tarayar Turai ta kammala wani tsari na wata doka, wadda ta shafi haƙƙin mallaka a intanet. Sai dai, akwai masu ƙorafi akan haka. Za mu ji ko su wanene.
Nigeria Elections 2019: Wasu daga cikin jami'an gwamnatin APC a Najeriya sun nuna ɓacin ransu matuƙa dangane da yadda ƙungiyoyi na dattijan arewa da ma wasu daga ɓangaren kudancin ƙasar suka nuna goyan bayansu ga ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar adawa ta PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar.
Ethiopia: Za mu duba yadda masana suke kallon kawo ƙarshen taron shugabannin ƙasashen Afrika, wanda aka gudanar a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha, da kuma abubuwan da taron ya cimmawa game da yiyuwar aiwatar da su a aikace.
France: Za mu duba batun matakan da sojojin gwamnatin ƙasar France suka ɗauka na kare wanda ya juya mulki da suka ce an yi yunƙurin aiwatarwa a ƙasar Cadi.
Iran, Lebanon: Za a ji sharhin [ unintelligible: bayan labaran? ] wadanda suka yi magana akan ziyarar wadansu harkokin wajen Iran a ƙasar Lebanon.
Shirin Ko Kun San, Kaza a kan dame, shirin labaran wasannin mako.
Venezuela: Shugaban ƙasar Venezuela ya ce ƙasar za ta zamai wa Amurka Vietnam matuƙar ta kai mata hari.
Bahrain: An cika shekaru takwas da fara yunƙurin al'umma a ƙasar Bahrain.
China: ƙungiyar kare hakkin bil Adama (human rights) na ƙasashen duniya sun zargi ƙasar China da take hakkokin musulmi.