Tarjamar Suratul Mulk da Hausa
67:1 تَبَـٰرَكَ ٱلَّذِى بِيَدِهِ ٱلْمُلْكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ
- Blessed is He in whose hand is dominion, and He is over all things competent -— Saheeh International
- Albarkatun Allah da alheransa sun yawaita, mulki gabaɗaya a hannunSa yake, Shi mai iko ne a bisa dukkan komai. --Quran/67/1
67:2 ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلْمَوْتَ وَٱلْحَيَوٰةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْغَفُورُ
- [[[He]]] who created death and life to test you [[[as]] to] which of you is best in deed - and He is the Exalted in Might, the Forgiving -
- Shi ne wanda ya halicci mutuwa kuma ya halicci rayuwa, don ya gwada ku, wanene zai kyautata aiki a cikin ku. Shi Mabuwayi ne ƙaƙƙarfa, Mai gafara ga bayinSa waɗanda suka nemi tubanSa. --Quran/67/2
67:3 ٱلَّذِى خَلَقَ سَبْعَ سَمَـٰوَٰتٍ طِبَاقًا ۖ مَّا تَرَىٰ فِى خَلْقِ ٱلرَّحْمَـٰنِ مِن تَفَـٰوُتٍ ۖ فَٱرْجِعِ ٱلْبَصَرَ هَلْ تَرَىٰ مِن فُطُورٍ
- [And] who created seven heavens in layers.[i.e., one covering or fitting over the other.] You do not see in the creation of the Most Merciful any inconsistency. So return [your] vision [to the sky]; do you see any breaks?
- Shi ne ya halicci sammai guda bakwai (7), wata kan wata, ba tare da wata ta taɓa jikin wata ba. Ba za ka gani ba a cikin halittun da Allah ya yi dangane da wani saɓani ko karkacewa ko illa. Ka mayar da ganin ka sama ka gani, ka duba ga gani, shin za ka samu wani huda ko wani tsaga a jikin sama? --Quran/67/3
67:4 ثُمَّ ٱرْجِعِ ٱلْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ يَنقَلِبْ إِلَيْكَ ٱلْبَصَرُ خَاسِئًا وَهُوَ حَسِيرٌ
- Then return [your] vision twice again.[i.e., repeatedly.] [Your] vision will return to you humbled while it is fatigued.
- Sannan ka ƙara mayar da ganin ka sama a karo na biyu. Wallahi gani zai dawo gare ka a taɓe, kuma yana mai nadama (ma'ana duk yadda za ka kalli sama, ba za ka ga matsala a jikin ta ba. --Quran/67/4
67:5 وَلَقَدْ زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِمَصَـٰبِيحَ وَجَعَلْنَـٰهَا رُجُومًا لِّلشَّيَـٰطِينِ ۖ وَأَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابَ ٱلسَّعِيرِ
- And We have certainly beautified the nearest heaven with lamps [i.e., stars] and have made [from] them what is thrown at the devils and have prepared for them the punishment of the Blaze.
- Haƙiƙa mun ƙawata saman duniya da fitilu na taurari. Kuma mun halicci taurari mun sanya su abin jifan sheɗanu masu hawa sama don sato zance. Haƙiƙa mun tanadawa shaiɗanu da kafirai azabar wata wuta mai tsananin ƙuna. --Quran/67/5
67:6 وَلِلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِرَبِّهِمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ
- And for those who disbelieved in their Lord is the punishment of Hell, and wretched is the destination.
- Waɗanda suka kafirce wa Ubangijinsu, azabar wutar Jahannama ta tabbata akan su. Tir da makoma idan ta zama wutar jahannama ce. --Quran/67/6
67:7 إِذَآ أُلْقُوا۟ فِيهَا سَمِعُوا۟ لَهَا شَهِيقًا وَهِىَ تَفُورُ
- When they are thrown into it, they hear from it a [dreadful] inhaling while it boils up.
- Idan an jefa wa'yannan kafirai da shaiɗanu cikin wutar jahannama, sai su ji wani sauti mai ƙarar gaske, mai tsoratarwa a cikin wannan wuta, tana zaɓalɓala, tana haɓaka. --Quran/67/7
67:8 تَكَادُ تَمَيَّزُ مِنَ ٱلْغَيْظِ ۖ كُلَّمَآ أُلْقِىَ فِيهَا فَوْجٌ سَأَلَهُمْ خَزَنَتُهَآ أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَذِيرٌ
- It almost bursts with rage. Every time a company is thrown into it, its keepers ask them, "Did there not come to you a warner?"
- Wutar ta kusata ta fito daga inda take saboda tsananin fushin Allah da ya cika ta. Duk sanda aka zuba wani ayari na jama'a a cikin wannan wuta, masu gadin wannan wutar za su dinga tambayar wa'anda aka jefa a cikin ta... suna ce musu: Shin ko annabi mai gargaɗi bai zo muku bane? --Quran/67/8
67:9 قَالُوا۟ بَلَىٰ قَدْ جَآءَنَا نَذِيرٌ فَكَذَّبْنَا وَقُلْنَا مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ مِن شَىْءٍ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا فِى ضَلَـٰلٍ كَبِيرٍ
- They will say, "Yes, a warner had come to us, but we denied and said, 'Allah has not sent down anything. You are not but in great error.'"
- Sai su ce: Tabbas! Haƙiƙa mai gargaɗi a bi Allah ya zo mana. Muka ƙaryata shi, muka kuma ƙaryata dukkan wani manzo. Kuma ma muka ce musu "Ubangiji fa bai saukar da wani abu na littafi ba." Ku fa ba ku kasance a wani yanayi na gaskiya ba face sai a cikin ɓata mai girma. --Quran/67/9
67:10 وَقَالُوا۟ لَوْ كُنَّا نَسْمَعُ أَوْ نَعْقِلُ مَا كُنَّا فِىٓ أَصْحَـٰبِ ٱلسَّعِيرِ
- And they will say, "If only we had been listening or reasoning, we would not be among the companions of the Blaze."
- Kuma 'yan wuta za su ce: Ina ma a ce mun ji manzannin mu, mun ji abinda suke gaya mana. Ina ma mun hankalci abinda manzanni suke gaya mana. Da mun ji abinda suke gaya mana, wallahi da ba za mu zamo daga cikin 'yan wuta ba. --Quran/67/10
67:11 فَٱعْتَرَفُوا۟ بِذَنۢبِهِمْ فَسُحْقًا لِّأَصْحَـٰبِ ٱلسَّعِيرِ
- And they will admit their sin, so [it is] alienation[From all good and from Allah's mercy.] for the companions of the Blaze.
- Suma sai su amsa laifin su, su tabbatar da sun saɓi Allah a wannan lokaci. Tir da ma'abuta wuta, nesa-nesa da su. --Quran/67/11
67:12 إِنَّ ٱلَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُم بِٱلْغَيْبِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ كَبِيرٌ
- Indeed, those who fear their Lord unseen will have forgiveness and great reward.
- Lalle waɗanda suke jin tsoron Ubangijinsu a fake a duniya ba tare da sun gan Shi ba, gafara da yafiyar zunubi ta tabbata a gare su da kuma wani lada gwaggwaɓa mai girma - shi ne Aljanna. --Quran/67/12
67:13 وَأَسِرُّوا۟ قَوْلَكُمْ أَوِ ٱجْهَرُوا۟ بِهِۦٓ ۖ إِنَّهُۥ عَلِيمٌۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
- And conceal your speech or publicize it; indeed, He is Knowing of that within the breasts.
- Ku ɓoye maganganun ku, ko ku bayyanar da su, lalle Ubangiji maɗaukakin sarki mai cikakken tsarki mai cikakken sani ne dangane da abinda ke cikin zuƙata.--Quran/67/13
67:14 أَلَا يَعْلَمُ مَنْ خَلَقَ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلْخَبِيرُ
- Does He who created not know, while He is the Subtle, the Aware?
- Ku saurara! Shi ya san haƙiƙanin abinda ya halitta, ya san halin su da ɗabi'ar su. Shi mai tausasawa bayinSa ne kuma mai basu labari dangane da abinda suke aikatawa. --Quran/67/14
67:15 هُوَ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ ذَلُولًا فَٱمْشُوا۟ فِى مَنَاكِبِهَا وَكُلُوا۟ مِن رِّزْقِهِۦ ۖ وَإِلَيْهِ ٱلنُّشُورُ
- It is He who made the earth tame for you - so walk among its slopes and eat of His provision - and to Him is the resurrection.
- Ubangiji Shi ne wanda ya halittar muku ƙasa mai sauƙi, don haka ku tafi a sasanninta da lungunanta da saqunanta. Ku ciyo daga arziƙinSa. Tattara bayi ya tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki. --Quran/67/15
67:16 ءَأَمِنتُم مَّن فِى ٱلسَّمَآءِ أَن يَخْسِفَ بِكُمُ ٱلْأَرْضَ فَإِذَا هِىَ تَمُورُ
- Do you feel secure that He who is above[Literally, "in ascendancy" or "over the heaven."] would not cause the earth to swallow you and suddenly it would sway? [In a circular motion, as in an earthquake.]
- Shin yanzu kun amince ga wanda yake sama (shi ne Allah), Ya girgiza ƙasa a ƙarƙashin ƙafafuwan ku, ta zo tana rorawa da ku? --Quran/67/16
67:17 أَمْ أَمِنتُم مَّن فِى ٱلسَّمَآءِ أَن يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا ۖ فَسَتَعْلَمُونَ كَيْفَ نَذِيرِ
- Or do you feel secure that He who is above would not send against you a storm of stones? Then you would know how [severe] was My warning.
- Shin yanzu kun amince ga wanda yake sama (Allah maɗaukakin sarki), Ya aiko muku da wata iska mai tsananin ƙarfi ta hallakar da ku? Toh fa da sannu za ku sani yanda azabarSa take da uƙubarSa ga waɗanda suka saɓa masa. --Quran/67/17
67:18 وَلَقَدْ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
- And already had those before them denied, and how [terrible] was My reproach.
- Tabbas! Haƙiƙa waɗanda suka zo tun kafinsu cikin al'ummatai sun ƙaryata da manzanninsu. Yaya uƙubata ta kasance ga wadanda suka ƙaryata da manzannin mu? --Quran/67/18
67:19 أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلطَّيْرِ فَوْقَهُمْ صَـٰٓفَّـٰتٍ وَيَقْبِضْنَ ۚ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا ٱلرَّحْمَـٰنُ ۚ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَىْءٍۭ بَصِيرٌ
- Do they not see the birds above them with wings outspread and [sometimes] folded in? None holds them [aloft] except the Most Merciful. Indeed He is, of all things, Seeing.
- Shin ba su yi duba ba zuwa ga tsuntsaye ba? Da suke saman kansu ba? Suna masu ninƙaya suna masu buɗe fuka-fukansu a sama? Kuma sai su tsuke fiffikensu a sanda suka so. Ba wanda yake riƙe su a sama su ƙi faɗowa, face sai Ubangiji wanda ya siffa daga rahama. --Quran/67/19
67:20 أَمَّنْ هَـٰذَا ٱلَّذِى هُوَ جُندٌ لَّكُمْ يَنصُرُكُم مِّن دُونِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ۚ إِنِ ٱلْكَـٰفِرُونَ إِلَّا فِى غُرُورٍ
- Or who is it that could be an army for you to aid you other than the Most Merciful? The disbelievers are not but in delusion.
- Shin wanene zai zamo mataimaki gare ku mai kare ku? Wanda ya siffanta da rahama. Tabbas! Kafirai ba a cikin wani abu suke ba na gaskiya wanda ya siffanta da rahama. Face sai a cikin ruɗi na shaiɗan. --Quran/67/20
67:21 أَمَّنْ هَـٰذَا ٱلَّذِى يَرْزُقُكُمْ إِنْ أَمْسَكَ رِزْقَهُۥ ۚ بَل لَّجُّوا۟ فِى عُتُوٍّ وَنُفُورٍ
- Or who is it that could provide for you if He withheld His provision? But they have persisted in insolence and aversion.
- Wanene ya isa ya azurta ku idan Allah ya riƙe arziƙi ga barin ku? Bari dai, suna yin kutse ne suna zarmewa a cikin girman kai da kuma nisantar addinin mu. --Quran/67/21
67:22 أَفَمَن يَمْشِى مُكِبًّا عَلَىٰ وَجْهِهِۦٓ أَهْدَىٰٓ أَمَّن يَمْشِى سَوِيًّا عَلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ
- Then is one who walks fallen on his face better guided or one who walks erect on a straight path?
- Shin yanzu wanda yake tafiya a kife ga fuskarsa... shin wannan shi zai fi shiriya? Ko kuma wanda yake tafiya a miƙe kuma yake tafiya akan gwadabe (hanya?) miƙaƙƙe... tsakanin kafiri da musulmi kenan. --Quran/67/22
67:23 قُلْ هُوَ ٱلَّذِىٓ أَنشَأَكُمْ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمْعَ وَٱلْأَبْصَـٰرَ وَٱلْأَفْـِٔدَةَ ۖ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ
- Say, "It is He who has produced you and made for you hearing and vision and hearts [i.e., intellect]; little are you grateful."
- Ka ce: Ubangiji shi ne wanda ya halicce ku, kuma ya halittar muku ji, kuma ya halittar muku gani, kuma ya halittar muku zukata, kaɗan ne kuke godewa Allah cikin ni'imomin da ya yi muku. --Quran/67/23
67:24 قُلْ هُوَ ٱلَّذِى ذَرَأَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَإِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
- Say, "It is He who has multiplied you throughout the earth, and to Him you will be gathered."
- Ka ce: Ubangiji shi ne wanda ya halicce ku, kuma ya sanya ku a banƙasa, kuma gare Shi za a tattara ku bakiɗaya! --Quran/67/24
67:25 وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَـٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ
- And they say, "When is this promise, if you should be truthful?"
- Kafirai suna cewa "Yaushe wannan alƙawarin zai zo ne na tashin alƙiyama? Ku bamu labari na gaskiya in kun kasance masu gaskiya ne cikin da'awarku na cewa Alƙiyama zata tsaya. --Quran/67/25
67:26 قُلْ إِنَّمَا ٱلْعِلْمُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
- Say, "The knowledge is only with Allah, and I am only a clear warner."
- Ka ce musu: kaɗai sanin tashin alƙiyama da lokacinta, iliminta yana wajen Allah. Ni kawai mai gargaɗi ne ga waɗanda suke saɓon Allah, mai kuma bayyanar da wa'azi. --Quran/67/26
67:27 فَلَمَّا رَأَوْهُ زُلْفَةً سِيٓـَٔتْ وُجُوهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَقِيلَ هَـٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تَدَّعُونَ
- But when they see it[1] approaching, the faces of those who disbelieve will be distressed, and it will be said, "This is that for which you used to call."[The punishment of which they were warned.]
- Yayin da suka ga alƙiyama da azabar Allah ta zo musu kusa da su, fuskokin kafirai za su munana, za su yi baƙiƙƙirin! Kuma za a ce musu, wannan shi ne abin da kuke iƙirarin ƙaryatawa... yau ga shi ya zo muku (tashin alƙiyama kenan). --Quran/67/27
67:28 قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِنْ أَهْلَكَنِىَ ٱللَّهُ وَمَن مَّعِىَ أَوْ رَحِمَنَا فَمَن يُجِيرُ ٱلْكَـٰفِرِينَ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ
- Say, [O Muḥammad], "Have you considered:[i.e., inform me.] whether Allah should cause my death and those with me or have mercy upon us, who can protect the disbelievers from a painful
- Ka ce ku bani labari, da Allah zai hallakar da ni, da zai hallakar da waɗanda suke tare da ni, wa ya isa ya hana? Ya yi falala gare mu... wa ya isa ya hana? To wanene kuma ya isa ya tsiratar da kafirai daga wata azaba mai raɗaɗi da Allah zai musu? --Quran/67/28
67:29 قُلْ هُوَ ٱلرَّحْمَـٰنُ ءَامَنَّا بِهِۦ وَعَلَيْهِ تَوَكَّلْنَا ۖ فَسَتَعْلَمُونَ مَنْ هُوَ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ
- Say, "He is the Most Merciful; we have believed in Him, and upon Him we have relied. And you will [come to] know who it is that is in clear error."
- Ka ce: abin bauta na gaskiya shi ne wanda ya siffanta da rahama. Mun yi imani da shi. Gare shi kaɗai muka dagora. Da sannu za ku san wanene yake cikin ɓata mabayyani. --Quran/67/29
67:30 قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِنْ أَصْبَحَ مَآؤُكُمْ غَوْرًا فَمَن يَأْتِيكُم بِمَآءٍ مَّعِينٍۭ
- Say, "Have you considered: if your water was to become sunken [into the earth], then who could bring you flowing water?"
- Ka ce ku bani labari, idan ruwanku ya wayi gari ya zamo a ƙafe, toh wanene ya isa ya zo muku da ruwa mai gudana?--Quran/67/30