Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/Dadin Kowa 1

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 07:47, 15 January 2022 by Admin (talk | contribs)

Source Video Error creating thumbnail: Unable to save thumbnail to destination

# English Hausa
1 NAZIR: Mom. NAZIR: Umma.
2 UMMA: The issue I want to discuss with you is whether you have met with Fauziyya or not. UMMA: Yauwa. Dama maganan da nake so mu yi. Ka je gun Fauziyya kuwa?
3 NAZIR: I swear, Mom, I have not gone. NAZIR: Wallahi, Umma ban je ba.
4 UMMA: Why? I am asking you. UMMA: Sobada me? Tambayan ka nake, Sobada me?
5 NAZIR: Please, Mom, put this issue aside! NAZIR: Umma, ni dan Allah ki bar maganan nan.
6 UMMA: Shut up! What do you mean I should stop talking about this? This directive is coming from your father. You better go and sort it out with that girl to make your father happy in this house. UMMA: Ka ga, tsaya. Wane irin a bar maganan nan? Umarnin fa mahaifinka ne. Ya Kamata ka je ku daidaita da yarinyan nan bari in gaya maka, domin a samu a faranta wa mahaifinka rai a gidan nan.
7 NAZIR: Honestly, Mom, I cant. NAZIR: Gaskiya, Umma ni ba zan iya ba.
8 UMMA: Nazir? You have the nerve to tell me that? Let me tell you that you better make an effort to reconcile with that girl. UMMA: Nazir, ni za ka kare wa kallo, ka ce da ni ba za ka iya ba? To, bari in gaya maka, kayi kokari ka je ku daidaita da yarinyan nan.
9 NAZIR: Why, Mom? The girl is Alawiyyas friend. She is her close friend. NAZIR: Haba Umma, yarinyan fa kawar Alawiyya ce. Aminiyarta ce fa.
10 UMMA: There is no deity worthy of worship except Allah, and Muhammad, peace and blessings of God be upon he who is the messenger of God. OK, in which verse of the Koran did you see that if she is a friend of Alawiyya you will not go to visit her to settle down? OK, let me tell you, in my position as your mother, I am directing you to meet with this girl, so that your father can be a happy man in this house. UMMA: La ilaha illallah Muhammadan Rasulallahi Salallahu alayhi wa sallam. To, a wane hadisin ka gani, ko aya ka gani in kawar Alawiyya ce ba za ka je wurin ta ba ku daidaita? To, bari in gaya maka. A matsayina na mahairfiyarka, na ba ka umarni ka je ku daidaita da yarinyar nan. Bari in gaya maka, domin mu samu farin cikin mahairfinka a cikin gidan nan.
11 NAZIR: Fauziyya is a very close friend of Alawiyya. NAZIR: Umma, Fauziyya nan fa aminiyar Alawiyya ce fa, kut-da-kut fa.
12 UMMA: Look, Nazir, I gave birth to you after carrying you in my womb, and you have the nerve to question my directives? UMMA: Yanzu, Nazir, in haife ka da cikina, ina gaya maka magana kana ba ni amsa?
13 NAZIR: Mom, for Gods sake, is this appropriate? In my position, someone has to choose a wife for me? Come on, Mom? NAZIR: Umma, yanzu fisabilillahi ya dace? Wai ni kamana sai an zaban man matar da zan aura? Haba, Umma.
14 UMMA: So, you have the nerve to speak to me this way? Certainly, you have become stubborn. Children of this generation! UMMA: Ni kake gaya wa wannan maganganu? Lallai, wuyanka ya yi kauri.‘Yayan zamani.
15 NAZIR: Mom, for Gods sake, think about it, the tradition of a forced marriage was a thing of the past. Even in the past, let alone now, these things were done in the villages, Mom. Think about it, Mom, for Gods sake. NAZIR: Umma, don Ya Rasulillahi, ki duba wanan abun ki ga. Ai a da ne ake wa mutane auren dole, ba yanzu ba. A da din ma, a kauye ake wannan abubuwan, ba yanzu ba Umma. Don Allah Umma, ki duba wannan abun mana Umma.
16 UMMA: This generation! Thank you. I gave birth to you. Well done. UMMA: Zamani! Na gode. In haifa ka da cikina . . . madalla.
17 NAZIR: Mom, for Gods sake, stop crying, Mom. OK, be patient, OK, I will go. That is all. I hear you. I have to go. Mom, for Gods sake, dont cry. NAZIR: Umma, don Allah ki dena kuka, Umma. To, ki yi hakuri, to, zan je. Shike nan. Na ji za ni. Don Allah Umma, ni kar ki yi kuka.
18 UMMA: Nazir, why did we have to get to this point? And you know how the issue is coming between me and malam? He repeatedly says that I am taking your side. UMMA: Haba Nazir, ya za ayi wannan abun? Ka san yaddda nake da Malam a gidan nan a gameda wannan. Kullum, kullum ce wa yake ni nake daure maka gindi a maganan nan.
19 NAZIR: Be patient, OK, I will go, be patient. Mom, for Gods sake, dont cry, be patient. Mom, if you weep because of me, I will not be happy. I urge you to calm down, Mom, because of the dignity of God. NAZIR: Ki yi hakuri, to zan je, ki yi hakuri. Umma don Allah kar ki yi kuka, ki yi hakuri. Umma in kika zubar ma ni da hawaye . . . ai ba zan ji dadi ba. Don girman Allah, Umma ki yi hakuri.
20 UMMA: OK, try to go, so you can sort it out. UMMA: To, ka yi kokari, ka je ku daidaita.
21 NAZIR: I will go, Mom. NAZIR: Zan je umma.
22 I. B.: Hey, dude! I. B.: Aaa, gayi!
23 NAZIR: Uh-huh. NAZIR: Hm mmm.
24 I. B.: Whats going on? I. B.: To, ya aka yi ne?
25 NAZIR: I. B., Im fine, I swear to God. What is the matter? Oh my God, damn. How is the town? NAZIR: I. B. fine wallahi. Ya aka yi ne? Wayyo Allahna, kash.Ya garin ne?
26 I. B.: Normal. I hope you have finished writing the song for us. I. B.: Normal. Ina fatan dai ka gama rubuta mana wannan wakar ko?
27 NAZIR: Hey! I swear to God, I havent written the song. NAZIR: Kai! Wallahi ban . . . wallahi ban rubuta wakar nan ba.
28 I. B.: Hey! I swear to God, you are very, very slow! I. B.: Kai! Kana da mugun slow wallahi tallahi.
29 NAZIR: Dude, it is not about being slow. I just dont have the inspiration for the song. Do you want me to write it anyhow? NAZIR: Kai, ba wai slow ba ne. Ba ni da inspiration na wakar nan. To, so kake in rubuta anyhow kawai?
30 I. B.: No . . . I dont mean that. I. B.: Ah ah . . . I dont mean that.
31 NAZIR: Oh, gosh! My brain is completely blocked. I swear to God that I have developed writers block. NAZIR: Ha haa alakakai, habakwakwalwata ce gabadaya ta cushe. Wallahi na sa mu writers block.
32 I. B.: I dont understand! I. B.: Ban gane ba?
33 NAZIR: I have a problem at home. This is what is contributing to putting me into this situation. NAZIR: Matsala nake da shi a gida. So shi yake contributing ya sa ni a cikin wannan yanayin wallahi.
34 I. B.: You know what? There are certain things in life that you have to ignore. Excessive thinking could cause hypertension in a young man such as you. And this can be a problem. I. B.: Ka gane, to akwai abubuwan da yakamata fa a rayuwa fa kana kauda kanka. Soboda, ka ga yanzu zai iya zame ma matsala, karshe a ce gaye kamar ka ya kamu da hawan jini. Ka ga ai da matsala.
35 NAZIR: I. B., there are some things that you can forget, there are some things that you cant forget. NAZIR: I. B., akwai abun da za ka iya mantawa da shi, akwai abun da za ka iya mantawa da shi ba.
36 I. B.: Certainly! I. B.: Haka ne.
37 NAZIR: I. B., just look at me, for Gods sake, someone like me, a woman should be chosen for him to marry? I am serious. This is not something to laugh at. NAZIR: Wai don Allah, I. B. ka kalle ni. Wai a ce kamar ni, ni ne za a zaban wa ma matan da zan aura? Am serious. Wannan ba abu ne na dariya ba.
38 I. B.: OK, who is she? I. B.: To, wannan wace ce?
39 NAZIR: Certainly, it is Fauziyya, the girl that I dont give a damn about. NAZIR: Wannan yarinyar mana, wai waceceahh Fauziyya ta ke, ko wa?
40 I. B.: OK, I dont see any reason for concern, because a woman has been given to you. Is this the reason why you are troubling yourself? I. B.: To, ni ban ga abun damuwa don an ba ka mace, kake wani damun kanka.
41 NAZIR: Hey, guy, in this century, someone is planning to choose a wife for you? So I would have a forced marriage? We have passed that century. It was done in the past. Now it is not done. Even then, women were forced into marriage, not men. But now we are in the computer age, of course. NAZIR: Haba guy, a wannan karnin da muke ciki? A ce wai, za a zaba ma matar da za ka aura? Za ayi ma auren dole kenan? An wuce wannan karnin. A da ake haka. Yanzu ba a haka. A da din ma a mata fa ake yi wa ba maza ba. Amma yanzu haba we are in a computer age mana.
42 I. B.: OK, now, what have you decided? I. B.: To, yanzu, me ka yanke?
43 NAZIR: OK, what choice do I have, other than to obey the orders of Mom and Dad because I dont want them to get upset? That is the only reason I will make a move. Otherwise, I swear to God, I will not. NAZIR: To, me zan yanke? Kawai na dai bi umarnin Umma ne da Dad, saboda bana son ransu ya baci kawai shi ya sa zan je. Amma in ba haka ba, da wallahi ba zan je ba.
44 I. B.: That is what I see. Do you know what we should do? I. B.: Watau ni abun da na gani. Ka san mai yakamata mu yi?
45 NAZIR: No! NAZIR: Ah ah.
46 I. B.: Let us pray so that God will guide us to make the best decision. I. B.: Mu yi addua, Allah ya zaba mana mafi alkhairi.
47 NAZIR: Amen. NAZIR: Amin.
48 I. B.: Just go. Probably the girl wont like you. I. B.: Kawai, ka je ka kawai. Ba ma Lallai ne a ce yarinya ta ce tana son ka ba.
49 NAZIR: Yeah, it is very likely! OK, man, how will I approach her? Why cant you accompany me later? NAZIR: Kuma haka ne fa. To, mutumina ya za ayi? Mu je ka raka ni mana anjima?
50 I. B.: Oh, no! Honestly, I dont have time. I have some errands to run. I. B.: Kai! Gaskiya, ba ni da lokaci. Ina da, da wata sabga da zan je in yi.
51 NAZIR: Malam, for Gods sake, what kind of errands do you have? Please, lets go together later. NAZIR: Malam, don Allah wace sabga kake da ita? Don Allah mu je ka raka ni anjima.
52 I. B.: Oh, no way! It has been three weeks now since I have seen Jamila. And if I call, she doesnt answer. I. B.: Kai, ina! Jamila, yau ya fi sati uku kenan ba ta fito min hira ba. Sannan in na kira ta ba ta dagawa.
53 NAZIR: OK, what happened? What happened between you two? NAZIR: To, me ya faru? me ya hada ku?
54 I. B.: It is most likely because she is mad that I did not buy her the bridesmaids dress for her friends wedding. I. B.: Ba zai wuce wannan haukan bukin kawarta ta ba, da ban yi mata ba.
55 NAZIR: Ha, my man, that has always been your problem. You are stingy! Otherwise, for Gods sake, why cant you provide her with more money for the wedding dress she wanted? NAZIR: Ha, mutumina kai dama matsalana da kai mako. In ba haka ba, haba don Allah. Dan ankon nan, a ba su mana?
56 I. B.: You know what? I have decided on a solution. I. B.: Ka san meye? Akwai ma shawarar da na yanke.
57 NAZIR: OK! NAZIR: Ok.
58 I. B.: The family of the younger sister of her father knows about our relationship. Are you following me? I. B.: Akwai gidan kanwar Babanta, ta san ni da ita. Ka gane?
59 NAZIR: Yes. NAZIR: Ok.
60 I. B.: OK, I will explain to her, so that she will not interpret my keeping away from the girl as disrespect to the family. I. B.: To, zan je kawai, in kora mata bayani. Soboda kar su ga na janye, su ce na yudare su.
61 NAZIR: Oh, you know what? Please, just ignore her. Come and go along with me, so that when we come back, tomorrow I will also go with you to see yours. NAZIR: Haa. Yanzu dai ka gane! Don Allah ka share ta mu je ka raka ni. In ya so, idan muka dawo, gobe ba sai in raka ka wajen ta ba?
62 I. B.: No, you know what, just go. I will be on my way now. I only came to ask for your companionship, so we can go together. But it appears you also have your own problem. I have to leave now! I. B.: Ah ah ka gane, to, kawai ka je kawai ni yanzu ka gane, ni ma kawai warewa zan yi. Dama zuwa na yi, in fada ma za ka raka ni. To kuma tun da kai ma ga naka matsalar. Ni yanzu zan wucewa kawai zan yi.