Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/064 talking to yourself

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 19:38, 23 June 2017 by Admin (talk | contribs)
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

#: Why talking to yourself is the first sign of success [1] <> Ka san yi wa kanka magana ba hauka ba ne, alama ce ta nasara? [2]

#: Eugene Gamble spent most of his career as a dentist in London, [3] <> Eugene Gamble ya shafe kusan tsawon rayuwarsa ta aiki a matsayin likitan hakori a Landan, [4]

#: quietly and diligently working on peoples teeth. [5] <> inda shiru kuma cikin natsuwa da kwazo yake yi wa mutane aiki a hakoransu. [6]

#: Then, three years ago, he decided to give up his lifes work [7] <> Kwatsam , shekera uku da ta wuce sai kawai ya yanke shawarar barin wannan aikin da kusan tsawon rayuwarsa abin da ya sani kenan [8]

#: to become an entrepreneur. [9] <> domin ya koma kasuwanci. [10]

#: There was just one problem: [11] <> To sai dai akwai matsala daya, [12]

#: he was no good at business. [13] <> matsalar ita ce bai iya kasuwanci ba. [14]

#: As his ideas failed, his confidence plunged. [15] <> Yayin da ya ga duk hanya ko kasuwancin da ya bullo wa sai ya kasa, sai guiwarsa ta yi sanyi. [16]

#: He could have gone back into dentistry [17] <> Da zai iya komawa aikinsa na likitan hakori, [18]

#: but he was determined to succeed in the business world. [19] <> to amma ya kuduri aniyar lalle sai ya yi nasara a fagen kasuwanci. [20]

#: So, he hired a business coach who gave him an odd piece of advice. [21] <> Daga nan ne ya dauko hayar wani kwararre da zai horad da shi a kan dabarun kasuwanci, wanda shi kuma ya ba shi wata shawara ta daban. [22]

#: He told me speak out loud,” says Gamble, who helps wealthy people invest in residential real estate. [23] <> Gamble wanda ke ba wa masu kudi shawara kan zuba jari a harkokin gidajen haya, ya ce, mutumin sai ya gaya min cewa in rinka fito da maganata fili ina yi ni kadai. [24]

#: Thats right. He was instructed to talk to himself. [25] <> Wato magana da kansa a fili. [26]

#: It was weird, because it was something new to me,” he says. [27] <> Gamble ya ce abin ya zamar masa banbarakwai, domin wani abu ne sabo a wurinsa. [28]

#: I didnt believe that it could work, [29] <> Ya kara da cewa bai yi tunanin hakan zi yi wani amfani ba, [30]

#: but once I tried itit made perfect sense.” [31] <> to amma yana fara gwadawa sai ya ga amfanin hakan. [32]

#: Talking to ourselves may seem strange [33] <> Abin zai iya zama wani bako ko banbarakwai [34]

#: because we tend to associate speaking out loud to nobody in particular as a sign of mental illness. [35] <> domin ana daukar mutum ya rika magana shi kadai kamar wata alama ce ta tabin hankali. [36]

#: However, theres a growing body of research to indicate that self-talk can help memory recall, [37] <> To sai dai akwai tarin bincike da ke nuna cewa mutum ya rika magana da kansa ko shi kadai, yakan sa mutum ya yi saurin tuna abu, [38]

#: confidence, [39] <> da ba shi karfin hali, [40]

#: focus and more. [41] <> da mayar da hankali kan abin da yake yi da sauransu. [42]

#: Its not an irrational thing to do,” says Gary Lupyan, an associate professor of psychology at the University of Wisconsin, [43] <> Masani a kan tunanin dan adam, mataimakin farfesa Gary Lupyan, na Jami'ar Wisconsin, [44]

#: who has studied how hearing ourselves speak can impact our memories. [45] <> wanda ya yi nazari a kan yadda idan mutum yana sauraren kansa yana magana hakan zai taimaka masa hadda, [46]

#: You dont know everything youre going to say[47] <> ya ce, yin hakan (wato mutum ya rika magana da kansa), ba hauka ba ne.- Ya ce duk abin da za ka furta ba lalle ne ka san shi ba, [48]

#: you can even surprise yourself.” [49] <> za ka ba wa kanka da kanka mamaki. [50]

#: His work, [51] <> A sakamakon nazari da binciken da ya yi a wannan fanni, [52]

#: which is one of the most cited studies in this field, [53] <> wanda kusan shi aka fi karantawa [54]

#: had people look at objects on a computer screen. [55] <> ya sa mutane suna kallon abubuwa a kwanfuta, [56]

#: Some had to say the name of the item out loud, [57] <> inda ya sa wasu daga cikin su rika fadar sunan abin da suke kallo da karfi, [58]

#: while others were instructed to remain silent and keep the word in their head. [59] <> yayin da ya sa sauran su yi shiru ka da su furta sunan. [60]

#: The result? [61] <> Ka san sakamakon da aka samu? [62]

#: The ones who said the word out loud were able to locate the objects on the screen more quickly. [63] <> Wadanda suka fadi sunan abin a fili ko da karfi, su suka iya ganin abin a kwamfutar da sauri. [64]

#: A similar experiment [65] <> A wani binciken irin wannan da aka yi, [66]

#: had people say the names of common grocery store items out loud. [67] <> shi ma an sa mutane su fadi sunayen wasu kayan abinci a fili. [68]

#: They then had to find those items by looking at photographs. [69] <> Daga nan kuma sai aka kawo hotuna aka sa su nuna abubuwan. [70]

#: The ones who said the words found the foods faster. [71] <> Wadanda suka fadi sunayen abubuwan a fili su suka yi saurin ganinsu. [72]

#: While we all know what a banana looks like, [73] <> Ya ce duk da cewa mun san yadda ayaba take [74]

#: saying the word aloud helps the brain activate additional information on that item, [75] <> amma fadin kalmar a fili na taimaka wa kwakwalwa ta samu karin bayani ko masaniya a kan ayaba, [76]

#: including what it looks like, he says. [77] <> abin da ya hada da yadda take a zahiri. [78]

#: We will, of course, find the banana at the store [79] <> Mai binciken ya ce, ba shakka za mu iya gano ayabar a kantin kayan abincin, [80]

#: regardless, [81] <> ko da ba mu furta sunanta ba a fili, [82]

#: but well find it faster if we speak the name. [83] <> amma za mu fi gano ta da sauri idan mun furta sunanta. [84]

#: Feel better with self-talk [85] <> Mutum na jin sauki idan ya yi wa kansa da kansa magana [86]

#: Anne Wilson Schaef, a former psychologist and [87] <> Wata tsohuwar malamar koyar da ilimin tunanin dan adam, Anne Wilson Schaef, [88]

#: now author and speaker, [89] <> wadda yanzu marubuciya ce da kuma gabatar da jawabi, [90]

#: often encouraged her clients to speak to themselves. [91] <> yawanci takan sa mutanen da take koyawa jawabi su rika magana da kansu. [92]

#: Not only did it improve her clientsmemories, [93] <> Bayan karfafa wa daliban nata haddarsu, ta yadda suke iya tuna abu da wuri, [94]

#: but it also changed the way many of them felt. [95] <> hakan ya kuma sauya yadda galibinsu ke ji. [96]

#: For instance, if a patient was angry, [97] <> Misali idan ran maras lafiya ya baci, [98]

#: shed tell them to say out loud what they were upset about. [99] <> sai ta bukace shi ya fadi abin da ya bata masa rai a fili ( da karfi). [100]

#: The anger would then disappear. [101] <> Daga nan sai ka ga wannan bacin ran ya kau. [102]

#: She believes it has something to do with who is listening to the words. [103] <> Tana ganin hakan abu ne da yake da alaka da wanda yake sauraron. [104]

#: All of us need to talk to someone whos interesting, intelligent, [105] <> Ta ce, dukkaninmu muna bukatar mu yi magana da wani wanda yake da sha'awarmu da basira, [106]

#: knows us well [107] <> wanda ya san mu sosai wanda kuma yake goyon bayanmu, [108]

#: and is on our side and thats us,” she says. [109] <> kuma wannan ba kowa ba ne illa mu kanmu. [110]

#: Were probably the most interesting person we know. [111] <> Ta ce, kusan ba wanda muka fi sani kamar mu kanmu. [112]

#: Knowing ourselves and how we feel can help us improve.” [113] <> Saboda haka sanin kanmu da yadda muke ji ka iya taimaka mana mu gyaru. [114]

#: Studies suggest that Schaef is onto something. [115] <> N/A [116]

#: In 2014, the University of Michigans Ethan Kross released a paper [117] <> A shekara ta 2014 Ethan Kross na Jami'ar Michigan ya yi wani rubutu [118]

#: saying that self-talk can make us feel better about ourselves and instil a confidence [119] <> wanda a ciki yake cewa magana da kanmu ka iya ba mu kwarin guiwa da jin dadi a kan kanmu, [120]

#: that can help us get through tough challenges. [121] <> wanda hakan zai iya taimaka mana mu yi maganin wani kalubale da ke gabanmu. [122]

#: However, we have to say the right words for this to work. [123] <> Amma sai mun furta kalmomin da suka dace kafin hakan ya yi aiki. [124]

#: Kross, along with several colleagues, [125] <> Kross tare da wasu abokan bincikensa, [126]

#: conducted a series of experiments [127] <> sun gudanar da gwaje-gwaje da dama, [128]

#: that had people describe emotional experiences [129] <> inda suka sa mutane su bayyana wani yanayi ko hali da suka shiga, [130]

#: using their own names or words likeyou,” “heandshe.” [131] <> ta hanyar amfani da sunansu ko kalmomi kamar kai da shi da ke. [132]

#: He found that talking in the third or second person, [133] <> Daga nan ya gano cewa mutum ya yi magana da wakilin suna na kai ko shi ko ke yana nufin shi kansa, [134]

#: helped people control their feelings and thoughts [135] <> hakan na taimaka wa mutum ya kwantar da hankalinsa da tunaninsa [136]

#: better than those who spoke in the first person. [137] <> fiye da wadanda suka yi amfani da kalmar wakilin suna ta ni. [138]

#: In another study, [139] <> A wani nazarin [140]

#: Kross, who outlined his research in the Harvard Business Review, [141] <> Kross wanda ya gabatar da sakamakon binciken nasa a Harvard, [142]

#: asked people to refer silently to themselves [143] <> ya bukaci mutane da su gabatar da kansu ( a ciki) [144]

#: in the second or third person while preparing for a speech [145] <> da wakilin suna na kai ko shi a yayin da suke shirya wani jawabi da za su gabatar, [146]

#: and found they were calmer, [147] <> sai ya gano hakan ya sa mutane sun fi kwantar da hankalinsu da kwarin guiwa, [148]

#: more confident and performed better on tasks than those who used only first-person words. [149] <> tare da tunani da kyau da kuma iya yin aiki fiye da wadanda suka yi amfani da kalmar wakilin suna ta ni. [150]

#: The results were so profound, wrote Kross, [151] <> Sakamakon ya ba wa Kross mamaki, [152]

#: that he now gets his young daughter to speak to herself in the third person [153] <> har ta kai yana sa karamar 'yarsa tana magana da kanta wato ita kadai, inda take gabatar da kanta da kalmar wakilin suna ta ita, [154]

#: when she is distressed. [155] <> a duk lokacin da ranta ya baci. [156]

#: While Gamble is not yet talking to himself in the third person[157] <> Duk da cewa har yanzu Gamble bai fara gabatar da kansa da kalmar wakilin suna ta shi ba, [158]

#: he finds it too strange[159] <> saboda yana ganin hakan kamar wani bakon abu, [160]

#: his coach has told him to repeat self-affirming comments out loud, [161] <> mai ba shi horo ya shawarce shi da ya rika amfani da kalmomi na karfafa zuciya da tabbatar da iko ko matsayi, [162]

#: such asdont do your best, do whatever it takes.” [163] <> misali, ka yi kawai ko ma me zai faru ya faru. [164]

#: He has taken that advice to heart and says it works. [165] <> Ya dauki wanna shawara kuma ya ce tana aiki. [166]

#: Self-talk has also helped him nail presentations [167] <> Kwarewa wajen gabatar da jawabi [168]

#: Self-talk has also helped him nail presentations. [169] <> Wannan dabara ta magana da kai, ta sa Gamble ya kware wajen gabatar da jawabi. [170]

#: Before he meets with a wealthy investor [171] <> Kafin ya gana da wani attajirin mai zuba hannun jari, [172]

#: he goes over his presentation out loud. [173] <> yakan yi nazarin abin da zai gabatar masa, [174]

#: Gamble first writes it down and then reads it out over and over again, [175] <> inda yakan yi ta karanta abin da ya rubuta a fili, [176]

#: fixing words he stumbles upon. [177] <> ya saba da kalmomin da ke ba shi matsala. [178]

#: By hearing himself speak, [179] <> Ya ce ta hanyar sauraren kansa yana karatu, [180]

#: his can better organise his thoughts, he says. [181] <> hakan na sa ya iya tsara maganganunsa da tunaninsa da kyau, [182]

#: He also remembers the presentation better. [183] <> kuma yana tuna bayani ko abin da zai gabatar da kyau. [184]

#: Talking to ourselves out loud is sometimes frowned upon[185] <> Wani lokaci mutum ya yi magana shi kadai da karfi ba abu ne da za a ji dadin yi ba, [186]

#: and we may not want to chat constantly with ourselves in public[187] <> kuma ba za mu so a ganmu ko da yaushe muna magana da kanmu ba a bainar jama'a, [188]

#: which is why most of us do not do it. [189] <> wanda abin da ya sa yawancinmu ba ma yin hakan kenan. [190]

#: Children do, however, and there is a lot of research that shows that [191] <> Yara su kuwa suna yi, domin bincike da dama ya nuna cewa, [192]

#: self-talk among kids is an important part of their development. [193] <> tsarin mutun ya rika magana da kansa na taimaka wa yara. [194]

#: A 2008 study, for instance, found that five-year-olds who talk to themselves out loud do better at motor tasks than when theyre quiet. [195] <> Domin a wani nazari na shekara ta 2008 a gano cewa yaro dan shekara biyar da ke magana da kansa (magana shi kadai) da karfi, ya ci kwazo a aikin da ya shafi kwakwalwa, fiye da idan ya yi shiru. [196]

#: Gamble believes he now has more confidence than ever. [197] <> Gamble yana ganin wannan tsari ya taimaka masa sosai ya ginu tare da samun kwarin guiwa fiye da da, [198]

#: While there are other things that have contributed to his successful transformation from dentist to real-estate entrepreneur, talking out loud has certainly played a part. [199] <> duk da cewa akwai wasu abubuwan da suka taimaka masa ya yi nasarar juyewa daga likitan hakori zuwa dan kasuwa mai harkar gidaje. [200]

Contents