Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/020 cheating

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations


#: We all know cheating is bad, So why do we do it [1] <> Me ya sa muke almundahana? [2]

#: Cheating at work and sport is unethical, but we sometimes do it anyway. Here's why. [3] <> Cuta a wurin aiki da fagen wasanni ba kyau, amma wasu lokutan mu kan yi. Ga dalili. [4]

#: Before this years Olympics had even begun, [5] <> Tun kafin a fara gasar wasannin Olympics ta bana, [6]

#: a major scandal sparked headlines around the world[7] <> wata badakala ta mamaye kafafen labaran duniya ita ce[8]

#: all but one of Russias track and field athletes were banned from this years Olympics [9] <> an haramtawayan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Rasha baki daya in ban da mutum guda daya tak shiga gasar, [10]

#: following claims of a state-sanctioned doping programme. [11] <> saboda zargin gwamnatin kasar ta ba su kwayoyin kara kuzari. [12]

#: As the Games have progressed, [13] <> Bayan da aka fara gasar, [14]

#: we've heard athletes accusing others of cheating, [15] <> mun jiyan wasa na zargin abokin karawarsa da amfani da haramtattun kwayoyi, [16]

#: such as US swimmer Lilly King calling out Russias Yulia Efimova, [17] <> kamaryar tseren nunkayar Amurka Lilly King da ta zargi takwararta ta Rasha, Yulia Efimova, [18]

#: or Australian swimmer Mack Horton accusing Chinese competitor Sun Yang of using banned drugs. [19] <> ko dan tseren ninkayar Australia Mack Horton wanda ya nuna yatsa ga abokin takararsa dan China, Sun Yang. [20]

#: But getting ahead using unethical means isnt distinct to sport. [21] <> Sai dai kuma samun nasara ta hanyar bin hanyoyin da basu dace ba, ba a fagen wasa kawai ta tsaya ba. [22]

#: There are many instances in our work, personal and social lives where the temptation to give ourselves a secret boost may be all too enticing. [23] <> Akwai lokuta da dama a wurin aikinmu da kuma rayuwarmu ta yau da kullum da mu kan ji bukatar taimakawa kanmu ta barauniyar hanya. [24]

#: But it is not only driven by greed, say experts. [25] <> Sai dai masana sun ce ba kwadayi ne kawai ke samu yin hakan ba. [26]

#: So why exactly do some people cheat? [27] <> To wane dalili ne ke sa wasu mutan su yi cuta? [28]

#: Is it just that they are morally corrupt or greedy? [29] <> Tsabar kwadayi ne da rashin tarbiyya? [30]

#: And does our often competitive society encourage it? [31] <> Shin kasayyar da muke a zamantakewar zamani ta na taimakawa a yi cuta? [32]

#: The science of cheating [33] <> Almundahana a kimiyyance [34]

#: Psychologists have [35] <> Masu nazarin halayyar mutane [36]

#: found that winning can make people more dishonest, [37] <> sun gano cewa samun nasara kan kara wa mutane kaimin cuwa-cuwa, [38]

#: while working as part of team can lead to more deceit. [39] <> yayin aiki a matsayin wani bangare na rukunin jamaa na kara sa a yi almundahana. [40]

#: Amos Schurr, a behavioural psychologist at Ben Gurion University in Israel, [41] <> Amos Schurr, mai nazarin dabiar mutane a jamiar Ben Gurion da ke Israila, [42]

#: has been looking into how group behaviour can make cheating seem okay [43] <> na gudanar da bincike kan yadda cudanya da mutane kan sa mu dauki cuta a matsayin wani abu mara muhimmanci [44]

#: and how winning a competition can make people more likely to be dishonest. [45] <> da kuma yadda nasara a gasa ke kara wa mutane kaimin yin cuta. [46]

#: The team behind the research conducted a series of experiments, [47] <> Binciken ya kunshi gwaje-gwaje da dama [48]

#: using trivia, memory [49] <> ta hanyar wasannin tambayoyinyar kure [50]

#: and dice games, [51] <> da kuma na kada dan dayis, [52]

#: where they watched how 23 volunteers reported their own winnings. [53] <> inda manazartan su ka binciki yaddayan wasan su 23 ke bayyana nasarar da su ka samu. [54]

#: The volunteers could win money [55] <> ‘Yan wasan dai na da damar samun kyautar kudi [56]

#: depending on, for example, what number dice they rolled. [57] <> bisa laakari da lambar da ta fito a dayis din da su ka kada. [58]

#: Schurrs team found that when they had won at a previous memory or trivia game, people were more dishonest, [59] <> Schurr da tawagarsa sun gano cewa wadanda su ka yi nasara a wasannin farko sun fi shirga karya, [60]

#: keeping more money than they were entitled to. [61] <> domin samun kudi fiye da hakkinsu. [62]

#: Schurrs team is researching how unethical behaviour may develop after exposure to competitive settings, [63] <> Tawagar Schurr dai na binciken yadda kasayya ke iya jawo almundahana, [64]

#: and how social or group ethics can make people cheat. [65] <> da kuma yadda cudanya da mutane ke sa wadansu su yi cuta. [66]

#: We are social creatures[67] <> “Dabioinmu sun danganta da irin abokan huldarmu[68]

#: when working in groups, [69] <> duk lokacin da mu ke aiki cikin jamaa, [70]

#: we follow the norms that the group establishes,” says Schurr. [71] <> mu kan bayyana dabiar da ta ke karbabbiya a wurin wannan gungun mutanen ne,” in ji Schurr. [72]

#: Collaborating in corruption [73] <> Hada-baki kan cuta [74]

#: People cheat when they are encouraged by their peers, [75] <> Mutane kan yi almundahana, idan abokan huldarsu su ka zuga su, [76]

#: according to analysis from the University of Nottingham in the UK, [77] <> kamar yadda wani bincike daga jamiar Nottingham da ke UK, [78]

#: which found cooperation can create ample opportunity for corruption. [79] <> ya bayyana, bayan gano cewa hadin baki na iya bada muhimmiyar damar cuwa-cuwa. [80]

#: Participants in the study were asked to work together on a dice-rolling game to win money. [81] <> Masu binciken, sun bukaci wasu mutane bibiyu su hada kai a gasar kada dayis da nufin cin kudi. [82]

#: The first participant rolled a die, [83] <> Dan wasa na farko zai kada dayis din [84]

#: and then reported the number to his or her partner. [85] <> sai ya gayawa na biyu lambar da ke jiki. [86]

#: If the partner rolled the same number, they both got a pay out. [87] <> Idan na biyun shi ma ya kada kuma ya samu irin lambar sak, sai a basu kudi su biyun. [88]

#: Perhaps unsurprisingly, the teams often put their heads together [89] <> A mafi yawan lokuta duk mutane biyun da aka hada a gasar, [90]

#: to lie to collect these winnings[91] <> kan hada baki su yi karya don su samu kudin[92]

#: the instances of winning double rolls were almost 500% higher than what would be expected if it were assumed the participants were being honest. [93] <> adadin lokutan da su ka ce sun kada lambobi iri daya a jere ya ninka adadin da hasashe ke nuna zai iya yi wa har sau biyar. [94]

#: The research found that the highest levels of corruption in a team occurred when the profits were shared equally [95] <> Masu binciken sun gano cewa cuwa-cuwa ta biyu cikin rukunin mutanen da ke raba-daidan abinda su ka samu, [96]

#: and when there were strong bonds in a group. [97] <> da kuma rukunin da su ke da fahimtar juna. [98]

#: The studys authors, [99] <> Wadanda su ka rubuta sakamakon binciken, [100]

#: Ori Weiseland Shaul Shalvi, concluded that [101] <> Ori Weisel da Shaul Shalvi sun kammala bayaninsu da cewa [102]

#: the corruption and immoral conduct at the roots of recent financial scandals [103] <> almundaha da rashin gaskiyar da suka haddasa badakala a kasuwannin hadahadar kudi na duniya [104]

#: are possibly driven not only by greed, but also by cooperative tendencies and aligned incentives.” [105] <> “ba lallai kwadayi ne kadai ya haddasa su ba, aa har da hadin baki da kuma yiwuwar raba-daidai a cuwa-cuwar da aka samo.” [106]

#: How cheating is changing [107] <> Yadda dabarun cuta ke sauyawa. [108]

#: The ways people cheat are changing, [109] <> Hanyoyin da mutane ke bi wurin kitsa cuta na sauyawa, [110]

#: and this is a significant problem in the world of finance, [111] <> kuma wannan muhimmiyar barzana ce ga harkokin kudi, [112]

#: high levels of company management and politics, [113] <> gudanar da kamfanunnuka da kuma shaanin siyasa, [114]

#: according to fraud analysts. [115] <> a cewar masu fashin baki game da damfara. [116]

#: Thanks to technology, there are ever-evolving ways for workers and students to cheat. [117] <> Fasahar kere-keren zamani ta bullo da hanyoyi da dama da maaikata da ma dalibai za su iya cuta. [118]

#: Phillip Dawson, associate director of the Centre for Research in Assessment [119] <> Phillip Dawson, mukaddashan daraktan cibiyar bincike kan jarrabawa [120]

#: and Digital Learning at Deakin University in Victoria, Australia, says: [121] <> da koyon karatu ta hanyar naurorin zamani a jamiar Deakin da ke Victoria, Australia ya ce: [122]

#: Some new frontiers for cheating [123] <> “Wadansu sababbin hanyoyin magudin jarrabawa [124]

#: include exam hacking [125] <> sun hada da sato bayanan tambayoyin jarrabawa da aka adana a kwamfuta [126]

#: and online tools that manipulate text such as getting away with copy-pasting text [127] <> da kuma bad-da-sawun kwaso bayanai kai tsaye ta intanet, [128]

#: by running it through Google Translate from English to Spanish to English.” [129] <> ta hanyar amfani da shafin fassarar Google, inda ake fassara bayanin da aka kwafa da Ingilishi zuwa Spananci sannan sai a sake fassara sakamakon zuwa Ingilishi.” [130]

#: The scam is also cropping up in workplaces such as consulting firms that produce international reports, or in media organisations and universities. [131] <> Haka kuma ana samun irin wannan fasahar a kamfanonin bada shawarwari, da kafafen yada labarai da kuma jamioi. [132]

#: But Dawson says there are also more ways to get caught, through sites like Turnitin, [133] <> Sai dai kuma Dawson ya ce akwai karin sababbin hanyoyin kama masu satar bayanan wasu kamar shafin Turnitin, [134]

#: which check for plagiarism. [135] <> wanda ke binciko duk wurin da aka dauko wani bayani kai tsaye daga intanet. [136]

#: Dawson adds: “Im not convinced that cheating is more [137] <> Dawson ya ce: “Ba na jin almundahana ta dadu [138]

#: or less prevalent than in years past. [139] <> ko ta ragu a cikinyan shekarun nan. [140]

#: Its just different.” [141] <> Kawai dai salonta ya sauya.” [142]

#: Dawson believes that time pressure and a higher cost of living [143] <> A ganin Dawson, tsadar rayuwa [144]

#: have made many people rely on extra sources of income other than their basic salary to live, [145] <> ta tilasta wa mutane neman karin hanyoyin samun kudi saboda albashinsu ba zai wadace su ba. [146]

#: which can make more people consider unethical or illegal ways to make money. [147] <> Hakan na iya sa wasu mutanen su fara neman hanyoyin samun kudi na cuwa-cuwa. [148]

#: As well, pressures on students to pass exams can make cheating an attractive option for those starved for time. [149] <> Haka kuma, matsantawar da ake wa dalibai sai sun ci jarrabawa na sa satar amsa ta zama zabin wadanda ke da karancin lokacin karatu. [150]

#: How to improve [151] <> Yadda za a gyara [152]

#: There is good news for those of us who feel guilty and may want to improve our behavior to be more honest in the workplace. [153] <> Albishir ga wadanda su ke jin ba dadi idan sun yi cuta kuma su ke fatan sauya dabioinsu ta yadda za su zamo masu gaskiya a wuraren ayyukansu. [154]

#: A good sense of perspective can diminish any temptation to cheat, [155] <> Daina muamala da macuta zai iya rage mana shaawar yin cutar, [156]

#: according to research from Harvard Business School that examined whether exposure to other peoples behaviour can increase your own dishonesty. [157] <> kamar yadda sakamakon wani bincike da aka gudanar a makarantar nazarin kasuwanci ta jamiar Harvard ya bayyana. [158]

#: It found that when a member of a group behaves dishonestly, it made the group as a whole more likely to behave the same way. [159] <> Binciken ya gano cewa zama da macuta na sa wa mutum amincewa da cutar. [160]

#: In the study, [161] <> Yadda aka gudanar da binciken kuwa, [162]

#: a group of friends observed a member of their own group cheating at a test, [163] <> wasu abokai a ka yi wa jarrabawa, amma ba da saninsu ba an sa daya daga cikinsu ya saci amsa a gabansu, [164]

#: which in turn made them more likely to cheat. [165] <> ko da su ka ga abokinsu na satar amsa sai su ma su ka fara kokarin yi. [166]

#: But when a group observed a stranger cheating, [167] <> Amma da wani bako ya fara satar amsa, [168]

#: the groups ethics and behaviour changed in a different waythat is, seeing a stranger cheat actually made the group of friends more likely to honestly complete the test. [169] <> sai su kuma abokan su ka hade kai su ka rubuta jarrabawarsu cikin kaida. [170]

#: The threshold of unacceptable behaviour is not fixed. Rather, it depends on the perspective through which people view their actions,” concludes Schurr. [171] <> “Mutane kan karbi dabia ne ko kuma su guje ta bisa mahangar abokanan huldarsu,” in ji Schurr. [172]

#: So, perhaps if we want to become more honest, [173] <> Don haka, in muna son mu zamo masu gaskiya, [174]

#: it may be a good idea to keep our dishonest rivals close, to maintain perspective on our own behaviour. [175] <> sai mu nesanta kanmu da abokai marasa gaskiya, mu kuma kusanta kanmu da abokan kasayya marasa gaskiya. [176]

Contents