Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/042 positive thinking make you lazy

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 00:29, 23 June 2017 by Admin (talk | contribs) (Created page with "== #:''Positive thinking can make you too lazy to meet your goals [http://www.bbc.com/capital/story/20161011-positive-thinking-can-...")
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

#:Positive thinking can make you too lazy to meet your goals [1] <> Sa rai da nasara na iya kawo lalaci; Sa rai da nasara na taimakawa amma kuma zai iya kashe gwiwa [2]

#:Want to succeed? Your optimism might be getting in the way. [3] <> Ka na son ka yi nasara? Me yiwuwa ne fata nagari ke hana ka cimma buri [4]

#: About fifteen years ago, [5] <> Kimanin shekaru 15 da su ka wuce [6]

#: when entrepreneur Michael Stausholm started a business with a friend, [7] <> lokacin da Michael Stausholm ya kafa wani kamfani tare da abokinsa, [8]

#: his partner painted a rosy picture of the future of the business and promised him a lot of success. [9] <> abokin ya nuna masa cewa kamfanin zai samu daukaka kuma kasuwancinsu zai yi riba. [10]

#: Stausholm believed him [11] <> Stausholm ya amince da bayanin, [12]

#: and felt uplifted, [13] <> kuma haka ya kara masa kwarin gwiwa [14]

#: as if saying it would will it to be so. [15] <> har ya ji kamar fadar daidai take da cikawa. [16]

#: Thinking positive, after all, is a common step to success, right? [17] <> Ko ba komai ai an ce tunanika, kamanninka ko? [18]

#:Positive thinking is something in the DNA of most entrepreneurs,” [19] <> "Sa rai da nasara, dabi'a ce da ta ratsa jinin mafi yawan masu kafa kamfanonin kansu," [20]

#: says Stausholm, who is based in Copenhagen and who previously worked for shipping company Maersk [21] <> in ji Stausholm, mazaunin Copenhagen wanda ya taba yin aiki a kamfanin safarar jiragen ruwa na Maersk [22]

#:and then went on to consult for large companies on sustainability issues. [23] <> inda daga bisani ya zama mai bada shawara ga manyan kamfanoni kan abubuwan da suka shafi dorewar harkokinsu. [24]

#:But when the business fell apart, he learned an important lesson. [25] <> Amma lokacin da kamfaninsu ya karye, ya koyi darasi mai muhimmanci. [26]

#:Theres a downside to the power of positivity. “Just being positive and happy go lucky is not going to workit has to be mixed with realism,” he says. [27] <> Wato sa rai da samun nasara shi ma ya na da tasa illar. "Sa rai da samun nasara kurum ba zai kai ka ko'ina ba - sai ka hada da kallon gaskiyar lamari". [28]

#:The power of positive thinking has been a guiding principle for business leaders at least since 1936 [29] <> Sa rai da samun nasara na cikin abubuwan da jagororin kamfanonin kasuwanci su ka sa gaba akalla tun a 1936 [30]

#:when Napoleon Hill published Think and Grow Rich. [31] <> lokacin da Napoleon Hill ya wallafa littafin 'Think and Grow Rich'. [32]

#:Two decades later Norman Vincent Peale wrote The Power of Positive Thinking, [33] <> Bayan shekaru 20 kuma Norman Vincent Peale ya rubuta 'The power of Positive Thinking', [34]

#:which has sold more than 21 million copies worldwide, [35] <> wanda kawo yanzu an sayar da fiye da kofe miliyan 21 a fadin duniya. [36]

#:and more recently Rhonda Byrnes The Secret has gripped business leaders and others with its promises of success based on positive thinking. [37] <> A baya-bayan nan kuma Rhonda Byrne ta rubuta 'The Secret' wanda shi ma yake kara jan hankalin masu kamfanonin kasuwanci game da muhimmancin sa rai da samun nasara. [38]

#:According to these positive-thinking tomes, [39] <> A cewar wadannan littattafan sa rai da samun nasarar, [40]

#:negative thoughts or doubts stand in the way of success. [41] <> shakka ko tunanin rashin nasara na zama kalubale ga samun nasarar kasuwanci. [42]

#:But, in fact, a new crop of research [43] <> Sai dai kuma sababbin binciken da aka gudanar a baya-bayan nan [44]

#:finds that positive thinking has its limits[45] <> na nuna cewa sa rai da samun nasara na da iyakarsa- [46]

#:and even brings its own pitfalls. [47] <> kai ya na ma kawo matsaloli. [48]

#:Positivity could be limiting your success. The seductive power of fantasy [49] <> Yaudarar kai [50]

#:Gabriele Oettingen, a professor of psychology [51] <> Gabriele Oettingen, farfesar nazarin halayyar dan Adam [52]

#:at New York University who wrote Rethinking Positive Thinking: Inside the New Science of Motivation, [53] <> a jami'ar New York, wacce ta rubuta littafin 'Rethinking Positive Thinking: Inside the New Science of Motivation', [54]

#:says that when she started studying positive thinking, [55] <> ta ce lokacin da ta fara nazarin sa rai da samun nasara, [56]

#:she discovered that energy, measured by blood pressure, [57] <> ta gano cewa karfin bugawar jinni [58]

#:drops when people generate happy fantasies about the future [59] <> na raguwa a duk lokacin da mutane su ke kyakkyawan zaton cewa za su samu rayuwa mai kyau a gaba [60]

#:like landing a job or earning money. [61] <> kamar samun aikin yi ko samun karin kudi. [62]

#:The problem is people dont get up their energy to fulfil their wishes,” says Oettingen. [63] <> "Matsalar ita ce mutane ba sa zage damtse su yi kokarin cika burikansu," in ji Oettingen. [64]

#:Often [65] <> Mafi yawan lokuta, [66]

#:when people fantasise about achieving their goals [67] <> idan mutane su ka fara mafarkin cimma burinsu [68]

#:they may not exert enough effort to actually achieve them, she says. [69] <> sai su kasa zage damtse wurin ganin sun biya bukatunsu. [70]

#:Oettingen found, for example, that two years after university graduates fantasised about getting a job, [71] <> Alal misali, Oettingen ta gano cewa, shekaru biyu bayan dalibai sun kammala jami'a da kyakkyawan zaton samun ingantaccen aiki, [72]

#:they ended up earning less and receiving fewer job offers than those graduates who were more filled with doubt and worry. [73] <> sai ka tarar su na aikin da ba su kai na daliban da suka kammala jami'a da fargabar samun aiki ba. [74]

#:It turns out they also sent out fewer job applications. [75] <> Masu kyakkyawan zaton ba sa aikawa da takardun neman aiki da yawa kamar na masu fargabar ba za su samu yadda su ke so ba. [76]

#:They fantasise about it and then feel already accomplished and relax,” [77] <> Ta ce; "Idan su ka yi tunanin samu, sai su ji kamar ma burinsu ya riga ya cika," [78]

#:and lose the motivation it takes to make things happen, she says. [79] <> hakan ke karya musu lagon ci gaba da kokarin nema. [80]

#:Nimita Shah, the director of the London-based group The Career Psychologist, [81] <> Nimita Shah, darakta a kamfanin nazarin halayyar bil'adama kan batutuwan da su ka shafi sana'a da ke birnin London 'The Career Psychologist', [82]

#:says people often come in feeling frustrated about [83] <> ta ce mutane da daman a zuwa wurinsu ne da takaicin cewa [84]

#:not being able to manifest their wishes [85] <> sun kasa cimma muradunsu [86]

#:and then they feel guilty [87] <> kuma sai su fara zargin kansu [88]

#:about having negative thoughts, worried that their downbeat thinking is part of the problem. [89] <> cewa tunanin rashin nasarar da su ke yi na da alaka matsalar da suke samu. [90]

#:Its similar to having an immediate diet quick fix,” says Shah. [91] <> Shah ta ce; "Fata nagari na iya kawo kaimi na dan lokaci, [92]

#:Fantasising about the future may help create a short-term boost, butin the long term it adds to people feeling worse”. [93] <> amma ya na sa mutane jin ba dadi idan tafiya ta yi nisa." [94]

#:Naturally hardwired [95] <> Haka Allah ya yi mu [96]

#:So, should we be worried and thinking the worst is around the corner more of the time? [97] <> Idan haka ne, kamata ya yi ke nan kullum mu kasance cikin fargabar cewa akwai matsala a cikin duk abubuwan da zamu yi? [98]

#:That could be tough. [99] <> Abin da kamar wuya. [100]

#:Optimism is embedded in the human psyche, [101] <> Fata nagari wani bangare ne na dabi'ar mutane, [102]

#:says Tali Sharot, author of The Optimism Bias [103] <> a cewar Tali Sharot, marubuciyar 'The Optimism Bias' [104]

#:and director of the Affective Brain Lab, a London-based group [105] <> kuma darakta a cibiyar bincike ta 'Affective Brain Lab' [106]

#:that studies how emotions affect the brain. [107] <> wacce ke nazarin yadda tunani yake tasiri akan kwakwalwa. [108]

#:She had been trying to study the impact of negative events on emotion [109] <> Ta na kokarin gano tasirin mummunan zato ne [110]

#:when she stumbled across the idea that people are naturally hardwired to think positively. [111] <> lokacin da ta gano cewa an gina halittar mutane ne kan kyakkyawan zato. [112]

#:In her initial experiments [113] <> A gwaje-gwajenta na farko, [114]

#:she asked people to imagine future negative scenarios [115] <> ta nemi mutane da su yi hasashen faruwar wani mummunan abu a rayuwarsu [116]

#:such as relationship breakups or losing a job. [117] <> kamar batawa da masoyansu ko kuma korarsu daga aiki. [118]

#:She found that people would automatically change the negative experience to a positive one[119] <> Sai ta gano cewa mutane na maye gurbin mummunan lamari da kyakkyawan zato- [120]

#:they would say, for example, that they broke up with their partner and found an even better one. [121] <> misali su kan ce, na bata da masoyina amma na samu wanda ya fi shi. [122]

#:It ruined my experiment,” says Sharot, [123] <> "Hakan ya bata min bincikena" in ji Sharot, [124]

#:but she realised that people have an inherent bias towards optimism. [125] <> amma ta gano cewa mutane sun fi karkato ga fatan alheri. [126]

#:They imagine the future to be better than the past,” she says. [127] <> Ta ce; "Su kan dauka cewa gaba tafi baya kyau." [128]

#:That sort of optimism bias, [129] <> Wannan sa rai da samun nasara, [130]

#:which Sharot calculates exists in 80% of the population regardless of culture or country, [131] <> wanda Sharot ta kiyasta cewa ana samunsa a kaso 80% na al'ummar kowacee kasa, [132]

#:helps people get motivated in the first place. [133] <> na taimakawa wurin ingiza mutane su yi abubuwan da su ka kamata. [134]

#:Studies also show that optimists live longer and are more likely to be healthier. [135] <> Sakamakon bincike ya kuma nuna cewa masu kyakkyawan fata sun fi samun tsawon rai da ingantacciyar lafiya. [136]

#:Positive thoughts, she says, can also become a self-fulfilling prophecy. [137] <> Ta kuma kara da cewa fata nagari na iya taimakawa mutane wurin gyara rayuwarsu; [138]

#:People who believe they are going to live longer may end up eating healthier and exercising. [139] <> wato wadanda su ke sa ran ganin su na motsa jiki tare da cin abinci mai kyau su kan zama masu yin hakan. [140]

#:And ingrained optimism bias also helps people prevail in the face of dire circumstances. [141] <> Haka kuma sa rai da samun nasara shi ke bai wa mutane damar jurewa idan suka samu koma baya. [142]

#:But the optimism bias also tends to cause people to underestimate risk. [143] <> Sai dai kuma wannan kyakkyawan fatan na sa mutane su raina hatsarin da suke fuskanta. [144]

#:That means for all its upside, we also, [145] <> Wannan na nufin kodayake sa rai da samun nasara na da rana, duk da haka ya na iya jawo mu kasa gane, [146]

#:say, underestimate the amount of time and money a project will take or how a new pair of shoes will make us happy. [147] <> alal misali, yawan kudi da lokacin da muke bukata wurin kafa wani sabon kamfani. [148]

#:Embracing your inner negative Nelly [149] <> Ciza-ka-busa [150]

#:But if our natural inclination is to be sunny in our thinking, [151] <> Tun da yake an halicce mu ne bisa tsarin yi wa kanmu kyakkyawan fata, [152]

#:it will take practice to take on board just enough negative to help offset those optimism blinders. [153] <> ashe ke nan sai mun tarbiyyantar da kanmu wurin gano matsalolin da zamu iya fuskanta a kokarin cimma nasarar abinda muka sa gaba. [154]

#:Using her two decades of research, [155] <> Bayan binciken fiye da shekaru 20, [156]

#:Oettingen developed a tool called WOOP, [157] <> Oettingen ta kirkiro wani ma'auni da ta kira WOOP [158]

#:which stands for wish, outcome, obstacle and plan. [159] <> wanda ke auna abinda muke fata, matsalalon da zamu iya fuskanta, hanyoyin da zamu iya kauce musu, da kuma yadda zamu tabbatar da burin namu. [160]

#:The tool, also available as a website [161] <> Ma'aunin da ake iya samu a shafin intanet [162]

#:and smartphone app, [163] <> ko kuma manhajar wayar komai-da-ruwanka, [164]

#:walks people through a series of exercises designed to help them come up with concrete strategies to achieve their short- or long-term goals, [165] <> wanda mutane za'a iya amfani da su wurin gano hanyoyin da zasu cimma manufofinsu [166]

#:mixing positive thinking with attention to any downsides and barriers. [167] <> ta hanyar gwama fata nagari tare da bada kulawa ta musamman ga abubuwan da za su iya kawo cikas. [168]

#:For example, you might want to start a company [169] <> Ga misali, ka na iya son kafa kamfani [170]

#:but then realise you hate to ask people for money or dont want to work long hours. [171] <> amma kuma ka san baka son tambayar mutane su ba ka kudi kumi ba ka san shafe sa'o'i masu yawa ka na aiki. [172]

#:You can then either figure out a way around those obstacles, [173] <> Don haka ko dai ka dauki matakan kaucewa wadannan matsaloli [174]

#:like teaming up [175] <> kamar hada kai [176]

#:with a sales person [177] <> da wanda ya kware wurin sayar da haja [178]

#:or sticking to predefined work hours. [179] <> ko kuma tabbatar da ka gudanar da aikin cikin wani kayyadadden lokaci. [180]

#:Or you might decide that the obstacle is too big and isnt worth it after allbefore youve performed poorly. [181] <> Ko kuma idan ka ga matsalar ta yi girma da yawa sai ka kwance niyyarka maimakon ka fara ka kuma kasa. [182]

#:Then at least you can put the goal aside without a bad conscience and you can sayno, no Ive looked it and at the moment it does not fit into my life’,” Oettingen says. [183] <> "Ka ga ke nan ka na iya sauya aniya ba tare da ka ji ba dadi ba," in ji Oettingen. [184]

#:When Stausholm started the sustainable pencil company Sprout a few years ago [185] <> Lokacin da Stausholm ya kafa kamfanin Sprout, mai samar da fensir din da ba zai yi illa ga muhalli ba [186]

#:he took lessons from his earlier business failures. [187] <> ya yi amfani da darasin da ya koya daga karyewar kamfaninsu na baya. [188]

#:He put all agreements down on paper [189] <> Duk yarjejeniyar da zai kulla ya na tabbatar an yi a rubuce, [190]

#:and made contingency plans for the worst-case scenario. [191] <> sannan kuma ya na fitar da tsare-tsaren matakan da zai dauka idan lamarin ya zo da matsala. [192]

#:Now the company sells more than 450,000 pencils a month in 60 countries, [193] <> A yanzu haka kamfanin na sayar da fensira fiye da 450,000 a kowanne wata a kasashe 60, [194]

#:results which have surprised even Stausholm. [195] <> abinda shi kansa Stausholm bai taba zaton haka ba. [196]

#:There is a lot of talk about being positive when being a business owner,” says Stausholm. [197] <> "Akwai maganganu da ake yi da yawa game da sa rai da samun nasara idan ka na da kamfaninka," in ji Stausholm. [198]

#:But the opposite of positive is not negative[199] <> "Kishiyar sa rai da samun nasara bashi ne sa rai da rashin nasara ba[200]

#:its having a sense of being realistic about what you can achieve and accomplish.” [201] <> sai dai fahimtar abinda za ka iya yi da wanda ba za ka iya ba." [202]

Contents