Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

'40 Hadiths in English <> Hadisai 40 da Hausa

Arba'una Hadith Sheikh Ja'afar Mahmud Adam YouTube Playlist

Hadith 1 <> Hadisi na 1

# Hadith 1 Hadisi na ɗaya
1 On the authority of Ameer ul-Mu&#8217;mineen (the Commander of the Faithful), Aboo Hafs `Umar ibn al-Khattaab radiAllaahu anhu, who said: I heard the Messenger of Allaah ﷺََ say: An karɓo daga sarkin muminai, Baban Hafs, Umar ɗan Alkhaɗɗabi Allah ya yarda da shi yace: Na ji Manzon Allah ﷺََ yana cewa:
2 Actions are but by intentions and every man shall have only that which he intended. “Dukkan aiyyuka suna tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya;
3 Thus he whose migration (Hijrah to Madeenah from Makkah) was for Allaah and His Messenger, his migration was for Allaah and His Messenger, Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da Manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa.
4 and he whose migration was to achieve some worldly benefit or to take some woman in marriage, his migration was for that for which he migrated. Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce dazai same ta ko kuma wata matar da zai aure ta to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa.
5 It is related by the two Imaams of the scholars of Hadeeth, Aboo `Abdillaah Muhammad ibn Ismaa`eel ibn Ibraheem ibn al-Mugheera ibn Bardizbah al-Bukhaaree Shugabannin maluman da suka rubuta littatafan hadisai ne suka ruwaito shi; Wato: Baban Abdullahi Muhammadu ɗan Isma’ila ɗan Ibrahima ɗan Almugiyrah ɗan Bardizbah,(AlBukhariyy), A cikin ingantattun littatafansu [Sahihul Bukhariyy, [lamba: 1]
6 and Aboo-l-Husain Muslim ibn al-Hajjaaj ibn Muslim al-Qushairee an-Naisaabooree, in their two Saheehs, which are the soundest of compiled books [i.e. the most truthful books after the Book of Allaah, since the Qur’aan is notcompiled’]. Da kuma Abul Husaini Muslimu ɗan Alhajjaju ɗan Muslimu, Alqushairiyyu Annaisaburiyyu. (acikin Sahihu Muslim), [lamba: 1907], waɗanda kuma sune mafi ingancin littatafan da aka rubuta.

Hadith 2 <> Hadisi na 2

# Hadith 2 Hadisi na biyu
1 Also on the authority of `Umar (radi Allaahu ‘anhu), who said: An ruwaito daga Umar Allah ya yarda da shi yace:
2 One day while we were sitting with the Messenger of Allaah ﷺََ there appeared before us a man whose clothes were exceedingly white and whose hair was exceedingly black; Wata rana muna wurin Manzon Allah ﷺََ, Sai wani mutum ya zo mana mai tsananin farin tufafi kuma mai tsananin baqin gashi;
3 no signs of journey were to be seen on him and none of us knew him. He walked up and sat down in front of the Prophet ﷺََ, babu wata alamar tafiya a tattare da shi, har ya zauna kusa da Annabi ﷺََ.
4 with his knees touching against the Prophets ﷺََ and placing the palms of his hands on his thighs he said: Sai ya jingina guiwoyinsa zuwa guiwoyinsa, ya kuma ɗora tafukansa akan cinyoyinsa, yace:
5 “O Muhammad, tell me about Islam. Ya Muhammadu ﷺََ , bani labari akan Musulunci?
6 The Messenger of Allaah ﷺََ said: Islaam is to testify that there is no deity worthy of worship but Allaah and Muhammad is the Messenger of Allaah, manzon allah ﷺََ Yace :Ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne,
7 to perform prayers, to give zakaah, to fast in Ramadaan, and to make the pilgrimage to the House if you are able to do so. kuma ka tsayar da salla, kuma ka bada zakka, kuma ka yi azumin watan ramadana, kuma ka yi hajjin ɗaki; idan ka samu hanyar zuwa gare shi.
8 He said: “You have spoken rightly”; and we were amazed at him asking him and saying that he had spoken rightly. He (the man) said: “Tell me about Eemaan. Sai yace: ka yi gaskiya Sai muka yi mamakinsa yana tambayarsa kuma yana gaskata shi! Sai yace: ka bani labari akan imani?
9 He (the Prophet, ﷺََ ) said: “It is to believe in Allaah, His Angels, His Books, His Messengers, and the Last Day, and to believe in divine destiny (qadr), both the good and the evil of it. Yace: Ka yi Imani da Allah da Mala’ikunsa da littatafansa da Manzanninsa da ranar ƙarshe, kuma ka yi imani da qaddara na alkhairinsa da na sharrinsa.
10 He said: “You have spoken rightly.” He (the man) said: “Then tell me about Ihsaan.” Yace: Kayi gaskiya. Yace: To ka bani labari akan “ihsani”?
11 He (the Prophet, ﷺََ ) said: “It is to worship Allaah as though you see Him, and if you do not see Him, then (knowing that) truly He sees you.” Sai yace: Shine ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa to shi yana ganinka.
12 He said: “Then tell me about the Hour.” He said: “The one questioned about it knows no better than the questioner.” Yace: To ka bani labari akan qiyamah? Sai yace: Wanda ake tambayarsa akanta bai fi wanda yayi tambayar sanin lokacinta ba.
13 He said: “Then tell me about its signs.” Sai yace: To ka bani labara kan alamominta?
14 He said: “That the slave-girl will give birth to her mistress, and that you will see barefooted, naked destitute shepherds competing in constructing lofty buildings.” Sai yace: Baiwa ta haifi uwar gijiyarta, kuma zaku ga marasa takalma tsiraru masu kiyon dabbobi suna yin gini masu tsayi.
15 Then he (the man) left, and I stayed for a time. Sannan sai ya tafi, sai na zauna na wani ɗan lokaci,
16 Then he (the Prophet, ﷺََ ) said: “O `Umar, do you know who the questioner was?” Sa'annan sai yace: Ya kai Umar shin ka san wanene mai yin wannan tambayar?
17 I said: “Allaah and His Messenger know best.” He said: “It was Jibreel, who came to teach you your religion.” Yace: Lallai shi mala'ika Jibrilu ne, yazo muku, domin ya karantar da ku addininku”.

Hadith 3 <> Hadisi na 3

# Hadith 3 Hadisi na uku
1 On the authority of Aboo `Abd ir-Rahmaan `Abdullaah, the son of `Umar ibn al-Khattab radiAllaahu ʻanhumaa, An ruwaito daga Abu abdirrahman, Abdullahi ɗan Umar ɗan Alkhaɗɗabi Allah ya yarda da su
2 who said: I heard the Messenger of Allaah صلى الله عليه وسلم say: ya ce: Naji Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yana cewa:
3 Islam has been built on five [pillars]: “An gina musulunci akan abubuwa guda biyar;
4 testifying that there is no deity worthy of worship except Allaah and that Muhammad is the Messenger of Allah, Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu manzon Allah ne,
5 establishing the salaah (prayer), da tsayar da salla,
6 paying the zakah (obligatory charity), bada zakka,
7 making the Hajj (pilgrimage) yin hajji,
8 and fasting in Ramadan. da azumin watan ramadana.

Hadith 4 <> Hadisi na 4

# Hadith 4 Hadisi na huɗu
1 On the authority of Aboo `Abd ir-Rahmaan `Abdullaah ibn Mas`ood (radiAllaahu anhu), who said: An ruwaito daga Abiy-abdurrahman, Abdullahi dan Masʼud Allah ya yarda da shi
2 The Messenger of Allahصلى الله عليه وسلم and he is the Truthful, the Believed, narrated to us: yace: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya bamu labari, kuma shi ne mai gaskiya abun gaskatawa:
3 Verily the creation of each one of you is brought together in his motherʼs womb for forty days in the form of a nutfah (a drop), Lallai ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwanaki arbaʼin yana maniyyi,
4 then he becomes an ʻalaqah (clot of blood) for a like period, Saʼannan sai ya kasance jini misalin haka,
5 then a mudghah (morsel of flesh) for a like period, sannan sai ya kasance tsoka misalin haka,  
6 then there is sent to him the angel who blows his soul into him Sannan sai a turo Malaʼika zuwa gare shi sai ya busa masa rai,
7 who is commanded with four matters: sai a umurce shi da kalmomi guda huɗu:
8 to write down his rizq (sustenance), a rubuta arzikinsa
9 his lifespan, da ajalinsa,
10 his actions, da aikinsa,
11 and whether he will be happy or unhappy (i.e. whether or not he will enter Paradise). da kuma shaƙiyyi ne ko mai rabo ne,
12 By the One, other than Whom there is no deity,   Na rantse da wanda babu wani abin bautawa idan ba shi ba,
13 verily one of you performs the actions of the people of Paradise Lallai ayanku zai aikata aiki irin na ʻyan aljanna
14 until there is but an arms length between him and it, har sai ya zama babu wani abu a tsakaninsa da tsakaninta sai ziraʼi,
15 and that which has been written overtakes him, sai littafi ya rigaye shi
16 and so he acts with the actions of the people of the Hellfire and thus enters it; sai yayi aiki irin na ʻyan wuta sai ya shige ta.

Hadith 5 <> Hadisi na 5

<small> --[[40 Hadiths/5|Hadith 5]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_5_.3C.3E_Hadisi_na_5|40]]</small>

# Hadith 5 Hadisi na biyar
1 On the authority of the Mother of the Faithful, Umm `Abdillaah `Aaishah (radi Allaahu ʻanhaa) , who said: The Messenger of Allaah :said صلى الله عليه وسلمََ An ruwaito daga Ummul Muʼuminina Ummu Abdullahi Aishatu Allah ya yarda da ita tace... manzon Allah ya ce:
2 “He who innovates something in this matter of ours [i.e. Islaam] that is not of it will have it rejected [by Allaah]”. Wanda ya ƙirƙiro wani abu daga cikin lamarinmu wanda abin da babu shi cikinsa to a mayar masa
3 Whoever performs a deed that is not in accordance with our matter will have it rejected. A wata riwayar Muslim: “Wanda ya aikata wani aikin da babu umarninmu a kai to a mayar masa.

Hadith 6 <> Hadisi na 6

<small> --[[40 Hadiths/6|Hadith 6]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_6_.3C.3E_Hadisi_na_6|40]]</small>

# Hadith 6 Hadisi na shida
1 On the authority of Aboo `Abdillaah an-Nu`maan the son of Basheer (rA), who said: I heard the Messenger of Allah ﷺََ peace and blessings be upon him, say:

Verily, the lawful is clear and the unlawful is clear, and between the two of them are doubtful matters about which many people do not know.

Thus he who avoids doubtful matters clears himself in regard to his religion and his honour, but he who falls into doubtful matters eventually falls into that which is unlawful, like the shepherd who pastures around a sanctuary, all but grazing therein. Truly every king has a sanctuary, and truly Allah's sanctuary is His prohibitions. Truly in the body there is a morsel of flesh, which, if it be whole, all the body is whole, and which, if it is diseased, all of [the body] is diseased. Truly, it is the heart.

An ruwaito daga abu Abdullahi; Nuumanu ɗan Bashir, Allah ya yarda da su yace: Na ji Manzon Allah ﷺََ yana cewa, “Lallai halal a bayyane yake, kuma lallai haram a bayyane yake,

kuma a tsakaninsu akwai alamura masu rikitarwa waɗanda dayawa daga cikin mutane ba su san su ba.

Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa hakika ya nemi kuɓutar da addininsa da mutuncinsa, Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ya auka cikin haram.

Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge, yayi kusa ya shiga (kiwo) a cikinsa, Ku saurara! Kowane sarki yana da iyaka,

Ku saurara! iyakar Ubangiji itace abubuwan da ya haramta, Ku saurara! Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru, idan ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! ita ce zuciya.

Bukhariy [[[lamba]]:52] da Muslim [[[lamba]]:1599] ne suka ruwaito shi.

Hadith 38 <> Hadisi na 38

<small> --[[40 Hadiths/38|Hadith 38]] of [[:Category:40_Hadiths#Hadith_38_.3C.3E_Hadisi_na_38|40]]</small>

# Hadith 38 Hadisi na talatin da takwas
1 On the authority of Sufyan bin Abdullah (may Allah be pleased with him) who said:


"I said, 'O Messenger of Allah, tell me something about Islam which I can ask of no one but you.'

He (peace be upon him) said, 'Say "I believe in Allah" — and then be steadfast. [Muslim][1][2]

An ruwaito daga Abu amrin, ko abiy Amrata, sufyan ɗan Abdullahi Allah ya yarda da shi yace:


Nace: Ya Manzon Allah ﷺَََ faɗa min wata Magana a cikin addinin musulunci wanda ba zan sake tambayar waninka ba game da ita?

Sai yace: Ka ce "Na yi imani da Allah" sannan ka daidaitu.

Source

Pages in category "40 Hadiths"

The following 10 pages are in this category, out of 10 total.