1. https://www.bbc.com/future/article/20140421-inside-the-minds-of-the-dead
|
1. https://www.bbc.com/hausa/vert-fut-42184433
|
2. Reading the minds of the ‘dead’
|
2. Ana iya gane aikin kwakwalwar matattu?
|
3. By Roger Highfield 21st April 2014
|
3. Daga Roger Highfield 4 Disamba 2017
|
4. Thousands of patients
|
4. Dubban marasa lafiya
|
5. remain trapped in a vegetative state between life and death.
|
5. na nan a dabaibayin langabun rashin sanin inda kansu yake, a yanayin rai kwakwai, mutu kwakwai (tsakanin rayuwa da mutuwa).
|
6. Three scientists are working to free them, as Roger Highfield reports.
|
6. Manyan masana kimiyya uku na kokarin ceto su, kamar yadda Roger ya kawo rahotanni al'amuran.
|
7. “Imagine you wake up, locked inside a box,” says Adrian Owen.
|
7. "Kaddara ka farka a cikin wani akwati, a cewar Adrian Owen.
|
8. "It's a perfect fit, down to every last one of your
|
8. "Ka ji garau tun daga
|
9. fingers
|
9. kan yatsun hannu
|
10. and toes.
|
10. zuwa yatsun kafa.
|
11. It's a strange
|
11. Lamarin ya yi bambarakwai
|
12. box
|
12. a akwati
|
13. because you can listen to absolutely everything going on around you, yet your voice cannot be heard.
|
13. tunda kana jin komai da ake yi a kewaye da kai, amma ba za a iya jin muryarka ba.
|
14. In fact, the box fits so tightly around your face and lips that you can't speak, or make a noise.
|
14. A gaskiya ma akwati garkame yake kam daure da fuskarka da lebanta ta yadda ba za ka iya magana ba ko wani surutu.
|
15. At first, this feels like a game.
|
15. Da farko, wannan al'amari ya yi kama da wasa.
|
16. Then reality sets in.
|
16. Sai batu na gaskiya.
|
17. You see and hear your family lamenting your fate.
|
17. Kana gani da jin yadda 'yan uwanka ke alhinin makomar da ka samu kanka.
|
18. You're too cold.
|
18. Ka daskare da sanyi.
|
19. Then too hot.
|
19. Sai kuma ka dumame da zafi.
|
20. You're always thirsty.
|
20. Ko da yaushe kana fama da kishirwa
|
21. The visits of your friends and family dwindle.
|
21. Ziyarar abokai da 'yan uwa sai ta ragu.
|
22. Your partner moves on. And there's nothing you can do about it."
|
22. Abokin zamanka shi ma ya dakata. Kuma babu abin da za ka iya yi kan haka."
|
23. Owen and I are talking on Skype.
|
23. Ni da Owen muna tattaunawa a kafar sadarwa ta Skype.
|
24. I’m sitting in London, UK,
|
24. Har yanzu ina nan a Landan, qasar Birtaniya,
|
25. and he’s in another London
|
25. shi ma yana nan a Landan
|
26. three-and-a-half thousand miles away at the University of Western Ontario, Canada.
|
26. kimnanin mil dubu uku da rabi daga Jami'ar Western Ontario ta qasar Canada.
|
27. Owen’s reddish hair
|
27. Jan gashin Owen
|
28. and close-cropped beard
|
28. da gemunsa da aka daddatse
|
29. loom large on my screen
|
29. sun bayyana akan akwatin talabijin dina,
|
30. as he becomes animated describing the torment of those with no voice: his patients.
|
30. inda aka yi mini zayyanarsa tare da kwatanta mini yadda wadanda ba sa iya magana ke shan azaba: marasa lafiyar da yake kula da su.
|
31. People in a “vegetative state”
|
31. Mutanen da "rashin lafiya ta langabar da su"
|
32. are awake yet unaware.
|
32. a farke suke ba tare da saninsu ba.
|
33. Their eyes can open and sometimes wander.
|
33. Idanunsu a bude har a wasu lokutan suka jujjuya.
|
34. They can smile,
|
34. Suna iya yin murmushi,
|
35. grasp another’s hand,
|
35. su kama hannun wani,
|
36. cry,
|
36. su yi kuka
|
37. groan or grunt.
|
37. ko gyaran murya.
|
38. But they are indifferent to a hand clap,
|
38. Sai dai motsin tafa hannu bai dame su ba,
|
39. unable to see or to understand speech.
|
39. ba sa iya gani ko fahimtar magana.
|
40. Their motions are not purposeful but reflexive.
|
40. Motsinsu ba da niyya ko manufa, sai dai kwatsam ya bijiro.
|
41. They appear to have shed their memories,
|
41. Alamu na nuna abin da ke damfare a kwakwalwarsu ya gushe,
|
42. emotions and intentions,
|
42. babu sosuwar zuciya ko kudura niyya,
|
43. those qualities that make each one of us an individual.
|
43. wasu dabi'u da suka ta'allaka a jikin daidaikunmu.
|
44. Their minds remain firmly shut.
|
44. Tunaninsu ya garkame gam.
|
45. Still, when their eyelids flutter open,
|
45. Har yanzu dai, idan idanunsu suka bude,
|
46. you are always left wondering if there’s a glimmer of consciousness.
|
46. sai a barka da mamakin cewa akwai dan burbushin farkawa tattare da su.
|
47. A decade ago,
|
47. Shekaru goma baya,
|
48. the answer would have been a bleak and emphatic no.
|
48. amsar tambaya kan lamari kawai ba a bukatarta ko kuma a ce kawai a'a!
|
49. Not any longer.
|
49. Kada a sake bijiro da ita ko kadan,
|
50. Using brain scanners,
|
50. ta hanyar amfani da na'urar daukar hoton bibiyar kwakwalwa,
|
51. Owen has found that some may be trapped inside their bodies
|
51. Owen ya gano cewa wasu kawai a dabaibaye suke a daure cikin jikinsu,
|
52. yet able to think and feel to varying extents.
|
52. duk da haka suna iya yin tunani har su dan ji wani abu gwargwadon hali.
|
53. The number of patients with disorders of consciousness has soared in recent decades,
|
53. Yawan majiyatan da ke fama da matsalar kasa farfadowa suna karuwa a shekrun nan,
|
54. ironically,
|
54. wani abin mamakin ma shi ne
|
55. because doctors have steadily got better at saving patients with catastrophic injuries.
|
55. likitoci sun samu dabarun ceto marasa lafiyar da suka samu munanan raunuka.
|
56. Today, trapped,
|
56. A yau, majiyatan da jikinsu ke dabaibaye da
|
57. damaged
|
57. jagwabewa
|
58. and diminished minds
|
58. da tsukewar kwakwalwa
|
59. inhabit clinics and nursing homes worldwide –
|
59. sun mamaye asibitoci a fadin duniya -
|
60. in Europe alone the number of new coma cases is estimated to be around 230,000 annually,
|
60. a Turai kawai yawan wadanda suke a some suna kaiwa kimanin 230,000 a kowace shekarta,
|
61. of which some 30,000 will languish in a persistent vegetative state.
|
61. inda daga cikinsu 30,00 ke kasancewa a yanayin langwabewa.
|
62. They are some of the most tragic
|
62. Irin wadanan su ne wadanda suka fi shiga matsanancin hali,
|
63. and expensive artefacts of modern intensive care.
|
63. inda ake tarairayarsu da na'urorin kula da lafiya na zamani masu tsada.
|
64. Owen knows this only too well.
|
64. Owen na da matukar fahimtar lamarin.
|
65. In 1997, a close friend set off on her usual cycle to work.
|
65. A shekarar 1997, wata kawarsa ta kud-da-kud ta ta shi yadda ta saba ta hau keke don zuwa wajen aiki.
|
66. Anne [[[name]] changed] had a weak spot on a blood vessel in her head,
|
66. Anne (wadda aka sauya sunanta) ta samu nakasu a magudanar jininta da ke kaiwa ga kokon kai,
|
67. known as a brain aneurysm.
|
67. wadda aka sani da raunannar jijiyar jinin kwakwalwa.
|
68. Five minutes into her trip,
|
68. Minti biyar da fara tafiyarta,
|
69. the aneurysm burst and she crashed into a tree.
|
69. sai langababbiyar jijiyar makwararar jininta ta fashe, inda nan take ta yi karo da wata bishiya.
|
70. She never regained consciousness.
|
70. Daga nan ba ta sake farfadowa ba.
|
71. The tragedy left Owen numb,
|
71. Wannan musifa ta sa Owen ya shiga zurfin tunani,
|
72. yet Anne’s accident would shape the rest of his life.
|
72. ta yarda hadarin Anne ya kawo masa sauyi tsawon rayuwarsa.
|
73. He began to wonder if there was a way to determine which of these patients were in an unconscious coma, which were conscious and which were somewhere in between?
|
73. Daga nan ya fara jefa alamar tambaya kan marasa lafiyar da ke cikin matsananciyar suma da wadanda sumarsu ba ta ta'azzara ba, da kuma wadanda suka samu kansu a tsakanin al'amuran biyu (matsanaciya da sassaukar suma)?
|
74. That year,
|
74. A wannan shekarar,
|
75. he had moved to the Medical Research Council’s Cognition and Brain Sciences Unit in Cambridge,
|
75. sai ya koma Cibiyar binciken Likitanci da ke nazarin fannoni kimiyyar kwakwalwa a Cambridge,
|
76. where researchers used various scanning techniques.
|
76. inda masu bincike suka yi amfani da dabarun daukar hotuna daban-daban.
|
77. One, positron emission tomography (PET),
|
77. Daya daga cikin dabarun mai lakabin PET
|
78. highlights different metabolic processes in the brain,
|
78. na nuna yadda kwakwalwa ke gudanar da ayyuka,
|
79. such as oxygen and sugar use.
|
79. wadanda suka hada da amfani da iskar oxygen da sarrafa sukari.
|
80. Another, known as functional magnetic resonance imaging (fMRI), can reveal active centres in the brain by detecting the tiny surges in blood flow that take place as a mind whirrs.
|
80. Gudar dabarar kuwa mai lakabin fMRI na nuna sassan kwakwalwa da ke aiki ta hanyar gano dishi-dishin jini da ke kwarara da yawa.
|
81. Owen wondered whether he could use these technologies to reach out to patients,
|
81. Owen ya cika da tunanin yin amfani da wannan fasahar kere-kere ga majiyata,
|
82. like his friend, stuck between sensibility and oblivion.
|
82. irin kawarsa da ke halin rai kwakwai, mutu kwakwai.
|
83. Conscious decision
|
83. Kudurin farfadowa
|
84. Half a century ago,
|
84. Tsawon rabin karni da ya wuce,
|
85. if your heart stopped beating
|
85. idan zuciyarka ta daina bugawa
|
86. you could be pronounced dead even though you may have been entirely conscious as the doctor sent you to the morgue.
|
86. sai a tabbatar da mutuwarka ko da daukacin jikinka na farke sai kawai likitoci su turaka wajen adana gawa (macuware).
|
87. This, in all likelihood,
|
87. Wannan lamarin
|
88. could explain notorious accounts through history of those who ‘came back from the dead’.
|
88. shi ke nuni da cewa a tarihi an sha samun wadanda "suka mutu, suka farfado."
|
89. As recently as 2011,
|
89. Tamkar yadda ta faru a shekarar 2011,
|
90. a council in the Malatya province
|
90. inda a Majalisar Lardin Malatya
|
91. of central Turkey
|
91. da ke tsakiyar kasar Turkiyya
|
92. announced it had built a morgue with a warning system and refrigerator doors that could be opened from the inside.
|
92. ta ba da sanarwar kera macuware mai nakararwa da kofofin sanyaya gawa da ake iya bude su daga ciki.
|
93. The problem is that
|
93. Matsalar dai ita ce
|
94. the scientific definition of “death” remains as unresolved as the definition of “consciousness”.
|
94. har yanzu ma'anar da kimiyya ta bai wa "mutuwa" ba a cimma matsaya kanta ba, tamkar yadda "farkawa" take.
|
95. Being alive is no longer linked to having a beating heart, explains Owen.
|
95. Kasancewa a raye yanzu bas hi da alaka da bugun zuciya, kamar yadda Owen ya bayyana.
|
96. If I have an artificial heart, am I dead?
|
96. Idan ina da zuciyar dashe, shin na mutu ke nan?
|
97. If you are on a life-support machine, are you dead?
|
97. Idan na'urar na tarairayar rayuwarka, ana nufin ka mutu ke nan?
|
98. Is a failure to sustain independent life a reasonable definition of death?
|
98. Gazawar gudanar da harkokin rayuwa a kashin kai na nufin mutuwa ke nan?
|
99. No, otherwise we would all be “dead” in the nine months before birth.
|
99. A'a, sabanin haka lamarin yake, domin da tuni daukacinmu mun "mutu" cikin watanni tara kafin a haife mu.
|
100. The issue becomes murkier
|
100. Lamarin na dada rincabewa
|
101. when we consider
|
101. idan muka yi la'akari da
|
102. those trapped in the twilight worlds between normal life and death –
|
102. wadanda ke dabaibaye a tsakanin rayuwa da mutuwa -
|
103. from those who slip in and out of awareness,
|
103. tun daga kan wadanda suka san inda suke da ma wadanda ba su san inda kansu yake ba,
|
104. who are trapped in a ‘minimally conscious state’,
|
104. wadanda ke dabaibaye a "tsukukun sumar farkawa,'
|
105. to those who are severely impaired in a vegetative state or a coma.
|
105. har zuwa kan wadanda jikinsu ke langabe ko doguwar suma.
|
106. These patients first appeared in the wake of the development of the artificial respirator during the 1950s in Denmark,
|
106. Wadannan majiyatan alamu na nuna a farke suke ta hanyar kakaba musu bututun shaker iska cikin shekarun 1950 a kasar Denmark,
|
107. an invention that redefined the end of life
|
107. wata kirkirar fasaha da ke nuni da karshen rayuwa
|
108. in terms of the idea of brain death
|
108. bisa la'akari da da mutuwar kwakwalwa,
|
109. and created the specialty of intensive care,
|
109. ta hanyar samar da kyakkyawar kulawa,
|
110. in which unresponsive and comatose patients who seemed unable to wake up again were written off as
|
110. inda ake gane marasa lafiyar da suka ki tashi sai a kimanta su a matsayin
|
111. “vegetables” or
|
111. "langababbu" ko
|
112. “jellyfish”.
|
112. "taushin jiki (irin na kifi mai fila-filai - jelly fish)".
|
113. As is always the case when treating patients,
|
113. Kamar yadda aka saba duk sa'adda ake yi wa marasa lafiya magani,
|
114. definitions are critical:
|
114. yanke matsaya na da wahala:
|
115. understanding the chances of recovery,
|
115. wato fahimtar yiwuwar rayuwarsa, tattare da
|
116. the benefits of treatments and so on all depend on a precise diagnosis.
|
116. alfanun maganin da ake yi da sauran al'amuran da suka danganta kan hakikanin cutar da aka gano.
|
117. In the 1960s,
|
117. A shekarun 1960,
|
neurologist Fred Plum
|
masanin sarrafa sakonnin kwakwalwa Fred Plum
|
118. in New York and
|
118. a New York da
|
119. neurosurgeon Bryan Jennett in Glasgow carried out pioneering work to understand and categorise disorders of consciousness.
|
119. mai tiyatar jijiyar laka Bryan Jennett a Glasgow su suka fara gudanar da bincike don gano yadda za a kimanta rukunin farfadowa farkawa.
|
120. Plum coined the term “locked-in syndrome”,
|
120. Plum ya kirkiro lakabin "matsalar dabaibayewa,"
|
121. in which a patient is aware and awake but cannot move or talk.
|
121. inda mara lafiya ya san inda kansa yake a farko, amma ba zai iya motsi ko Magana ba.
|
122. With Plum, Jennett devised
|
122. Tare da Plum, Jenett ya kirkiro
|
123. the Glasgow Coma Scale
|
123. ma'aunin sumar Glasgow (Glasgow Coma Scale)
|
124. to rate the depth of coma,
|
124. don kimanta yanayin suma,
|
125. and Jennett followed up with the Glasgow Outcome Scale
|
125. sai Jennett ya sake samar da wani ma'aunin sakamakon Glasgow
|
126. to weigh up the extent of recovery,
|
126. don kimanta yanayin farfadowa,
|
127. from death to mild disability.
|
127. wato daga mutuwa zuwa 'yar karamar nakasa.
|
128. Together they adopted the term
|
128. Gaba dayansu sai suka rika amfani da lakabin
|
129. “persistent vegetative state”
|
129. “matsanancin langabewar jiki”
|
130. for patients who, they wrote,
|
130. ga marasa lafiyar da suka rubuta
|
131. “have periods of wakefulness when their eyes are open and move;
|
131. "kimar lokacin farfadowarsu da zarar idanunsu sun bude suna motsi;
|
132. their responsiveness is limited to primitive postural and reflex movements of the limbs, and they never speak.”
|
132. tasirin warkewarsu an ta'allaka shi ga motsin gabobi ko karsashin gabar da aka taba, kuma ba sa taba yin magana."
|
133. In 2002, Jennett was among a group of neurologists who chose the phrase
|
133. A shekarar 2002, Jennett na cikin gungun masana aikin kwakwalwa da suka yi furucin
|
134. “minimally conscious”
|
134. "farkawa kadan"
|
135. to describe those who are sometimes awake
|
135. don kwatanta wadanda a wani lokaci suke a farke
|
136. and partly aware,
|
136. tare da dan sanin inda kansu yake,
|
137. who show erratic signs of consciousness so that at one time they might be able to follow a simple instruction
|
137. da ke nuna alamun farkawa ta yarda a wani lokaci za su iya bin umarnin abin da aka ce su yi,
|
138. and another they might not.
|
138. wasu kuwa ba za su iya ba.
|
139. Even today, however, we’re still arguing over who is conscious and who isn’t.
|
139. Har zuwa yau, ana ci gaba da taqaddama kan wane ne ya san inda kansa yake da kuma wanda bai sani ba.
|