More actions
40 Hadiths in English <> Hadisai 40 da Hausa
- About Imam Nawawi's 40 Hadith and https://40hadithnawawi.com/posts/the-project/
- 40 Hadith class with Imam M.S Adly https://www.clubhouse.com/room/xXQvDdlg
- The concept of compiling "40 Hadiths" as told by Sh. Arsalan Haque [1]
- Arba'una Hadith Sheikh Ja'afar Mahmud Adam YouTube Playlist
Hadith 1 <> Hadisi na 1
# | Hadith 1 | Hadisi na ɗaya |
---|---|---|
1 | On the authority of Ameer ul-Mumineen (the Commander of the Faithful), Aboo Hafs `Umar ibn al-Khattaab radiAllaahu anhu, who said: I heard the Messenger of Allaah ﷺََ say: | An karɓo daga sarkin muminai, Baban Hafs, Umar ɗan Alkhaɗɗabi Allah ya yarda da shi yace: Na ji Manzon Allah ﷺََ yana cewa: |
2 | Actions are but by intentions and every man shall have only that which he intended. | “Dukkan aiyyuka suna tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya; |
3 | Thus he whose migration (Hijrah to Madeenah from Makkah) was for Allaah and His Messenger, his migration was for Allaah and His Messenger, | Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da Manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa. |
4 | and he whose migration was to achieve some worldly benefit or to take some woman in marriage, his migration was for that for which he migrated. | Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce dazai same ta ko kuma wata matar da zai aure ta to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa. |
5 | It is related by the two Imaams of the scholars of Hadeeth, Aboo `Abdillaah Muhammad ibn Ismaa`eel ibn Ibraheem ibn al-Mugheera ibn Bardizbah al-Bukhaaree | Shugabannin maluman da suka rubuta littatafan hadisai ne suka ruwaito shi; Wato: Baban Abdullahi Muhammadu ɗan Isma’ila ɗan Ibrahima ɗan Almugiyrah ɗan Bardizbah,(AlBukhariyy), A cikin ingantattun littatafansu [Sahihul Bukhariyy, [lamba: 1] |
6 | and Aboo-l-Husain Muslim ibn al-Hajjaaj ibn Muslim al-Qushairee an-Naisaabooree, in their two Saheehs, which are the soundest of compiled books [i.e. the most truthful books after the Book of Allaah, since the Qur’aan is not ‘compiled’]. | Da kuma Abul Husaini Muslimu ɗan Alhajjaju ɗan Muslimu, Alqushairiyyu Annaisaburiyyu. (acikin Sahihu Muslim), [lamba: 1907], waɗanda kuma sune mafi ingancin littatafan da aka rubuta. |
Hadith 2 <> Hadisi na 2
Hadith 3 <> Hadisi na 3
# | Hadith 3 | Hadisi na uku |
---|---|---|
1 | On the authority of Aboo `Abd ir-Rahmaan `Abdullaah, the son of `Umar ibn al-Khattab radiAllaahu ʻanhumaa, | An ruwaito daga Abu abdirrahman, Abdullahi ɗan Umar ɗan Alkhaɗɗabi Allah ya yarda da su |
2 | who said: I heard the Messenger of Allaah صلى الله عليه وسلم say: | ya ce: Naji Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yana cewa: |
3 | Islam has been built on five [pillars]: | “An gina musulunci akan abubuwa guda biyar; |
4 | testifying that there is no deity worthy of worship except Allaah and that Muhammad is the Messenger of Allah, | Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu manzon Allah ne, |
5 | establishing the salaah (prayer), | da tsayar da salla, |
6 | paying the zakah (obligatory charity), | bada zakka, |
7 | making the Hajj (pilgrimage) | yin hajji, |
8 | and fasting in Ramadan. | da azumin watan ramadana. |
Hadith 4 <> Hadisi na 4
# | Hadith 4 | Hadisi na huɗu |
---|---|---|
1 | On the authority of Aboo `Abd ir-Rahmaan `Abdullaah ibn Mas`ood (radiAllaahu anhu), who said: | An ruwaito daga Abiy-abdurrahman, Abdullahi dan Masʼud Allah ya yarda da shi |
2 | The Messenger of Allahصلى الله عليه وسلم and he is the Truthful, the Believed, narrated to us: | yace: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya bamu labari, kuma shi ne mai gaskiya abun gaskatawa: |
3 | Verily the creation of each one of you is brought together in his motherʼs womb for forty days in the form of a nutfah (a drop), | Lallai ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwanaki arbaʼin yana maniyyi, |
4 | then he becomes an ʻalaqah (clot of blood) for a like period, | Saʼannan sai ya kasance jini misalin haka, |
5 | then a mudghah (morsel of flesh) for a like period, | sannan sai ya kasance tsoka misalin haka, |
6 | then there is sent to him the angel who blows his soul into him | Sannan sai a turo Malaʼika zuwa gare shi sai ya busa masa rai, |
7 | who is commanded with four matters: | sai a umurce shi da kalmomi guda huɗu: |
8 | to write down his rizq (sustenance), | a rubuta arzikinsa |
9 | his lifespan, | da ajalinsa, |
10 | his actions, | da aikinsa, |
11 | and whether he will be happy or unhappy (i.e. whether or not he will enter Paradise). | da kuma shaƙiyyi ne ko mai rabo ne, |
12 | By the One, other than Whom there is no deity, | Na rantse da wanda babu wani abin bautawa idan ba shi ba, |
13 | verily one of you performs the actions of the people of Paradise | Lallai ayanku zai aikata aiki irin na ʻyan aljanna |
14 | until there is but an arms length between him and it, | har sai ya zama babu wani abu a tsakaninsa da tsakaninta sai ziraʼi, |
15 | and that which has been written overtakes him, | sai littafi ya rigaye shi |
16 | and so he acts with the actions of the people of the Hellfire and thus enters it; | sai yayi aiki irin na ʻyan wuta sai ya shige ta. |
Hadith 5 <> Hadisi na 5
<small> --[[40 Hadiths/5|Hadith 5]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_5_.3C.3E_Hadisi_na_5|40]]</small>
# | Hadith 5 | Hadisi na biyar |
---|---|---|
1 | On the authority of the Mother of the Faithful, Umm `Abdillaah `Aaishah (radi Allaahu ʻanhaa) , who said: The Messenger of Allaah :said صلى الله عليه وسلمََ | An ruwaito daga Ummul Muʼuminina Ummu Abdullahi Aishatu Allah ya yarda da ita tace... manzon Allah ya ce: |
2 | “He who innovates something in this matter of ours [i.e. Islaam] that is not of it will have it rejected [by Allaah]”. | Wanda ya ƙirƙiro wani abu daga cikin lamarinmu wanda abin da babu shi cikinsa to a mayar masa |
3 | Whoever performs a deed that is not in accordance with our matter will have it rejected. | A wata riwayar Muslim: “Wanda ya aikata wani aikin da babu umarninmu a kai to a mayar masa. |
Hadith 6 <> Hadisi na 6
<small> --[[40 Hadiths/6|Hadith 6]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_6_.3C.3E_Hadisi_na_6|40]]</small>
Hadith 7 <> Hadisi na 7
<small> --[[40 Hadiths/7|Hadith 7]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_7_.3C.3E_Hadisi_na_7|40]]</small>
# | Hadith 7 | Hadisi na bakwai |
---|---|---|
1 | On the authority of Abu Ruqayya Tameem ibn Aus ad-Daaree (radi Allaahu anhu) that the Prophet ﷺَََ said:
|
An ruwaito daga Abu Rukayya; Tamim ɗan Ausin Ad-dari Allah ya yarda da shi yace: Annabi ﷺَََ yace:
|
Hadith 8 <> Hadisi na 8
<small> --[[40 Hadiths/8|Hadith 8]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_8_.3C.3E_Hadisi_na_8|40]]</small>
# | Hadith 8 | Hadisi na takwas |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abdullah ibn Umar (ra): The Messenger of Allah (ﷺ) said, |
An ruwaito daga Abdullahi ɗan Umar (Allah Ya yarda da su): |
2 | "I have been ordered to fight against the people until they testify that there is none worthy of worship except Allah and that Muhammad is the Messenger of Allah, | An umarce ni da in yaƙi mutane har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, |
3 | and until they establish the salah and pay the zakat. | su tsayar da sallah, kuma su bayar da zakka; |
4 | And if they do that then they will have gained protection from me for their lives and property, unless [they commit acts that are punishable] in Islam, and their reckoning will be with Allah." [Bukhari & Muslim] [2] | idan sun aikata haka to sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai dai haƙƙin musulunci, hisabinsu yana wajen Allah maɗaukakin sarki. |
Hadith 9 <> Hadisi na 9
<small> --[[40 Hadiths/9|Hadith 9]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_9_.3C.3E_Hadisi_na_9|40]]</small>
# | Hadith 9 | Hadisi na tara |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (ra): I heard the Messenger of Allah (ﷺ) say, |
An ruwaito daga Abu Huraira: Na ji Manzon Allah SAW yana cewa: |
2 | “What I have forbidden for you, avoid. | "Duk abinda na hane ku, to ku nisance shi, |
3 | What I have ordered you [to do], do as much of it as you can. | abinda na umarce ku kuzo da shi gwargwadon iko, |
4 | For verily, it was only the excessive questioning and their disagreeing with their Prophets that destroyed [the nations] who were before you.” [Bukhari & Muslim] | Kuma lallai abinda ya halakar da wadanda suka zo kafin ku (shine) yawan tambayoyinsu da saɓawarsu ga Annabawansu |
Hadith 10 <> Hadisi na 10
<small> --[[40 Hadiths/10|Hadith 10]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_10_.3C.3E_Hadisi_na_10|40]]</small>
# | Hadith 10 | Hadisi na goma |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (ra): The Messenger of Allah (ﷺ) said,
|
An ruwaito daga Abu hurairata Allah ya yarda da shi yace: manzon Allah ﷺَََ yace:
|
Hadith 11 <> Hadisi na 11
<small> --[[40 Hadiths/11|Hadith 11]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_11_.3C.3E_Hadisi_na_11|40]]</small>
# | Hadith 11 | Hadisi na goma sha ɗaya |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Muhammad al-Hasan ibn Ali ibn Abee Talib (may Allah be pleased with him), the grandson of the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him), and the one much loved by him, who said: I memorised from the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him): “Leave that which makes you doubt for that which does not make you doubt.” [At-Tirmidhi] [An-Nasai] At-Tirmidhi said that it was a good and sound (hasan saheeh) hadeeth. [4] |
An ruwaito daga Abu Muhammadu; Hasanɗan Aliyu ɗan Abu ɗalib, Jikan Manzon Allah ﷺَ abin qaunarsa allah ya yarda dasu, yace: Na haddato daga Manzon Allah ﷺَ yace: Ka kyale duk abinda yake sanya ka kokwanto zuwa ga abinda ba ya maka kokwanto Tirmiziy yace: hadisi ne mai kyau ingantacce. |
Hadith 12 <> Hadisi na 12
<small> --[[40 Hadiths/12|Hadith 12]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_12_.3C.3E_Hadisi_na_12|40]]</small>
# | Hadith 12 | Hadisi na goma sha biyu |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said, “Part of the perfection of one’s Islam is his leaving that which does not concern him.” A hasan (good) hadeeth which was related by at-Tirmidhi and others in this fashion. [5] |
an ruwaito daga Abu Hurairata Allah ya yarda da shi yace: Manzon Allah ﷺَََ yace: Yana daga kyan musulunci mutum barin abinda bai shafe shi ba. Hadisi ne mai kyau, Tirmiziy [lamba:2318] da Ibnu-Majah [Lamba:3976] suka ruwaito shi. |
Hadith 13 <> Hadisi na 13
<small> --[[40 Hadiths/13|Hadith 13]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_13_.3C.3E_Hadisi_na_13|40]]</small>
# | Hadith 13 | Hadisi na goma sha uku |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hamzah Anas bin Malik (may Allah be pleased with him) — the servant of the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) — that the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said: None of you [truly] believes until he loves for his brother that which he loves for himself. [Al-Bukhari] [Muslim] [6] |
An ruwaito daga Abu Hamza, Anas ɗan Malik imanin ɗayanku ba zaya cika ba har sai yaso wa ɗan’uwansa irin abinda yake so wa kansa. Bukhariy [lamba:13] da Muslim [lamba:45] suka ruwaito shi. |
Hadith 14 <> Hadisi na 14
<small> --[[40 Hadiths/14|Hadith 14]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_14_.3C.3E_Hadisi_na_14|40]]</small>
# | Hadith 14 | Hadisi na goma sha huɗu |
---|---|---|
1 |
On the authority of Ibn Masood (may Allah be pleased with him) who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said, “It is not permissible to spill the blood of a Muslim except in three [instances]: the married person who commits adultery, a life for a life, and the one who forsakes his religion and separates from the community.” [Al-Bukhari] [Muslim] [7] |
An ruwaito daga Abdullahi ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi yace: Manzon Allah ﷺَََ yace: "Jinin mutum musulmi baya halatta sai da ɗaya daga cikin laifuka guda uku: magidancin da yayi zina, da rai wacce ta kashe rai, da wanda ya bar addininsa ya rabu da jama’a." Bukhariy [lamba:6878] da Muslim [lamba:1676]. |
Hadith 15 <> Hadisi na 15
<small> --[[40 Hadiths/15|Hadith 15]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_15_.3C.3E_Hadisi_na_15|40]]</small>
# | Hadith 15 | Hadisi na goma sha biyar |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said: Let him who believes in Allah and the Last Day speak good, or keep silent; and let him who believes in Allah and the Last Day be generous to his neighbour; and let him who believes in Allah and the Last Day be generous to his guest. [Al-Bukhari] [Muslim] [8] |
An ruwaito daga Abu Hurairata (R,A) yace: Lallai Annabi ﷺَََ yace: Wanda ya yi imani da Allah da ranar qarshe ya faɗi alheri ko yayi shiru, Wanda ya yi imani da Allah da ranar qarshe to ya girmama maqobcinsa, Wanda ya yi imani da Allah da ranar qarshe to ya girmama baqonsa. Bukhariy [Lamba:6018], da Muslim [lamba:48]suka ruwaito |
Hadith 16 <> Hadisi na 16
<small> --[[40 Hadiths/16|Hadith 16]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_16_.3C.3E_Hadisi_na_16|40]]</small>
# | Hadith 16 | Hadisi na goma sha shida |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him): A man said to the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), “Counsel me,” so he (peace and blessings of Allah be upon him) said, “Do not become angry.” The man repeated [his request for counsel] several times, and [each time] he (peace and blessings of Allah be upon him) said, “Do not become angry.” [Al-Bukhari] [9] |
An ruwaito daga Abu hurairata R.A (yace): Wani mutum yazo yace da Annabi ﷺَََ : Kayi min wasiyya sai yace: Kada ka yi fushi, sai yayi ta maimaita buqatarsa, sai (Annabi) yace, kada ka yi fushi. Bukhariy [lamba:6116] ya ruwaito shi. |
Hadith 17 <> Hadisi na 17
<small> --[[40 Hadiths/17|Hadith 17]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_17_.3C.3E_Hadisi_na_17|40]]</small>
# | Hadith 17 | Hadisi na goma sha bakwai |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Ya’la Shaddad bin Aws (may Allah be pleased with him), that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said: Verily Allah has prescribed ihsan (proficiency, perfection) in all things. So if you kill then kill well; and if you slaughter, then slaughter well. Let each one of you sharpen his blade and let him spare suffering to the animal he slaughters.” [Muslim] [10] |
An ruwaito daga Abu Ya’alah Shaddadu ɗan Ausi Allah ya yarda da shi daga Annabi ﷺَََ yace: Allah ta’alah ya rubuta kyautatawa ga kowanne irin abu; Idan za ku yi kisa ku kyautatawa kisan, Idan za ku yi yanka ku kyautata yankan, kowanne ɗayanku ya wasa wuqarsa, ya hutar da abin yankansa Muslim [lamba:1955] ya ruwaito shi. |
Hadith 18 <> Hadisi na 18
<small> --[[40 Hadiths/18|Hadith 18]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_18_.3C.3E_Hadisi_na_18|40]]</small>
# | Hadith 18 | Hadisi na goma sha takwas |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Dharr Jundub ibn Junadah, and Abu Abdur-Rahman Muadh bin Jabal (may Allah be pleased with him), that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:
|
An ruwaito daga Abu Zarri; wato Jundubu ɗan Junadata, da Abu Abdurrahman; wato Mu’azu ɗan Jabal Allah ya yarda da su, (yace): Manzon Allah ﷺَََ yace:
|
Hadith 19 <> Hadisi na 19
<small> --[[40 Hadiths/19|Hadith 19]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_19_.3C.3E_Hadisi_na_19|40]]</small>
# | Hadith 19 | Hadisi na goma sha tara |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Abbas Abdullah bin Abbas (may Allah be pleased with him) who said:[12] |
An ruwaito daga Abdullahi ɗan Abas Allah ya yarda da su yace: |
2 |
One day I was behind the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) [riding on the same mount] and he said, |
Na kasance a bayan Manzon allah ﷺَََ wata rana,sai yace da ni, |
3 | “O young man, I shall teach you some words [of advice]: |
"Ya kai yaro! Zan sanar da kai wasu kalmomi: |
4 | Be mindful of Allah and Allah will protect you. |
Ka kiyaye Allah sai ya kiyaye ka, |
5 | Be mindful of Allah and you will find Him in front of you. | ka kiyaye Allah za ka same shi a gaba gare ka, |
6 | If you ask, then ask Allah [alone]; and if you seek help, then seek help from Allah [alone]. | Idan zaka roqa to ka roqi Allah, idan zaka nemi taimako ka nemi taimakon Allah. |
7 | And know that if the nation were to gather together to benefit you with anything, they would not benefit you except with what Allah had already prescribed for you. | Ka sani daa al’umma za su taru don su amfane ka da wani abu, ba za su iya amfanar da kai komai ba , sai dai abinda Allah ya rubuta maka. |
8 | And if they were to gather together to harm you with anything, they would not harm you except with what Allah had already prescribed against you. | Idan kuma daa al’umma za su taru don su cuce ka da wani abu ba za su cuce ka da komai ba, sai da abinda Allah ya rubuta agareka. |
9 | The pens have been lifted and the pages have dried.” | An ɗauke alkaluma, takardun kuma sun bushe" |
10 | It was related by at-Tirmidhi, who said it was a good and sound hadeeth. | Tirmiziy [lamba:2516] ya ruwaito shi, yace hadisi ne mai kyau ingantacce. |
11 | Another narration, other than that of Tirmidhi, reads: | A wata riwayar kuma wacce ba ta (Imam) tirmiziy ba, |
12 | Be mindful of Allah, and you will find Him in front of you. | Ka kiyaye dokar Allah, zaka samu Ubangiji a gabanka, |
13 | Recognize and acknowledge Allah in times of ease and prosperity, and He will remember you in times of adversity. | ka nemi sanin Allah a lokacin da ka ke cikin yalwa zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani. |
14 | And know that what has passed you by [and you have failed to attain] was not going to befall you, and what has befallen you was not going to pass you by. | Ka sani duk abinda ya kuskure maka to bai kasance zai same ka ba, Duk kuma abinda ya same ka bai kasance zai kuskure maka ba. |
15 | And know that victory comes with patience, relief with affliction, and hardship with ease. | Ka sani lallai cin nasara yana tare da haquri, yayewar musiba kuma tana tare da baqin ciki, kuma lallai a tare da tsanani akwai sauki. |
Hadith 20 <> Hadisi na 20
<small> --[[40 Hadiths/20|Hadith 20]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_20_.3C.3E_Hadisi_na_20|40]]</small>
# | Hadith 20 | Hadisi na ashirin |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Masood Uqbah bin ’Amr al-Ansaree al-Badree (may Allah be pleased with him) who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said, “Verily, from what was learnt by the people from the speech of the earliest prophecy is: If you feel no shame, then do as you wish.” [Al-Bukhari] [13] |
An ruwaito daga Abu Mas’ud; Uqbatu ɗan Amru Al’ansariy Albadariy Allah ya yarda da shi yace: Manzon Allah ﷺَََ yace: Yana daga cikin abinda mutane suka riska daga zancen annabtar farko: idan har ka zamo ba ka jin kunya to ka aikata duk abinda kake so Bukhariy ya ruwaito shi [lamba:3483] |
Hadith 21 <> Hadisi na 21
<small> --[[40 Hadiths/21|Hadith 21]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_21_.3C.3E_Hadisi_na_21|40]]</small>
# | Hadith 21 | Hadisi na ashirin da ɗaya |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu `Amr — and he is also called Abu `Amrah — Sufyan bin Abdullah ath- Thaqafee (may Allah be pleased with him) who said: I said, "O Messenger of Allah, tell me something about al-Islam which I can ask of no one but you." He (peace and blessings of Allah be upon him) said, "Say I believe in Allah — and then be steadfast." [Muslim] [14] |
An ruwaito daga Abu amrin, ko abiy Amrata, sufyan ɗan Abdullahi Allah ya yarda da shi yace: Nace: Ya Manzon Allah ﷺَََ faɗa min wata Magana a cikin addinin musulunci wanda ba zan sake tambayar waninka ba game da ita? Sai yace: Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka daidaitu. Muslim ya ruwaito shi.[lamba 38] |
Hadith 22 <> Hadisi na 22
<small> --[[40 Hadiths/22|Hadith 22]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_22_.3C.3E_Hadisi_na_22|40]]</small>
# | Hadith 22 | Hadisi na ashirin da biyu |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Abdullah Jabir bin Abdullah al-Ansaree (may Allah be pleased with him) that: A man questioned the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) and said, |
An ruwaito daga abu Abdullahi Jabir ɗan Abdullahi Al’ansari Allah ya yarda da su yace wani mutum ya tambayi Annabi ﷺََ yace: |
2 | “Do you think that if I perform the obligatory prayers, fast in Ramadhan, treat as lawful that which is halal, and treat as forbidden that which is haram, and do not increase upon that [in voluntary good deeds], then I shall enter Paradise?” He (peace and blessings of Allah be upon him) replied, “Yes.” [Muslim] | Ba ni labari idanna sallaci salloli na wajibi, na’azumci watan Ramadan, na hahalatta halal, na haramta haram. Ban qara komai a kan haka ba, zan shiga Aljanna? sai Annabi ﷺََ yace: Eh! (Za ka shiga aljanna). Muslim ne yaruwaito shi [lamba:15]. |
3 | Ma’anan: (Na haramta haram shine: Na ni sance shi. Ma’anan: Na halatta halal shine: Na yi aiki da shi inaqudurta halaccinsa). | |
4 |
Hadith 23 <> Hadisi na 23
<small> --[[40 Hadiths/23|Hadith 23]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_23_.3C.3E_Hadisi_na_23|40]]</small>
# | Hadith 23 | Hadisi na ashirin da uku |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Malik al-Harith bin Asim al-Asharee (may Allah be pleased with him) who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said,
|
An ruwaito daga Abu Malik; Haris ɗan Asim Al-ash’ariy yace: Manzon Allah ﷺََ yace:
|
Hadith 24 <> Hadisi na 24
<small> --[[40 Hadiths/24|Hadith 24]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_24_.3C.3E_Hadisi_na_24|40]]</small>
# | Hadith 24 | Hadisi na ashirin da hudu |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Dharr al-Ghifaree (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) from his Lord, that He said:
|
An ruwaito daga Abu zarrin Al’gifariy Allah ya yarda da shi daga Annabi ﷺََ cikin abinda Annabi yake ruwaitowa daga Ubangijinsa; lallai Allah mabuwayi da ɗaukaka yace:
|
Hadith 25 <> Hadisi na 25
<small> --[[40 Hadiths/25|Hadith 25]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_25_.3C.3E_Hadisi_na_25|40]]</small>
# | Hadith 25 | Hadisi na ashirin da biyar |
---|---|---|
1 |
Also on the authority of Abu Dharr (may Allah be pleased with him): Some people from amongst the Companions of the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said to the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him),
|
An ruwaito daga Abu zarrin Al’gifariy Allah ya yarda da shi kuma yace: Lallai wasu mutane daga cikin sahabban Manzon Allah ﷺََ sun ce da Annabi ﷺََ
|
Hadith 26 <> Hadisi na 26
<small> --[[40 Hadiths/26|Hadith 26]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_26_.3C.3E_Hadisi_na_26|40]]</small>
# | Hadith 26 | Hadisi na ashirin da shida |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said,
|
An ruwaito daga Abu hurairata Allah ya yarda da shi ya ce:“ Manzon Allah ﷺََ yace:
|
Hadith 27 <> Hadisi na 27
<small> --[[40 Hadiths/27|Hadith 27]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_27_.3C.3E_Hadisi_na_27|40]]</small>
# | Hadith 27 | Hadisi na ashirin da bakwai |
---|---|---|
1 |
On the authority of an-Nawas bin Sam’an (may Allah be pleased with him), that the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said: Righteousness is in good character, and wrongdoing is that which wavers in your soul, and which you dislike people finding out about. [Muslim] And on the authority of Wabisah bin Ma’bad (may Allah be pleased with him) who said: I came to the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) and he (peace and blessings of Allah be upon him) said, “You have come to ask about righteousness.” I said, “Yes.” He (peace and blessings of Allah be upon him) said, “Consult your heart. Righteousness is that about which the soul feels at ease and the heart feels tranquil. And wrongdoing is that which wavers in the soul and causes uneasiness in the breast, even though people have repeatedly given their legal opinion [in its favour].” A good hadeeth transmitted from the musnads of the two imams, Ahmed bin Hambal and Al- Darimi, with a good chain of authorities. [20] |
An ruwaito daga Annawas ɗan Sam’an Allah ya yarda da shi, daga Annabi ﷺََ yace: Albirru shine: kyakkyawan halayya, Shi kuma laifi shine Abinda yayi maka susa a cikin ranka, kuma kake qin mutane suganshi. Muslim [lamba:2553] ya ruwaitoshi. An ruwaito daga Wabisa ɗan Ma’abad, yace: Na zo wajen Manzon Allah ﷺ sai yace: Ka zo ka tambayi ma’anan albirru? Sai nace: E (na’am), Sai yace: Ka yi fatawa wa zuciyarka, Albirru: shine abinda rai ya nitsu zuwa gareshi, zuciya itama ta samu nitsuwa da shi. Shi kuma ismu: Duk abinda ya yi susa acikin rai, kuma ya yi ta kai-komo a cikin qirji, koda mutane sun baka fatawa, sun kuma yi ta baka fatawa. Hadisi ne mai kyau (hasan), Mun ruwaitoshi a cikin littatafan Musnad guda biyu; Ahmad ɗan Hanbal [lamba:4/227], da Addarimiy, [2/246] da isnadi mai kyau (hasan). |
Hadith 28 <> Hadisi na 28
<small> --[[40 Hadiths/28|Hadith 28]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_28_.3C.3E_Hadisi_na_28|40]]</small>
# | Hadith 28 | Hadisi na ashirin da takwas |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Najeeh al-’Irbaad ibn Saariyah (may Allah be pleased with him) who said:
[Abu Dawud] It was related by at-Tirmidhi, who said that it was a good and sound hadeeth. [21] |
An ruwaito daga Abu Nujaih, wato: Irbadu ɗan Sariya Allah ya yarda da shi yace:
Abu dawud [lamba:4607] da Timiziyy [lamba:266] yace: hadisi ne mai kyau ingantacce. |
Hadith 29 <> Hadisi na 29
<small> --[[40 Hadiths/29|Hadith 29]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_29_.3C.3E_Hadisi_na_29|40]]</small>
# | Hadith 29 | Hadisi na ashirin da tara |
---|---|---|
1 |
On the authority of Muadh bin Jabal (may Allah be pleased with him) who said:
It was related by at-Tirmidhi, who said it was a good and sound hadeeth. [22] |
An ruwaito daga Mu’azu ɗanJabal Allah ya yarda da shi yace:
Tirmiziy [lamba:2616] ya ce hadisi ne mai kyau ingantacce |
Hadith 30 <> Hadisi na 30
<small> --[[40 Hadiths/30|Hadith 30]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_30_.3C.3E_Hadisi_na_30|40]]</small>
# | Hadith 30 | Hadisin talatin |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Tha’labah al-Kushanee — Jurthoom bin Nashir (may Allah be pleased with him) — that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:
A hasan hadeeth narrated by ad-Daraqutnee and others. [23] |
An ruwaito daga Abu Sa’alabata; wato: Jursumu ɗan Nashir Allah ya yarda da shi. ya karɓo daga manzon Allah ﷺََ yace:
Hadisi ne hasan, Daraquɗuniy [4/184]، da waninsa suka ruwaito shi. |
Hadith 31 <> Hadisi na 31
<small> --[[40 Hadiths/31|Hadith 31]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_31_.3C.3E_Hadisi_na_31|40]]</small>
# | Hadith 31 | Hadisin talatin da daya |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu al-’Abbas Sahl bin Sa’ad as-Sa’idee (may Allah be pleased with him) who said: A man came to the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) and said, “O Messenger of Allah, direct me to an act which, if I do it, [will cause] Allah to love me and the people to love me.” So he (peace and blessings of Allah be upon him) said, “Renounce the world and Allah will love you, and renounce what the people possess and the people will love you.” A hasan hadeeth related by Ibn Majah and others with good chains of authorities. [24] |
An ruwaito daga Abu Abbas; Sahlu ɗan Sa’ad Assa’idiy Allah ya yarda da shi yace: Wani mutum yazo wajen Annabi ﷺََ yace: Ya Manzon Allah! Nunamin aikin da idan na aikatashi, Allah zai qaunace ni, mutane suma za su qaunaceni; Sai ya ce: Ka yi zuhudu cikin lamarin duniya, sai Allah ya qaunace ka, kuma kanisanci abin hunnun mutane, sai mutane su qaunace ka. Hadisi ne hasan, Ibnu-Majahne ya ruwaito shi [lamba:4102] dawaninsa ta hanyoyi masukyau. |
Hadith 32 <> Hadisi na 32
<small> --[[40 Hadiths/32|Hadith 32]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_32_.3C.3E_Hadisi_na_32|40]]</small>
# | Hadith 32 | Hadisin talatin da biyu |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Sa’eed al-Khudree (may Allah be pleased with him), thatthe Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said: There should be neither harming (darar) nor reciprocating harm (dirar). A hasan hadeeth related by Ibn Majah, ad-Daraqutnee and others as a musnad hadeeth. It was also related by Malik in al-Muwatta in mursal form from Amr bin Yahya, from his father from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), but leaving Abu Sa’eed from the chain. And it has other chains of narrations that strengthen one another. [25] |
An ruwaito daga Abu Sa’idu, wato Sa’ad ɗan Malik ɗan sinan Al-Khudiry Allah ya yarda da shi yace: Manzon Allah ﷺََ yace: Babu cuta babu cutarwa Hadisine hasan, Ibnu Majahya ruwaito shi, [lamba:2341] da Daraquɗuniy [lamba:228] dawaninsu Musnadan. Haka Imamu Malik [2/746] ya ruwaito shi acikin Muwaɗɗa Mursalan daga Amru ɗan Yahya, daga babansa, daga Annabi ﷺََ, bai ambaci Abu sa’idb, Amma hadisin yana dahanyoyin da sashinsu ya ke qarfafa sashi. |
Hadith 33 <> Hadisi na 33
<small> --[[40 Hadiths/33|Hadith 33]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_33_.3C.3E_Hadisi_na_33|40]]</small>
# | Hadith 33 | Hadisin talatin da uku |
---|---|---|
1 |
On the authority of Ibn Abbas (may Allah be pleased with him), that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said: Were people to be given everything that they claimed, men would [unjustly] claim the wealth and lives of [other] people. But, the onus of proof is upon the claimant, and the taking of an oath is upon him who denies. A hasan hadeeth narrated by al-Baihaqee and others in this form, and part of it is in the two Saheehs. [26] |
An ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da su ya ce: Manzon Allah ﷺََ. ya ce: Da za a bai wa mutune (abinda suka faɗa) daga da'awarsu, to da waɗansu sun yi da’awar dukiyar waɗansu da jininsu sai dai hujja tana kan mai da’awa, rantsuwa kuma tana kanwanda ya yi musu. Hadisi ne mai kyau (hasan), Baihaqiy ya ruwaitosh [10/252], da waninsa. Wani sashina hadisin yana cikin Bukhariy da Muslim. |
Hadith 34 <> Hadisi na 34
<small> --[[40 Hadiths/34|Hadith 34]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_34_.3C.3E_Hadisi_na_34|40]]</small>
# | Hadith 34 | Hadisin talatin da huɗu |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Sa`eed al-Khudree (may Allah be pleased with him) who said: I heard the Messenger of Allah (ﷺ) say, “Whosoever of you sees an evil, let him change it with his hand; and if he is not able to do so, then [let him change it] with his tongue; and if he is not able to do so, then with his heart — and that is the weakest of faith.” [Muslim] [27] |
An ruwaito daga Abu Sa’id Al-Khuduriy Allah ya yarda da shi yace: Na ji Manzon Allah ﷺََ yana cewa: Duk wanda ya ga abin qi to ya gusar da shi dahannunsa, idan kuma ba shida iko to ya gusar da shi daharshensa, idan bai samu ikoba, to sai ya qi abin azuciyarsa, wannan kuma shine mafi raunin imani. Muslim ne ya ruwaito shi [lamba:49]. |
Hadith 35 <> Hadisi na 35
<small> --[[40 Hadiths/35|Hadith 35]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_35_.3C.3E_Hadisi_na_35|40]]</small>
# | Hadith 35 | Hadisin talatin da biyar |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said, “Do not envy one another, and do not inflate prices for one another, and do not hate one another, and do not turn away from one another, and do not undercut one another in trade, but [rather] be slaves of Allah and brothers [amongst yourselves]. A Muslim is the brother of a Muslim: he does not oppress him, nor does he fail him, nor does he lie to him, nor does he hold him in contempt. Taqwa (piety) is right here [and he pointed to his chest three times]. It is evil enough for a man to hold his brother Muslim in contempt. The whole of a Muslim is inviolable for another Muslim: his blood, his property, and his honour.” [Muslim] [28] |
An ruwaito daga Abu Hurairata Allah ya yarda da shi yace: Manzon Allah ﷺََ yace: Kada kuriqa yi wa juna hassada, kuma kada ku yi kore (cikin kasuwanci), kada kuyi qiyayya da juna, kada ku juyawa juna bayanku, kuma kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin ɗan’uwansa, Kukasance bayin Allah ‘yan’uwan juna. Musulmi ɗan’uwan musulmi ne, baya zaluntar sa, kuma baya qin taimakonsa, kuma baya yimasa qarya, kuma baya wulaqantar da shi, Taqawar Allah da bin dokokinsa yananan, sannan yayi nuni aqirjinsa (har) sau uku Ya ishi mutum sharri, ya riqa raina ɗan’uwansa musulmi, Jinin kowanne musulmi dadukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi. Muslim ne ya ruwaito shi [Lamba:2564]. |
Hadith 36 <> Hadisi na 36
<small> --[[40 Hadiths/36|Hadith 36]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_36_.3C.3E_Hadisi_na_36|40]]</small>
# | Hadith 36 | Hadisin talatin da shida |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), that the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said: Whoever removes a worldly grief from a believer, Allah will remove from him one of the griefs of the Day of Resurrection. And whoever alleviates the need of a needy person, Allah will alleviate his needs in this world and the Hereafter. Whoever shields [or hides the misdeeds of] a Muslim, Allah will shield him in this world and the Hereafter. And Allah will aid His slave so long as he aids his brother. And whoever follows a path to seek knowledge therein, Allah will make easy for him a path to Paradise. No people gather together in one of the Houses of Allah, reciting the Book of Allah and studying it among themselves, except that sakeenah (tranquility) descends upon them, and mercy envelops them, and the angels surround them, and Allah mentions them amongst those who are with Him. And whoever is slowed down by his actions, will not be hastened forward by his lineage. Related by [Muslim] in these words. [29] |
An ruwaito daga Abu hurairata Allah ya yarda da shi daga Annabi ﷺََ yace: Wanda duk ya kautarwa mumini wani baqin ciki daga cikin baqin cikin duniya Allah zai kautar masa dawani baqin ciki daga baqin cikin qiyama, Duk wanda yakawo sauqi ga wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauqi a duniya da lahira. Wanda ya suturce musulmi Allah zai yi masa sutura a duniya da lahira, Allah yana cikin taimakon bawa matuqar bawan yana taimakon ɗan’uwansa. Wanda ya kama wani tafarki yana neman ilmi acikinsa Allah zai sauƙakemasa hanyar shiga aljanna. Babu wasu mutane da za sutaru a cikin wani ɗaki daga ɗakunan Allah, suna karanta littafin Allah, suna yin darasinsa a tsakaninsu dajuna; face (sai) nutsuwa ta sauka a kansu, rahama talulluɓe su, Mala’iku kuma sukewaye su, Sai kuma Allah ya ambace su ga waɗanda suke wajensa. Wanda duk aikinsa ya yi sanɗa da shi to dangatakarsa ba za ta yigaggawa da shi ba. Muslimne ruwaito shi [Lamba:2699]. da wannan lafazin. |
Hadith 37 <> Hadisi na 37
<small> --[[40 Hadiths/37|Hadith 37]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_37_.3C.3E_Hadisi_na_37|40]]</small>
# | Hadith 37 | Hadisin talatin da bakwai |
---|---|---|
1 |
On the authority of Ibn Abbas (may Allah be pleased with him), from the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him), from what he has related from his Lord: Verily Allah ta’ala has written down the good deeds and the evil deeds, and then explained it [by saying]: “Whosoever intended to perform a good deed, but did not do it, then Allah writes it down with Himself as a complete good deed. And if he intended to perform it and then did perform it, then Allah writes it down with Himself as from ten good deeds up to seven hundred times, up to many times multiplied. And if he intended to perform an evil deed, but did not do it, then Allah writes it down with Himself as a complete good deed. And if he intended it [i.e., the evil deed] and then performed it, then Allah writes it down as one evil deed.” [Al-Bukhari] [Muslim]. [30] |
An ruwaito daga Dan Abbas Allah ya yarda da su, daga Manzon Allah ﷺََ, cikin irin abinda yaruwaito daga Ubangijisa mai girma da ɗauka yace: Allah ya rubuta ayyukan alheri da munana, sannan yabayyana hakan, Wanda duk ya himmatu zai aikata wani kyakkywan aiki sai bai samu aikatawa ba, Allah zai rubutamasa kyakkyawan aiki guda ɗaya cikakke a wurinsa, idan kuma ya himmatu zai aikata wani kyakkywan aiki sai kuma ya aikata shi to Allah zai rubuta masa lada guda goma izuwa ninki ɗari bakwai zuwa ninki ɗayawa. Idan ya himmantu zai aikata mummuna sai kuma bai aikata ba Allah zai rubutamasa kyakkyawa guda ɗaya cikakke a wurinsa, idan kuma ya himmantu da ita (ya’aikatata) to Allah zai rubutamasa mummunan aiki guda ɗaya. Bukhariy [6491] da Muslim [lamba:131] a cikin sahihan litattafansu da wannan harafi. Ka yi dubi, ya kai ɗan’uwa –Allah ya datar da mu, da kai- zuwa ga girman tausasawan Allah ta’alah, kuma ka yi tunani cikin laffuzan wannan hadisin. Kuma faɗinsa (a wajensa ) na yin nuni kan yadda Allah ya bada muhimmanci kan wannan lamarin. Faɗinsa kuma (cikakkiya) don qarfafawa ne, da kuma qara bada muhimmanci. Sai faɗin hadisin dangane da mummunan aikin da bawa ya yi niyyar aikatawa, sa’annan sai ya bar aikata shi (Allah zai rubuta kyakkyawa cikakke a wurinsa ), sai hadisin ya qarfafa maganar da kalmar (cikakke ). (Idan kuma ya aikata ta, to sai ya rubuta mummuna guda ɗaya), a nan kuma, sai ya qarfafi maganar don ya qarantata, ta hanyar amfani da kalmar (guda ɗaya ), ba da kalmar (cikakkiya) ba. Godiya da baiwa na Allah ta’alah ne, ba za mu iya qididdige yabo ba a gare shi. Kuma datarwa na Allah ne! |
Hadith 38 <> Hadisi na 38
<small> --[[40 Hadiths/38|Hadith 38]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_38_.3C.3E_Hadisi_na_38|40]]</small>
# | Hadith 38 | Hadisi na talatin da takwas |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said, “Verily Allah ta’ala has said: ‘Whosoever shows enmity to a wali (friend) of Mine, then I have declared war against him. And My servant does not draw near to Me with anything more loved to Me than the religious duties I have obligated upon him. And My servant continues to draw near to me with nafil (supererogatory) deeds until I Love him. When I Love him, I am his hearing with which he hears, and his sight with which he sees, and his hand with which he strikes, and his foot with which he walks. Were he to ask [something] of Me, I would surely give it to him; and were he to seek refuge with Me, I would surely grant him refuge.’ ” [Al-Bukhari] |
An ruwaito daga AbuHurairata, Allah ya yarda da shi yace, Manzon Allah ﷺََ yace: Allah ta’alah yace: Duk wanda yayi ga ba da waliyyina to na bashi sanarwa yazo yayi yaqi da ni, Bawana ba zai kusance ni dawani abu da na fi qauna sama da abinda na wajabtamasa. Bawana ba zai gusheba yana kusanta ta da nafiloli har sai na qauna ce shi, idan na qaunace shi sai nakasance jinsa da yake ji dashi, da ganinsa da yake ganida shi, hannunsa da yake damqa da shi, da kafarsa dayake tafiya da ita. da Wallahi idan ya roqe ni zan bashi, kuma wallahi idan ya nemi tsarina zan tsare shi. Bukhariy ne ruwaito shi [lamba:6502]. |
Hadith 39 <> Hadisi na 39
<small> --[[40 Hadiths/39|Hadith 39]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_39_.3C.3E_Hadisi_na_39|40]]</small>
# | Hadith 39 | Hadisi na talatin da tara |
---|---|---|
1 |
On the authority of Ibn Abbas (may Allah be pleased with him), that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said: Verily Allah has pardoned [or been lenient with] for me my ummah: their mistakes, their forgetfulness, and that which they have been forced to do under duress. A hasan hadeeth related by Ibn Majah, and al-Bayhaqee and others. [31] |
An ruwaito daga ɗan Abbas Allah ya yarda da shi yace: Manzon Allah ﷺََ yace: “Allah ya yafe wa’al’ummata abinda ta yi dakuskure da wanda ta yi damantuwa da abinda aka tilasta su akansa. Hadisine mai kyau, Ibnu majah ne yaruwaito shi [lamba:2045] da baihakia cikin sunan [7]. |
Hadith 40 <> Hadisi na 40
<small> --[[40 Hadiths/40|Hadith 40]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_40_.3C.3E_Hadisi_na_40|40]]</small>
# | Hadith 40 | Hadisi na arba'in |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abdullah ibn Umar (may Allah be pleased with him), who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) took me by the shoulder and said, “Be in this world as though you were a stranger or a wayfarer.” And Ibn Umar (may Allah be pleased with him) used to say, “In the evening do not expect [to live until] the morning, and in the morning do not expect [to live until] the evening. Take [advantage of] your health before times of sickness, and [take advantage of] your life before your death.” [Al-Bukhari] [32] |
An ruwaito daga Abdullahi ɗan Umar Allah ya yarda da su yace: Manzon Allah ﷺََ yã dã fa kã faɗãta, sannan yace: Ka kasance a duniya tamkar baqo ko kuma wanda yake kan hanya. ɗan Umar (R.A) ya kasance yana cewa: Idan kayi yammaci kar ka jira safiya, idan kuma ka wayi gari to kar ka jira yammaci, ka riqi aikin alheri lokacin lafiyarka saboda lokacin rashin lafiyarka, ka riqi aikin alheri lokacin rayuwarka, saboda ka amfana lokacin mutuwarka, Bukhariy ne ya ruwaitoshi [lamba:6416]. |
Hadith 41 <> Hadisi na 41
<small> --[[40 Hadiths/41|Hadith 41]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_41_.3C.3E_Hadisi_na_41|40]]</small>
# | Hadith 41 | Hadisi na arba'in da ɗaya |
---|---|---|
1 |
On the authority of Abu Muhammad Abdullah bin ’Amr bin al-’Aas (may Allah be pleased with him) who said: The Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said, “None of you [truly] believes until his desires are subservient to that which I have brought.” [Imam an-Nawawi says:] We have related it in Kitab al-Hujjah with a saheeh chain of narrators. [33] |
An ruwaito daga Abu Muhammadu; wato Abdullahi ɗan Amru ɗan Aas Allah ya yarda da su yace: Manzon Allah ﷺََ yace: “ɗayanku ba ya zama mumini har sai son zuciyarsa tana biyayya ga abinda nazo dashi. Hadisine ne ingatacce, mai kyau mun ruwaito shi a cikin littafin Hujja da isnadi ingantacce. |
Hadith 42 <> Hadisi na 42
<small> --[[40 Hadiths/42|Hadith 42]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_42_.3C.3E_Hadisi_na_42|40]]</small>
# | Hadith 42 | Hadisi na arba'in da biyu |
---|---|---|
1 |
On the authority of Anas (may Allah be pleased with him) who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say, “Allah the Almighty has said: ‘O Son of Adam, as long as you invoke Me and ask of Me, I shall forgive you for what you have done, and I shall not mind. O Son of Adam, were your sins to reach the clouds of the sky and you then asked forgiveness from Me, I would forgive you. O Son of Adam, were you to come to Me with sins nearly as great as the Earth, and were you then to face Me, ascribing no partner to Me, I would bring you forgiveness nearly as great as it [too].’ ” It was related by at-Tirmidhi, who said that it was a hasan hadeeth. [34] |
An ruwaito daga Anas ɗan Malik Allah ya yarda da shi yace: Na ji Manzon Allah ﷺََ yana cewa: Allah maɗaukakin sarki yana cewa: Ya kai ɗan Adam! Lallai ba zaka bautamin ba kuma ka sanya rai game da rahamata face nagafarta maka ba tare da nadamu ba. Ya kai ɗan Adam! da ace zunubanka za su cika sashen sama gabaɗaya sannan sai ka nemi gafarata sai in gafarta maka. Ya kai ɗan Adam! da ace zaka zomin da cikin qasa gabaɗaya zunubi ne sannan sai kagamu da ni ba tare da ka haɗani da kowa ba ni kuma zan kawo maka gafara cikin qasa. Tirmizi ne ya ruwaito shi [lamba:3540], Yace: hadisi ne mai kyau, ingantacce. |
Pages in category "40 Hadiths"
The following 10 pages are in this category, out of 10 total.