Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/014 job interviews

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 23:21, 21 June 2017 by Admin (talk | contribs) (/* #: Are nervous habits derailing your job interview? [http://www.bbc.com/capital/story/20160921-are-nervous-ticks-derailing-your-job-interview] Ko ka san cewa dabi'ar ka ta fargaba na iya shafar jarrabawar neman aikin da ka ke yi ? [http://www.bbc....)
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

#: Are nervous habits derailing your job interview? [1] <> Ko ka san cewa dabi'ar ka ta fargaba na iya shafar jarrabawar neman aikin da ka ke yi ? [2]

#: When it comes to job interviews, [3] <> Idan ana magana akan batun jarrabawar neman aiki, [4]

#: you'd be right to presume your stellar CV, [5] <> za'a iya cewa mutum na da gaskiya idan ya dauka cewa irin yadda ya tsara takardar bayanan ilimi da ayyukan da ya yi ko yake yi [6]

#: personal presentation and, more importantly, how well you answer questions [7] <> da kuma yadda ya gabatar da kansa, kuma musamman yadda ya amsa tambayoyin da aka yi masa, [8]

#: could land you the position. [9] <> zai iya sa ya samu aikin da ya ke nema. [10]

#: But your mannerisms and gestures could be holding you back. [11] <> Sai dai kuma dabi'ar mutum ka iya janyo masa cikas. [12]

#: In fact, they can reveal much about you, even if you dont want them toboth positive and negative. [13] <> Domin dabi'un mutum za su iya bayyana ko shi wani irin mutum ne koda kuwa baya son wadannan dabi'un- wato kodai masu kyau ne ko kuma marasa kyau. [14]

#: And, most of the time we dont even realise were doing them. [15] <> Kuma a mafi yawan lokuta ba mu cika sanin muna irin wadannan dabi'un ba. [16]

#: Conscious or unconscious, repeated behaviour like batting your eyes, twisting your ring or touching your hair, may influence the recruiter on the other side of the table more than you think. [17] <> Mai yiyuwa mutum yana sane ko kuma ba tare da saninsa ba, yawan goge idanuwa, ko matse 'yan yatsun hannu ko kuma taba gashin kai zai iya sauya tunanin mai gudanar da jarrabawar daukar aiki fiye da yadda kake tunani. [18]

#: As Isabel Schuermann, an image consultant and etiquette trainer based near Frankfurt, says, [19] <> Kamar yadda Isabel Schuermann, wani mai horas da ma'aikata kan kyawawan dabi'un aiki dake kusa da Frankfurt ke cewa. [20]

#: Your body cannot not communicate.” [21] <> "Tilas jikinka ya riƙa aikewa da saƙo". [22]

#: "A lack of eye contact, for instance, [23] <> Misali rashin hada ido [24]

#: may send a signal that youre hard to trust [25] <> zai iya aikewa da saƙon cewa mutum ba shi da gaskiya, [26]

#: A lack of eye contact, for instance, may send a signal that youre hard to trust, or a foot turned inward might suggest youre insecure. [27] <> ko kuma ajiye ƙafafuwa a karkace zai iya sa a riƙa kallon mutum a matsayin wanda ke cikin zullumi. [28]

#: N/A [29] <> Masu yin jarrabarar daukar aiki suna tantance gaskiya da kuma ilimi ta hanyar kallon ƙwayar idon mutum [30]

#: The good news is that [31] <> Sai dai wani labari mai dadin ji anan shi ne, [32]

#: you can rid yourself of unwanted mannerisms and behaviours. [33] <> mutum zai iya magance wasu dabi'unsa marasa kyau, kuma matakin farko shine sanin irin wadannan dabi'un. [34]

#: But, be warned, its harder to tame those quirks when you're nervous. [35] <> Amma wani gargadi shi ne yana da wahala a magance irin wadannan dabi'u idan mutum yana cikin zullumi. [36]

#: Heres what you can do: [37] <> Amma ga wasu abubuwan da ya kamaya mutum ya yi. [38]

#: Facing your quirks [39] <> Ka fuskanci matsalar ka [40]

#: Once youve acknowledged your mannerisms, [41] <> Matuƙar ka amince da irin dabi'un ka, [42]

#: its time to curb them. [43] <> to lokaci ya yi da zaka magance su. [44]

#: Perform role play and practice speaking to an interviewer until the nervous gestures are under control. [45] <> Ka riƙa sa kanka a matsayin wanda ke yiwa wani jarrabawa har sai ka shawo kan wadannan dabi'u. [46]

#: For instance, [47] <> Misali, [48]

#: you may reduce the amount of time you spending cracking your knuckles, [49] <> kana iya rage yawan matse 'yan yatsun ka [50]

#: picking your cuticles, or staring down your conversation partner. Others suggest acknowledging your quirk when it arises. [51] <> ko kuma kallon ƙasa a duk lokacin da kake magana da wani. [52]

#: Daniela Lehmann-Stein, who leads a human resources team at Nielsen in Frankfurt, [53] <> Daniela Lehmann-Stein, wacce ta jagoranci wata tawaga ta masu kula da ma'aikata a Nielsen dake Frankfurt, [54]

#: says that while she's had interview training, [55] <> ta ce ya yin da take samun horo kan dubarun yadda za'a riƙa yiwa masu neman aiki jarrabawa, [56]

#: she resists checklist-style thinking in which she mentally ticks off a box that saysno annoying quirks or mannerisms.” [57] <> ta rubuta a takarda jerin abubuwan da ta saba yi ba tare da saninta ba, wanda kuma take son ta daina, misali ta rubuta cewa bata son yin wani abu da zai dauke mata hankali. [58]

#: Instead, [59] <> A maimakon hakan, [60]

#: Lehmann-Stein, who has hired dozens of people during 17 years in HR roles in multinational companies, [61] <> Lehmann-Stein, wacce ita ce ke daukar hayan mutane aiki a shekaru 17 da take aiki a ɓangaren kula da ma'aikata a wani katafaren kamfani [62]

#: wants to get to know a candidate and see how the person handles the situation if something becomes distracting. [63] <> na son ta san wanda ke neman aiki idan ta ga yadda mutum ya yi wani abu ko kuma wani abu ya dauke mishi hankali. [64]

#: "Authenticity is very important [65] <> Tantancewa tana da matukar muhimmanci. [66]

#: Authenticity is very important. [67] <> "Tantancewa ta na da matukar muhimmanci, [68]

#: If someone describes him or herself as very open [69] <> saboda idan mutum ya bayyana kansa a matsayin wanda ba shi da zurfin ciki, [70]

#: and then at the same time he or she is sitting in a very closed position, with shoulders and arms very tight to the body, [71] <> kuma a bangare guda, aka ga ya ware kansa ya zaune gefe guda shi kadai, [72]

#: then this would come across as a contradiction. [73] <> wannan zai janyo ta-ba-ba game da iƙirarin sa- a cewar ta". [74]

#: But its not like Im screening the candidate all the time trying to detect mismatches,” she says. [75] <> N/A [76]

#: At the same time, Lehmann-Stein says shes often impressed when people openly address a physical reaction they may be having in a certain situation. [77] <> Wata hanya kuma ta magance wata dabi'ar ita ce maida yanayin tamkar abun dariya. [78]

#: Sometimes its helpful to be aggressive about it. If I know that I get red spots on my face or neck when Im nervous, … [79] <> Lehmann-Stein ta ce zan so a ce kowane mutum mai jarrabawar neman aiki zai riƙa nuna gaskiyar dabi'ar sa tare da ƙarin kwarjini ta wannan fuska. [80]

#: Why we do it? [81] <> Me ya ke sa mu ke yi ne? [82]

#: Nervous gestures often have a psychological origin, Burch says. [83] <> Yanayi na rashin natsuwa yana da asali a halayyar dan adam, in ji Burch [84]

#: In other words, if you can identify the cause, [85] <> Idan zaka gano dalilan [86]

#: you can minimise the unwanted mannerism. [87] <> zaka iya magance dabi'un da ka ke yi da ba su da ce ba. [88]

#: For instance, sometimes the cause is insecurity from not feeling prepared, Burch says. [89] <> Alal misali, Burch ya ce a wasu lokuta dalilan su ne fargaba saboda rashin shiryawa. [90]

#: She has seen how some clients have overcome this by being well prepared for the interview[91] <> Ta ƙara da cewa ta ga yadda wasu mutane suka shawo kan wannan dabi'a ta hanyar kintsawa sosai a lokacin yin jarrabawar daukar aiki. [92]

#: The whole package [93] <> Daukacin abunda ya ƙunsa [94]

#: If youre lucky, you might get an interviewer like Schuermann, [95] <> Idan ka yi sa'a zaka iya samun mai yin jarrabawar daukar aiki kamar Schuermann, [96]

#: who looks at the candidate as a whole. [97] <> wanda sai ya kalli mai neman aiki daga sama har ƙasa. [98]

#: You should never ever interpret just one gesture. You need four to five clues to come up with an interpretation,” Schuermann says. [99] <> "Kada ka taba fassara kallo daya kawai, kana bukatar hanyoyi hudu zuwa biyar kafin ka iya fassara ko wane irin mutum ne, " in ji Schuermann. [100]

#: In the end, most decisions to hire are based on a wide range of factors. [101] <> A ƙarshe dai shawarar a dauki mutum aiki sun danganta ne akan wasu dalilai da dama. [102]

#: Recalling her days in HR, leadership, and development at Deutsche Bank in Frankfurt, Schuermann says, [103] <> Schuermann ta ce idan ta tuna zamanin da take aiki a sashen kula da daukar ma'aikata a bankin Deutsche da ke Frankfurt, [104]

#: The candidate who got the job was not only brilliant in the technicals [105] <> "wadanda ke dacen samun aiki ba wai kawai suna da ilimi ba kadai ta fuskar bangaren da suka ƙware, [106]

#: but was good in personality, [107] <> har ma suna da tarbiya, [108]

#: knew how to engage in small talk [109] <> kuma sun iya magana tare [110]

#: and understood how to manage people and communicate with charisma.” [111] <> da fahimtar yadda za su yi mu'amala da jama'a cikin yanayi na kwarjini." [112]

Contents