Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/058 if all animals were smart

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: What would happen if all animals were as smart as us [1] <> Me zai faru idan dabbobi suna da hankali irin na mutane? [2]

#: If every species on the planet were suddenly equally intelligent, would we cooperate or fight? [3] <> Idan duk halittar da ke fadin duniyar nan na da hankali irin namu, zamu hada kai ne ko kuma zamu yaki juna? [4]

#: In Planet of the Apes, [5] <> A fim dinPlanet of the Apes’, [6]

#: a man finds himself in a world governed by hyper-intelligent primates that lord over enslaved human underlings. [7] <> wani mutum ya samu kansa a wata duniya da birrai masu hankali da tunani ke bautar da mutane. [8]

#: Pierre Boulle, author of the 1963 book on which the film series was based, [9] <> Pierre Boulle, wanda ya rubuta littafin a 1963 wanda daga baya aka mai da shi fim [10]

#: said his now-classic story fell under the genre ofsocial fantasy”. [11] <> ya ce labarin na sa na cikin rukuninin-da-ace’. [12]

#: What if that fantasy was expanded, however, [13] <> To me zai faru idan aka fadada hasashen, [14]

#: to include not only apes with human-like intelligence, [15] <> ya zama ba birrai ne kadai zasu yi irin tunanin mutane ba, [16]

#: but all species on Earth? [17] <> har ma dukkan wata nauin halitta dake duniya? [18]

#: What if every animal on the planet has suddenly woken up a rational, self-aware being? [19] <> Idan aka wayi gari duk dabbar da ke duniya ta zama mai hankali da tunani me zai faru? [20]

#: Would one creature come to rule all others, [21] <> Wata halittar za ta mulki ragowar ne [22]

#: much as we humans have done, [23] <> kamar yadda mutane su ka yi [24]

#: or would our varied kind arrive at some sort of peaceful, enlightened coexistence? [25] <> ko kuma za a samu sasantawa ne a gudanar da rayuwa cikin daidaito da mutunta juna? [26]

#: It might seem like an absurd thought experimentits certainly not possible[27] <> Wannan dai batu ne da ba zai taba yiwuwa ba [28]

#: however, exploring the question can reveal intriguing (and depressing) truths about human nature, [29] <> amma tattauna shi zai sa mu fahimci gaskiya game da dabiar biladama [30]

#: and our place as the planets dominant species. [31] <> da kuma matsayinmu a duniya, na halittar da ta mallake dukkan halittu. [32]

#: Unfortunately, the hypothetical answer isnt pretty: [33] <> Abin takaicin shi ne, da hakan za ta faru da lamarin ba zai yi kyau ba: [34]

#: Chaos would be the simple word for what would happen,” says Innes Cuthill, [35] <> “Rikici ne zai barke a bankasa,” in ji Innes Cuthill, [36]

#: a behavioural ecologist at the University of Bristol. [37] <> masanin dabiar zamantakewar halitta a jamiar Bristol. [38]

#: We should definitely not assume that intelligence is a good thing.” [39] <> “Mu daina dauka cewa hankali ya na sa kirki.” [40]

#: Wed all kill each other,” continues Robin Dunbar, [41] <> “Ai kashe juna zamu yi,” in ji Robin Dunbar, [42]

#: an evolutionary psychologist at the University of Oxford. [43] <> mai nazarin sassauyawar dabiar halittu a jamiar Oxford. [44]

#: Humans are not noted for their curiosity and peace in the context of meeting new people.” [45] <> “Ba a san mutane da neman zaman lafiya ba idan suka hadu da jinsin mutanen da basu san su ba.” [46]

#: Josep Call, a comparative psychologist at the University of St. Andrews, agrees. [47] <> Josep Call, mai ilimin kwatanta dabiar halittu a jamiar St. Andrews ya amince da cewa. [48]

#: If you look at human history, [49] <> “Idan ka duba tarihin dan Adam, [50]

#: I am very pessimistic about just wanting to be friends,” he says. [51] <> ba na jin mun yi shahara kan kulla abota. [52]

#: Maybe now were a little better than we were in the past, [53] <> Ba mamaki yanzu mun dan sassauta fiye da kakanninmu na baya, [54]

#: but look around the world and tell me if you think that is really the case.” [55] <> amma duba duniyar a yanzu ka gaya man in har mutane jinsin lumana ne.” [56]

#: Given our long track record [57] <> Idan aka yi laakari da dogon tarihin da mu ke da shi [58]

#: of exterminating other species [59] <> na hallaka wasu jinsin halittun [60]

#: as well as our own kind, [61] <> har ma dayan uwanmu mutane, [62]

#: theres no reason to think that either we [63] <> babu wani dalili da ke nuna cewa mu, [64]

#: or the now self-aware animals would behave any differently. [65] <> ko kuma duk wata dabba da ta samu irin tunaninmu za mu iya wata dabia sabanin wacce mu ke a kai. [66]

#: Essentially, World War Three would likely break out. [67] <> A takaice dai, yakin duniya na uku ne zai barke. [68]

#: We react very negatively and aggressively to strangers and to threats,” Cuthill says. [69] <> “Mu na da mummunar alaka tsakaninmu da bakin jinsi musamman wadanda mu ke kallonsu a matsayin barazana,” in ji Cuthill. [70]

#: Given that, who would win? [71] <> Idan ko haka ne, wa zai yi nasara? [72]

#: Many species, of course, would not stand a chance. [73] <> Jinsina da yawa dai ba su da alamar nasara. [74]

#: Herbivores, for example, [75] <> Misali, duk dabbobin da ke cin tsirrai zalla, [76]

#: need to spend most of their time eating grass in order to acquire enough energy to function. [77] <> na bukatar bata lokaci da yawa wurin cin abinci da zai ishe su. [78]

#: This limits the time they could invest in communication, [79] <> Don haka za su samu takaitaccen lokacin da za su sadar da bayanai a tsakaninsu, [80]

#: tool making, [81] <> su kera ababen more rayuwa, [82]

#: culture-building or engaging in combat. [83] <> su bunkasa aladunsu ko kuma su yi yaki. [84]

#: Protein-eaters would thus have an edge. [85] <> Don haka dabbobin da ke cin abinci samfurin protein su ne za su yi zarra. [86]

#: Sharks, dolphins and killer whales would be out, [87] <> A cikinsu, kifayenshark’, ‘dolphin’, dawhalesu ma ba inda za su kai [88]

#: since they are confined to the ocean[89] <> tun da iyakarsu cikin ruwa. [90]

#: although oceanic creatures may engage in their own underwater struggles for power. [91] <> Sai dai za su iya fafatawa tsakaninsu don samun mulkin cikin ruwan. [92]

#: Likewise, animals that cannot survive outside of their particular nichethe swamp, the rainforest canopy, [93] <> Haka kuma duk dabbobin da ba sa iya rayuwa sai a wasu kebantattun wurare kamar kurmi, [94]

#: the desert[95] <> ko hamada [96]

#: would not be able to conquer the world, [97] <> ba za su iya mulkar duniya ba. [98]

#: Large predators like lions, [99] <> Manyan mafarauta irin su zaki, [100]

#: tigers, [101] <> damisa, [102]

#: bears, [103] <> da kyarkyeci [104]

#: wolves and even non-predators [105] <> da ma wadanda ba sa farautar [106]

#: like elephants [107] <> irin su giwa [108]

#: and rhinos, [109] <> da mugun dawa [110]

#: however, could have a go at it, á la Jurassic Park. [111] <> su ne zaa fafata da su, kamar yadda ta faru a fim dinJurassic Park.’ [112]

#: In the short term, [113] <> A farkon wayewarsu, [114]

#: they would likely pose the biggest threat to our dominion. [115] <> su ne zasu zama babbar barazana gare mu. [116]

#: Should we be stripped naked and thrown into the savannah or forest, [117] <> Da zaa tsiraita mu a jefa mu cikin dokar daji, [118]

#: they would most definitely beat us. [119] <> tabbas su za su yi nasara akan mu. [120]

#: But given our possession of modern weapons [121] <> Amma kasancewar muna da makaman zamani, [122]

#: and the fact that humans are far more numerous than other large predators, [123] <> kuma mutane sun fi wadannan dangin halittun yawan alumma, [124]

#: those creaturesnewfound smarts would likely only allow them to outmanoeuvre us for a brief time [125] <> barazanar ta su ba za ta yi nisa ba [126]

#: before we obliterated them [127] <> kafin mu shafe su daga bayan kasa [128]

#: (which, incidentally, we are currently already in the process of doing for many). [129] <> (abinda, a yanzu ma muke cikin yi wa jinsin halittu da yawa). [130]

#: As Alex Kacelnik, a behavioural ecologist at the University of Oxford, says: “Ultimately, I think wed beat them to the ground. We would win.” [131] <> Kamar yadda Alex Kacelnik, masanina dabiar zamantakewar halittu a jamiar Oxford ya ce: “Daga karshe dai mu zamu yi nasara.” [132]

#: But with the most formidable carnivores out of the picture, a new competitor would emerge: [133] <> Amma fa da zarar mun kawar da manyan dabbobi masu cin nama, zamu fuskanci wadansu abokan adawar: [134]

#: our closest primate relatives. [135] <> ‘yan uwanmu makusanta, wato birrai. [136]

#: As Cuthill points out, [137] <> Kamar yadda Cuthill ya bayyana, [138]

#: our technology [139] <> kayayyakin fasaharmu [140]

#: has largely enabled us to come as far as we have as a species, [141] <> sun taimaka matuka wurin ci gabanmu, [142]

#: and primates share much of the same physiology [143] <> kuma birrai na da halitta irin ta mu, [144]

#: that allows us to use that technology. [145] <> wacce za ta basu damar amfani da fasaharmu. [146]

#: Chimpanzees, orangutans, bonobos and gorillas could access our computers [147] <> Za su iya amfani da kwamfutocinmu, [148]

#: and wield our guns [149] <> su rike bindigoginmu [150]

#: while also enjoying the benefits of stronger and more agile bodies than the human form. [151] <> sannan su amfana da halittar jikinsu wacce tafi ta dan Adam kuzari. [152]

#: They could also quickly set about creating unique technologies by coopting human tools for their own use. [153] <> Haka kuma za su iya kirkiro na su kayan fasahar cikin gaggawa ta hanyar amfani da kayan fasahar mutane. [154]

#: But our primate cousinsabilities to do all of this [155] <> Sai daiyan uwanmu birrai zasu iya wadannan abubuwa ne kurum [156]

#: would likely hinge on whether they can somehow hack into our accumulated knowledge, [157] <> idan har za su iya samun tarin ilimin da mu ke da shi [158]

#: including how to use technologies, [159] <> a yadda ake amfani da kayayyakin fasahar, [160]

#: how to engage in effective warfare, [161] <> yadda ake yaki, [162]

#: how to understand us[163] <> yadda za su fahimce mu[164]

#: the enemy[165] <> abokan gabarsu[166]

#: and much, much more. [167] <> da kuma sauran ilimai da dama. [168]

#: Harnessing that knowledge for their own use [169] <> Amfani da iliminmu domin amfaninsu [170]

#: would be key to domination, [171] <> shi ne hanya guda tilo da zasu iya bi wurin murkushe mu. [172]

#: but it is something they likely would not be able to achieve before we took them out as well. [173] <> Sai dai ba za su samu wadataccen lokacin da za su mallaki iliminmu kafin su ma mu kawar da su daga doron kasa. [174]

#: If they were given all this knowledge then wed have a tie between humans and primates,” Call says. [175] <> “Da ace za su samu duk ilimin da muke da shi to da za a yi canjaras tsakanin mutane da birrai,” in ji Call. [176]

#: If not, even though theyd be a strong contender, [177] <> “In kuwa ba haka ba, koda yake za su zamo babban kalubale gare mu, [178]

#: they would still not become the dominant species.” [179] <> duk da haka ba zasu iya mallake duniya ba.” [180]

#: With enough time, though, [181] <> Amma fa idan lokaci ya tsawaita, [182]

#: the ability to quickly adapt to changing environments and circumstances would likely be the strongest weapon in the quest for world domination. [183] <> babban ginshikin mallakar duniya shi ne iya rayuwa cikin kowanne yanayi da muhalli. [184]

#: Indeed, this is one of the skills at the heart of humanitys ability to conquer the Earth. [185] <> Hakika, wannan kwarewar na daga cikin sirrin daukar biladama a ban kasa. [186]

#: Though we evolved in warm grasslands, [187] <> Duk da dai asalinmu daga yanki mai dumi da yawan ciyayi mu ke, [188]

#: we soon found ways to inhabit environments that varied drastically [189] <> mun gano hanyoyi da dama na rayuwa a sassan duniya dabam-daban, [190]

#: compared to our primordial origins, from mountain tops to the tundra. [191] <> kama daga tsaunuka zuwa hamadar kankara. [192]

#: Numbers would also count, [193] <> Haka kuma yawan adadi zai yi rana, [194]

#: as would the ability to evade detection. [195] <> da kuma kwarewa wurin iya buya. [196]

#: In other words, [197] <> Watau dai, [198]

#: all evidence points to bacteria and other microbes inheriting the Earth[199] <> alamomi na nuna cewa halittunbacteriada sauran kananan halittu irinsu su ne za su gaje mulkin duniya[200]

#: even more so than they already do today. [201] <> fiye da yadda su ke yi a yanzu. [202]

#: No, bacteria do not have nervous systems, [203] <> Aabacteriaba su da kwakwalwa [204]

#: so the idea of them becoming intelligent is even more far-fetched than that of other multi-cellular species suddenly developing smarts to rival our own. [205] <> don haka ba zata taba yiwuwa su samu hankali da tunani irin na mutane ba. [206]

#: But that impossibility is likely a blessing, given their ubiquity. [207] <> Amma dai gazawar tasu, alheri ne a gare mu, idan aka yi laakari da yawansu. [208]

#: Bacteria are already everywhere, including inside us,” Call says. [209] <> “Ko a yanzubacteriana koina, har da cikin jikinmu,” in ji Call. [210]

#: They would be a very, very strong contender.” [211] <> “Da za su yi hankali da kuwa za su iya ganin bayanmu.” [212]

#: It wouldnt surprise me if something small wins,” agrees Dunbar. “My guess is were likely to become prey to much more primitive forms of life, to bacteria and viruses.” [213] <> “Ba zan yi mamaki ba idan wata karamar halitta danginvirusta mallake duniya,” in ji Dunbar. [214]

#: Humans would be in deep trouble if they had to fight intelligent bacteria, especially the really bad ones,” Call says. [215] <> “Mutane za su shiga cikin balai idan fada ya hado su da kananan halittu masu hankali da tunani,” in ji Call. [216]

#: The problem is we could not get rid of them all, [217] <> “Matsalar ita ce, ba zamu iya kawar da su ba, [218]

#: because they are essential for our own survival.” [219] <> saboda mu na bukatarsu domin ci gaba da rayuwa.” [220]

#: Even if humanity is killed off, however, [221] <> Koda an hallaka mutane baki daya, [222]

#: conflicts would likely continue to rage on. [223] <> rikicin dai ba karewa zai yi ba. [224]

#: Theres no reason to believe [225] <> Babu wani dalili da zai sa mu yi tsammanin [226]

#: any animal with Homo sapiens-level intelligence [227] <> dabbobin da ke da hankali da tunani irin na mutane [228]

#: would behave any differently [229] <> za su yi halayya dabam [230]

#: than we ourselves have in terms of exploitation of other species and resources. [231] <> da wacce mu ke yi ta wurin murkashe sauran halittu da mallake su. [232]

#: Likewise, [233] <> Haka kuma [234]

#: intra-species conflict would also break out. [235] <> za a samu rikice-rikice cikin jinsin halittu guda. [236]

#: Remember that animals dont solve problems for the good of their species,” Kacelnik says. [237] <> “Ku tuna cewa dabbobi ba sa magance matsaloli domin amfanin jinsinsu baki daya,” in ji Kacelnik. [238]

#: They compete within the species [239] <> “Su na rigima da junansu ne [240]

#: for the advantage of their own kind, their own cultural or family group.” [241] <> domin amfanin kabilarsu ko iyalansu.” [242]

#: All told, the situation would probably end badly for almost everyone. [243] <> Watau dai kusan babu wanda zai amfana idan kowacce halitta ta sami hankali da tunani irin na mutane. [244]

#: As species fell, [245] <> Duk lokacin da aka karar da wani jinsin halitta, [246]

#: ecosystems would collapse, [247] <> muhallan da suke ciki za su ci gaba da lalacewa, [248]

#: leaving only the heartiest survivors[249] <> babu wanda zai tsira sai dai masu kwarin rai [250]

#: the bacteria, cockroaches and perhaps ratsto inherit the Earth. [251] <> irin subacteria’, kyankasai da ko gafiyoyi. [252]

#: As Cuthill says, [253] <> Kamar dai yadda Cuthill ya ce: [254]

#: whichever species were left wouldprobably screw up the planet just like were doing”. [255] <> “Duk jinsin halittar da aka bari a baya, za su bata duniyar ne kamar yadda mu ke yi a yanzu.” [256]

#: I dont see any reason to think that other species would be any more altruistic than we are,” he says. [257] <> Ya ce: “Ba na jin akwai wani jinsin halittu da za su fi mu tausayi da jin kai. [258]

#: The balance of nature that we see is only there because of a balance of power.” [259] <> Daidaiton da ake samu a rayuwar yanzu na faruwa ne saboda wani yafi wani karfi a duniya.” [260]

Contents