Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/31

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Links

  1. Suhbah Institute Imam Mahad Tafseer on Quran/31/8

Suratul Luqman 31 in Hausa

# Aya Source
31:1 A. L. M. ha.gumi
31:1 A. L. M. Surah_031.pdf
31:2 wadancan ayoyin littafin ne mai hikima. ha.gumi
31:2 wadannan (harrufan) sun qumshi hujjoji na wannan littafin mai hikimah. Surah_031.pdf
31:3 shiriya da rahama ne ga masu kyautatawa. ha.gumi
31:3 shiriya ce da rahamah ga masu kyautatawa. Surah_031.pdf
31:4 wadanda ke tsai da salla kuma suna bayar da zakka kuma su, suna yin imanin yakini, ga lahira. ha.gumi
31:4 wadanda ke tsai da sallah, kuma suna bayar da zakkah, kuma game da lahira su yaqinai ne. Surah_031.pdf
31:5 wadannan suna a kan shiriya ta daga ubangijinsu kuma wadannan su ne masu babban rabo. ha.gumi
31:5 wadannan suna a kan shiriya ta ubangijinsu, kuma su ne masu babban rabo. Surah_031.pdf
31:6 kuma akwai daga cikin mutane wanda ke sayen tatsuniyoyi domin ya batar da mutane daga hanyar allah, ba da wani ilmi ba, kuma ya rike ta abin izgili! wadancan suna da wata azaba mai wulakantawa. ha.gumi
31:6 akwai daga cikin mutane wanda ke riqon hadisai mara tushe domin su batar da mutane daga hanyar allah ba da wani ilmi ba, kuma su dauke ta abin izgili. wadancan suna da wata azaba mai wulakantawa. Surah_031.pdf
31:7 kuma idan an karanta ayoyinmu a gare shi, sai ya juya baya, yana mai girman kai, kamar dai bai saurare su ba kamar dai akwai wani danni a kan kunnuwansa! to, ka yi masa bushara da azaba mai radadi. ha.gumi
31:7 kuma idan an karanta ayoyinmu a ga dayansu, sai ya juya baya, yana mai girman kai, kamar dai bai saurare su ba, kamar dai akwai wani danni a kan kunnuwansa. to, ka yi masa bishara da azaba mai radadi. Surah_031.pdf
31:8 lalle, wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, suna da gidajen aljannar ni'ima. ha.gumi
31:8 lalle, wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan qwarai, sun cancanci gidajen aljannar ni'ima. Surah_031.pdf
31:9 suna dawwama a cikinsu allah ya yi alkawarin, ya tabbatar da shi. kuma shi ne mabuwayi, mai hikima. ha.gumi
31:9 za su dawwama a cikinsu.wannan shi ne alkawarin allah. kuma shi ne mabuwayi, mafi hikimah. Surah_031.pdf
31:10 (allah) ya halitta sammai, ba da ginshiki wanda kuke gani ba, kuma ya jefa duwatsu masu kafuwa a cikin kasa, domin kada ta karkata da ku kuma ya watsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan muka tsirar a cikinta, daga kowane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa. ha.gumi
31:10 ya halitta sammai ba tare da ginshiqi ba wanda za ku iya gani. kuma ya sanya cakosoba (tsaunika) a cikin qasa, domin kada ta fadi da ku, kuma ya watsa kowance irin halitta a cikinta. muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan muka tsirar a cikinta, kowane nau'i biyu mai ban sha'awa. Surah_031.pdf
31:11 wannan shi ne halittar allah. to ku nuna mini, "mene ne wadanan da ba shi ba suka halitta? a'a, azzalumai suna a cikin bata bayyananna." ha.gumi
31:11 wannan shi ne halittar allah; to, ku nuna mini abin da kuke bauta baicinsa suka halitta. lalle, azzalumai suna a cikin bata bayyananna. Surah_031.pdf
31:12 kuma lalle hakika mun bai wa lukman hikima. (muka ce masa) ka gode wa allah, kuma wanda ya gode, to yana godewa ne domin kansa kawai kuma wanda ya kafirta, to, lalle, allah mawadaci ne, godadde. ha.gumi
31:12 mun bai wa luqman hikimah: (muka ce masa) “ka gode wa allah.” duk wanda ya yi godiya, to yana godewa ne domin kansa. amma wadanda suka kafirta, to, allah mawadaci ne, godadde. Surah_031.pdf
31:13 kuma a lokacin da lukman ya ce wa dansa, alhali kuwa yana yi masa wa'azi, "ya karamin dana! kada ka yi shirki game da allah. lalle shirki wani zalunci ne mai girma." ha.gumi
31:13 kuma a lokacin da luqman ya ce wa dansa, saad da ya ke fadakar da shi, "ya dana, kada ka yi shirki da allah; lalle shirki wani zalunci ne mai girma." Surah_031.pdf
31:14 kuma mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa ta dauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu (muka ce masa) "ka gode mini da kuma mahaifanka biyu. makoma zuwa gare ni kawai take." ha.gumi
31:14 kuma mun yi wasiyya ga mutum dangane da iyayensa. mamansa ta dauki (cikinsa), sai qarfinta ya dinga raguwa. kuma ya dauki shekaru biyu (na dauniya) har ga yayewa. ka gode mini, da kuma iyayenka. zuwa gare ni ne makoma take. Surah_031.pdf
31:15 kuma idan mahaifanka suka tsananta maka ga ka yi shirki game da ni, ga abin da ba ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu da'a. kuma ka abuce su a cikin duniya gwargwadon shari'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare ni, sa'an nan zuwa gare ni makomarku take sa'an nan in ba ku labari game da abin da kuka kasance kuna aikatawa. ha.gumi
31:15 kuma idan iyayenka suka nufa su tilastaka don ka yi shirka da ni, ga abin da ba ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi masu daa. amma ka ci gaba da kyauta masu a cikin na duniya gwargwado. ka bi hanyar wadanda kawai suka mayar da al'amari zuwa gare ni. a qarshe, zuwa gare ni ne makoman dukanku take, sa'an nan zan sanar da ku game da abin da kuka kasance kuna aikatawa. Surah_031.pdf
31:16 ya karamin dana! lalle ita idan gwargwadon kwayar komayya ce ta kasance, to, ta kasance a cikin wani falalen dutse, ko a cikin sammai, ko a cikin kasa, allah zai kawo ta lalle allah mai tausasawa ne, masani. ha.gumi
31:16 ya dana, ka sani cewa, ko da wani abu ta kasance dan mitsili kamar qwayar kamayya ce, a cikicikin dutse, ko da ta kasance a cikin sammai, ko qasa, allah zai kawo ta. lalle allah mai tausasawa ne, masani.” Surah_031.pdf
31:17 ya karamin dana! ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi hakuri a kan abin da ya same ka. lalle, wancan yana daga muhimman al'amura. ha.gumi
31:17 ya dana, ka tsai da sallah. kuma ka yi umurni ga ayyukan qwarai, kuma ka yi hani daga mugunta, kuma ka daure haquri a kan abin da ya same ka. wadannan su ne halaye mafi girma. Surah_031.pdf
31:18 kada ka karkatar da kundukukinka ga mutane, kada ka yi tafiya a cikin kasa kana mai nuna fadin rai. lalle, allah ba ya son dukan mai takama, mai alfahari. ha.gumi
31:18 kada ka nuna wa mutane girman kai, ko ka yi yawo a cikin qasa kana mai nuna fadin rai. allah ba ya son dukan mai taqama, mai alfahari. Surah_031.pdf
31:19 kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. lalle mafi munin sautuka hakika shi ne sautin jakuna. ha.gumi
31:19 kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka sassauta sautinka - mafi munin sautuka shi ne sautin jakuna. Surah_031.pdf
31:20 ashe, ba ku gani ba, cewa allah ya hore muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin kasa, kuma ya zuba ni'imominsa a kanku, bayyanannu da boyayyu? kuma akwai daga mutane wanda ke yin jidali ga al'amarin allah, ba da wani ilmi ba, kuma ba da wata shiriya ba, kuma ba da wani littafi mai haskakawa ba. ha.gumi
31:20 shin, ba ku gani ba, cewa allah ya hore maku abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin qasa, kuma ya zuba ni'imominsa a kanku - bayyanannu da boyayyu? amma duk da haka, wasu daga mutane suna jayayya ga al'amarin allah, ba tare da wani ilmi ba, kuma ba tare da wata shiriya ba, kuma ba tare da wani littafi mai fadakarwa ba. Surah_031.pdf
31:21 kuma idan aka ce musu, "ku bi abin da allah ya saukar," sai su ce: "a'a, muna bin abin da muka sami ubanninmu a kansa." shin ko da shaidan na kiran su ne zuwa ga azabar sa'ir, ha.gumi
31:21 idan aka ce masu, "ku bi abin da allah ya saukar," sai su ce, "a'a, muna bin abin da muka sami iyayenmu ne a kansa." to, shin idan shaidan ne kiran su zuwa ga azabar sa'ir fa?, Surah_031.pdf
31:22 kuma wanda ya mika fuskarsa zuwa ga allah, alhali kuma yana mai kyautatawa, to, lalle ya yi riko ga igiya amintacciya. kuma zuwa ga allah akibar al'amura take. ha.gumi
31:22 wadanda suka miqa wuyansu gaba daya zuwa ga allah, alhali kuma suna masu kyautatawa, to, lalle sun riqi igiya amintacciya. saboda zuwa ga allah ne aqibar al'amura take. Surah_031.pdf
31:23 kuma wanda ya kafirta, to, kada kafircinsa ya bakanta maka rai, zuwa gare mu makomarsu take, sa'an nan mu ba su labari game da abin da suka aikata. lalle allah, masani ne ga abin da ke a cikin kiraza. ha.gumi
31:23 amma wadanda suka kafirta, to, kada kafircinsu ya baqanta maka rai. zuwa gare mu makomarsu take, sa'an nan mu ba su labari game da abin da suka aikata. allah, masani ne ga abin da ke a cikin sadarin zukatansu. Surah_031.pdf
31:24 muna jishe su dadi kadan sa'an nan mu tilasta su ga shiga zuwa azaba kakkaura. ha.gumi
31:24 muna barinsu su, su dan more, saan nan mu tilasta su ga shiga zuwa azaba kakkaura. Surah_031.pdf
31:25 kuma lalle, idan ka tambaye su, "wane ne ya halitta sammai da kasa?" lalle za su ce: "allah ne." ka ce: "godiya ta tabbata ga allah" a'a, mafi yawansu ba su sani ba. ha.gumi
31:25 idan ka tambaye su, "wane ne ya halitta sammai da qasa?" za su ce, "allah ne." ka ce, "alhamduli-allah." amma duk da haka mafi yawansu ba su sani ba. Surah_031.pdf
31:26 abin da yake a cikin sammai da kasa duka na allah kawai ne. lalle, allah shi ne mawadaci, godadde. ha.gumi
31:26 duk abin da ke cikin sammai da qasa na allah ne. allah shi ne mafi wadata, godadde. Surah_031.pdf
31:27 kuma da dai abin da ke a cikin kasa duka, na itace, ya zama alkalumma, kuma teku tana yi masa tawada, a bayansa da wadansu tekuna bakwai kalmomin allah ba za su kare ba. lalle, allah mabuwayi ne, mai hikima. ha.gumi
31:27 idan da za mayar da itatuwan da ke cikin qasa, su zama alqalumma, saannan teku ta yi masa tawada, a kuma qara da tekuna bakwaii kalmomin allah ba za su qare ba. allah mabuwayi ne, mafi hikimah. Surah_031.pdf
31:28 halittarku ba ta zama ba, kuma tayar da ku bai zama ba, face kamar rai guda. lalle, allah mai ji ne, mai gani. ha.gumi
31:28 halittar dukanku da tayar da ku daidai take da na mutum daya. allah mai ji ne, mai gani. allah kadai ne abin bautawa Surah_031.pdf
31:29 ashe, ba ku ga, lalle, allah yana shigar da dare a cikin rana ba, kuma yana shigar da rana a cikin dare kuma ya hore rana da wata kowane yana gudana zuwa a ajali ambatacce kuma lalle allah masani ne ga abin da kuke aikatawa? ha.gumi
31:29 shin, ba ku gani ba cewa allah yana shigar da dare a cikin yini, saannan ya shigar da yini a cikin dare, kuma ya hori rana da wata suna yi maku hidima, kowane yana gudana a cikin kewayar falakinta na qayadedden ajali, kuma cewa allah masani ne ga abin da kuke aikatawa? Surah_031.pdf
31:30 wannan fa domin allah shi ne gaskiya, kuma abin da suke kira wanda ba shi ba, shi ne karya, kuma lalle, a1lah shi ne madaukaki, mai girma. ha.gumi
31:30 wannan ya tabbatar da cewa allah shi ne gaskiya, saannan abin da suke kira wanda ba shi ba, shi ne qarya, kuma, allah shi ne madaukaki, mafi girma. Surah_031.pdf
31:31 ashe, ba ka