Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/045 bestseller secret

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: A new book claims to have the formula to a bestselling novelbut can an algorithm help writers have a hit? Hephzibah Anderson investigates. [1] <> Marubuta sun bayar da shawarwari game da dabaru da matakan da marubuci ya kamata ya dauka domin littafinsa ya samu karbuwa a kasuwa [2]

#: As countless writing tutorials preach, an arresting opening line is crucial to ensnaring an audience. [3] <> Darussan koyar da rubutu da dama kan jaddada muhimmancin jumlar farkon littafi wurin samun karbuwarsa a wurin masu karatu. [4]

#: The authors of a new book, seductively titled The Bestseller Code, concur. [5] <> Marubutan wani sabon littafi mai taken 'The Bestseller Code' sun amince da wannan ra'ayi. [6]

#: They are Jodie Archer and Matthew L Jockers, and along with Days, [7] <> Jodie Archer da Matthew L. Jockers [8]

#: they single out opening sentences by the likes of Toni Morrison, Jeffrey Eugenides and Virginia Woolf. [9] <> sun ce jumlolin da fitattun marubuta irin su Sylvia Day, da Toni Morrison, da Jeffrey Eugenides da Virginia Woolf [10]

#: All say, encapsulate the conflict of a 300-page story in some 20 words or less. [11] <> kan yi amafani da su wurin bude labaransu, kan dunkule rikicin da ke cikin littafi mai shafuka 300 a cikin jumla guda mai kalmomi 20 ko ma kasa da haka. [12]

#: But while Archer and Jockers both boast appropriately bookish credentials[13] <> Ko da yake Archer da Jockers na da dangantaka da harkar littattafai[14]

#: she is a former Penguin editor, [15] <> domin kuwa ita tsohuwar edita ce a kamfanin wallafa littattafai na Penguin, [16]

#: he is an associate professor of English at the University of Nebraska[17] <> yayinda shi kuma farfesan nazarin Ingilishi ne a Jami'ar Nebraska[18]

#: their advice has a highly unconventional derivation. Its based on the gleanings of an algorithm. [19] <> wannan shawarar ta su ta dogara ne kacokan a kan alkaluman lissafi. [20]

#: Archer also happens to have worked at Apple [21] <> Archer ta kuma yi aiki a kamfanin Apple, [22]

#: and Jockers, a self-styledliterary quant”, and was the co-founder of Stanford Universitys Literary Lab in Silicon Valley. [23] <> shi kuma Jockers yana daga cikin wadanda suka kafa cibiyar gwaje-gwajen adabi ta Jami'ar Stamford. [24]

#: By harnessing machine learning [25] <> Ta hanyar amfani da na'urorin kwamfuta, [26]

#: theyve been able to mine the texts of 20,000 novels [27] <> sun bi diddigin littattafan kagaggun labarai fiye da 20,000 [28]

#: published over the past 30 years, [29] <> wadanda aka wallafa a shekaru 30 da suka gabata, [30]

#: analysing theme, plot, and character, [31] <> inda suka yi nazarin jigo, da zubi, da warwarar labarin, da taurarin littattafai [32]

#: along with other variables such as style and setting. [33] <> da kuma abubuwan da suka danganci salo da wurin da aka gina labarin a kai. [34]

#: Pulling together all these data points, [35] <> Sun ce idan aka tattara wadannan bayanan, [36]

#: they say their algorithm can predict whether a manuscript will become a New York Times bestseller. [37] <> lissafinsu zai iya hasashen ko littafi zai yi kasuwa ko ba zai yi ba. [38]

#: It gave Chad Harbachs literary debut, The Art of Fielding, a 93.3% chance of becoming a bestseller. [39] <> Lissafin nasu ya nuna cewa littafin 'The Art of Fielding' na Chad Harbach na da damar yin fice a kasuwa da kaso 93.3 cikin dari. [40]

#: Mitch Alboms spiritual tale, The First Phone Call from Heaven, was 99.2% – [41] <> Littafin Mitch Albom mai taken 'The First Phone Call From Heaven' ya samu maki 92.2 cikin dari, [42]

#: the same as Michael Connollys The Lincoln Lawyer. [43] <> haka ma 'The Lincoln Lawyer' na Michael Connolly. [44]

#: These figurestheir existence, their decimal places, their accuracyhave made some people excited, [45] <> "Samuwar wadannan alkaluman lissafi sun faranta ran wadansu mutane, [46]

#: others angry, and more than a few suspicious”, Archer and Jockers admit. [47] <> sun fusata wadansu, sannan kuma da dama sun shiga tantama", in ji Archer da Jockers. [48]

#: What if? [49] <> In da ace [50]

#: Of course, theres a sturdy canon of writing advice already out there. [51] <> Tuni dai masana suka dade suna bayar da shawarwari game da dabaru da matakan da marubuci ya kamata ya dauka domin littafinsa ya samu karbuwa a kasuwa. [52]

#: According to Stephen King, you should focus not on plot but situation, [53] <> A cewar Stephen King, ba zubin labari ne ya kamata ya dauki hankalin marubuci ba sai dai yanayin da za a gina labarin a kai, [54]

#: the most interesting of which can be expressed as awhat-if?’ question. [55] <> wanda za a dunkule shi da fadin "in da ace", wato me zai faru in da kaza da kaza za su faru? [56]

#: Go easy on the research, [57] <> Haka kuma ba sai ka zurfafa bincike ba, [58]

#: beware of dialogue, [59] <> ka yi hattara da yadda taurarin littafin ke tattaunawa da juna, [60]

#: and remember that people love reading about work. [61] <> kuma ka tuna cewa mutane suna son karanta labarin ciki. [62]

#: God knows why but they do”. [63] <> "Ban san dalili ba amma dai su na so," in ji Stephen King. [64]

#: In Writing with the Master, [65] <> A cikin littafin "Writing With the Master" [66]

#: Chicago ad-man Tony Vanderwarker [67] <> mashiryin tallace-tallace a garin Chicago Tony Vanderwarker [68]

#: highlights three secrets of success as [69] <> ya bayyana sirrika uku na daukakar littafi [70]

#: taught him by none other than John Grisham: [71] <> da ya ce fitaccen marubuci John Grisham ne ya koya masa: [72]

#: have an elevator pitch, a strong middle and a great hook. [73] <> ka samu dunkulallen labari, wanda tsakiyarsa ke da kwari sannan kuma yana da jan hankali. [74]

#: Sophie Kinsella, author of the Shopaholic series, has more practical advice: [75] <> Sophie Kinsella, marubuciyar jerin littattafan Shopaholic cewa ta yi sirrin rubuta littafin da zai karbu a kasuwa shi ne: [76]

#: always carry a notebook, [77] <> kullum ka kasance dauke da littafin rubuta sababbin abubuwa, [78]

#: always plan [79] <> ka tsara yadda za ka rika rubuta labarai, [80]

#: and take a break for a cocktail if you get stuck. [81] <> sannan kuma ka shakata da barasa idan ka ji rubutun ya cushe ma. [82]

#: Few know more about the mechanics of bestsellerdom than Jonny Geller, [83] <> Mutane kadan ne a duniya suka fi Jonny Geller, [84]

#: joint CEO and MD of the books division at literary and talent agency Curtis Brown. [85] <> shugaban sashen wakiltar marubuta na kamfanin Curtis Brown, sanin sirrin yadda littafi ke samun karbuwa a kasuwa. [86]

#: Agent to the likes of John le Carré, Tracy Chevalier and David Nicholls, [87] <> Geller, wanda shi ne wakilin fitattun marubuta irinsu John le Carré, da Tracy Chevalier, da David Nicholls, a wurin kulla yarjejeniya da kamfanonin wallafa litattafai, [88]

#: Geller recently delivered a TEDx talk [89] <> Geller ya gabatar da wata laccar TEDx, [90]

#: distilling 20 yearsworth of observations to five main components that the mostphenomenalof bestsellers share. [91] <> inda ya bayyana muhimman abubuwa biyar da litattafan da suka fi karbuwa a kasuwa suka kunsa bisa nazarin da ya yi na tsawon shekaru 20. [92]

#: They include a well-crafted voice [93] <> Abubuwan sun hada da gamsasshiyar muryar bayar da labari, [94]

#: with a story powerful enough to provide a bridge, that transports the reader from somewhere familiar to somewhere new. [95] <> da kuma kwakkwaran labarin da zai iya dauke mai karatu daga duniyar da ya saba da ita zuwa wata duniyar ta daban. [96]

#: The story should also have deeper themes that resonate beyond itshook” – Emma Donoghues Room, [97] <> Haka kuma labarin na bukatar jigo mai taba zuciya fiye da ainihin abin da ya ja hankali a cikinsa. [98]

#: for instance, is not just about a mother and child holed up in a room for years, [99] <> Misali littafin 'Room' na Emma Donoghue ya zarta jigon wata uwa da danta da aka kulle a daki tsawon shekaru, [100]

#: it is about parental love in its purest form. [101] <> ya tabo batun irin tsantsar son da iyaye ke yi wa 'ya'yansu. [102]

#: Sometimes, he says, a book will simply tap into the zeitgeist[103] <> Ya ce kuma, wani lokacin littafi kan dace ne da zamanin da ya fito [104]

#: itprovides escapism in a terrifying world, [105] <> ya "samar da mafaka a lokacin da duniya ke cikin yamutsi, [106]

#: echoes paranoia in an insecure one, [107] <> ya bayyana tsoro lokacin da ake cikin fargaba, [108]

#: promotes romance in an era of indulgence, explores literary complexity in a society in turmoil.” [109] <> ko kuma ya tallata soyayya a lokacin da ake cikin jin dadi." [110]

#: Just make sure the reader has to turn each page, desperate to find out what happens next. [111] <> Sirrin karbuwar littafi shi ne ka tabbatar mai karatu ya juya shafi na gaba cike da shaukin gano mai ya faru. [112]

#: Ultimately, plenty of Archer and Jockersfindings jive with the advice that is already available, [113] <> Alkaluman lissafin Archer da Jocker sun dace da mafi yawan shawarwarin da aka saba bai wa marubuta, [114]

#: its just that big data has enabled them to create graphs and bar charts [115] <> kawai dai samuwar na'urorin tattara bayanai tare da nazari a kansu [116]

#: to demonstrate the importance of a rhythm in a plot, for instance. [117] <> ta ba su damar nuna muhimmancin wasu abubuwan da aka sani kamar samun fadi-tashi a cikin warwarar jigon littafi. [118]

#: But this granular approach has yielded some surprising insights that a human reader, [119] <> Sai dai kuma wannan tsarin na son a bi diddigi, [120]

#: too caught up in the drama and beauty of a text, is likely to miss. [121] <> ya sa suna iya gano abin da mutum ba zai gane ba saboda dadin labari ya kwashe shi. [122]

#: For instance, sex sells but only in a niche marketerotica, unsurprisingly. [123] <> Misali, sun gano cewa jima'i na sayar da littafi amma iri guda kurum, wanda daman an yi shi ne don batsa. [124]

#: But is there really a formula to be found? [125] <> Amma anya da akwai wata dabarar da za a iya amfani da ita ko da yaushe domin littafi ya samu karbuwa? [126]

#: As Jeffrey Archer quipped when I asked him about it: [127] <> Da na tambayi marubuci Jeffrey Archer sai ya ce: [128]

#: Yes, there is a formula for writing a bestseller. Just make sure the reader has to turn each page, desperate to find out what happens next. Its that easy.” [129] <> "Akwai mana. Kurum ka tabbatar mai karatu ya juya shafi na gaba cike da shaukin gano mai ya faru. Shi ke nan." [130]

#: Painting by numbers [131] <> Kashe basira [132]

#: That hasnt stopped aspiring authors from trying over the years[133] <> Hakan bai hana masu burin rubuta littafi kokarin nemo sirrin ba[134]

#: sometimes with extravagant success. [135] <> wani lokacin kuma su kan dace da gagarumar sa'a. [136]

#: When bit-part actress Jacqueline Susann knuckled down to writing her one and only novel in 1962, [137] <> Lokacin da wata 'yar fim Jacqueline Susann ta so rubuta littafinta na farko kuma na karshe a 1962, [138]

#: she wanted it to be a smash hit, like novels by Harold Robbins, the big seller of the day. [139] <> ta bayyana kudirin samar da labari mai kasuwa kamar irin litattafan Harold Robbins, wanda shi ke tashe a zamanin. [140]

#: She bought three copies of each of his books and got out her scissors (literally). [141] <> Don haka sai ta sai littattafansa uku da suka fi kasuwa ta duba kamanceceniyar da ke tsakaninsu sannan ta rubuta nata, bisa wannan tsarin da ta gano. [142]

#: Her efforts paid off and the resulting novel, Valley of the Dolls, went on to become the fastest seller in history. [143] <> Nata littafin, 'Valley of the Dolls' ya zamo littafin da aka fi saurin cinikinsa a tarihi kuma har yanzu ana ci gaba da sake wallafa shi. [144]

#: At the other end of the market, [145] <> A daya bangaren kuma, [146]

#: post-graduate courses in creative writing [147] <> kwasa-kwasan gaba da digiri da ake gudanarwa a manyan jami'o'i [148]

#: trade on the idea that good literary writing can be, if not quite taught, then productively nurtured. [149] <> na nuna cewa rubutu baiwa ce da ba za a iya koyar da ita ba, sai dai a nuna maka yadda za ka kyautata baiwarka. [150]

#: One of this summers runaway bestsellers [151] <> Daya daga cikin litattafan da suka fi samun kasuwa a bana, [152]

#: is Stephanie Danlers Sweetbitter. [153] <> Sweetbitter' na Stephanie Danler [154]

#: A first novel about life and love behind the scenes in a fancy New York restaurant. [155] <> ya bayar da labarin yadda rayuwa ke gudana ne a cikin wani kayataccen shagon sayar da abinci a birnin New York. [156]

#: Danler writes from experienceshe waitressed at Danny Meyers famous Union Square Café – [157] <> Danler ta rubuta abin da ta sani ne kasancewar ta taba yin aikin shagon sayar da abinci a New York, [158]

#: but her prose [159] <> amma kuma salon rubutunta [160]

#: has also been shaped by an MFA at the New School, [161] <> ya samo asali ne daga digiri na biyu da ta yi a kan rubuta kagaggun labarai. [162]

#: where she was taught by its fiction coordinator, Helen Schulman, herself a bestselling author. [163] <> Daya daga cikin malamanta, wacce ita ma fitacciyar marubuciya ce, Helen Schulman, [164]

#: Self-confessedly old school, Schulman is squeamish about the idea of a writer using the bestseller-o-meter to advance their work. Moreover, she finds it hard to envisage how literary talent and the hard graft needed to help it flourish could ever be strategised. [165] <> ta ce babu wasu alkaluman lissafi da za su bayyana sirrin daukakar Danler: [166]

#: It's who Stephanie is from her head and heart down to her fingertips that [167] <> "Rayuwar Stephanie da baiwarta [168]

#: made Sweetbitter what it is. Nothing predictable about that”. [169] <> su ne suka yi tasiri a kan littafin 'Sweetbitter' ba wasu alkaluman lissafi ba." [170]

#: Even if there were such a code, [171] <> Idan har da akwai dabarar da marubuta za su yi amfani da ita domin littafinsu ya samu karbuwa, [172]

#: wouldnt applying it to prose have a deadening effect[173] <> anya hakan ba zai kashe musu basira ba, [174]

#: like a kind of literary painting by numbers? [175] <> ya zama kowa ya koma yin abu guda? [176]

#: Nothing hinders novelists other than the limits to their own imagination”, says Geller. [177] <> "Babu abinda ke yi wa mai kirkirar labari kamar ace za a takaita tunaninsa," in ji Geller. [178]

#: But one writer who admits shed be curious to get her hands on the software is Naomi Alderman, [179] <> Sai dai wata marubuciya da ta ce za ta so ta samu wadannan alkaluman lissafin karbuwar littafin ita ce Naomi Alderman, [180]

#: bestselling author of novels including Disobedience, and co-creator of hit fitness app, Zombies, Run! [181] <> marubuciyar fitattun littattafai irin su Disobedience. [182]

#: We all know that appearing on the bestseller lists is only one measure of a book's success,” she observes, “and that a certain kind of formulaic book does tend to sell very well, just as formulaic pop music often sells well. People like what they're familiar with. [183] <> Ta ce: "Kowa ya san akwai irin littattafan da kan samu karbuwa a kasuwa fiye da wasu saboda mutane sun fi son abin da suka saba da shi. [184]

#: I'm really most interested in the bestsellers that no formula could predictand in brilliant books that aren't bestsellers at all.” [185] <> Sai dai ni nafi sha'awar littattafan da suka yi kasuwa bayan sun sabawa wadancan ka'idojin ko kuma littattafan da ba sa kasuwa duk da kasancewar sun yi rubutu da kyau." [186]

#: In fact, some hit novels did slip past the bestseller-o-meter. Archer and Jockers admit that the bestseller-o-meter was confounded by 15% of the books it analysed, [187] <> A hakikanin gaskiya, akwai littattafan da suka sabawa alkaluman lissafin Archer da Jockers. [188]

#: among them Kathryn Stocketts The Help, whose chances of success it rated as 50-50. [189] <> A cikinsu akwai 'The Help' na Kathryn Stockett wanda na'urar ta ce ya na da kashi 50 cikin dari na shika-shikan karbuwa a kasuwa, sai ga shi kuma ya yi fice fiye da zatonsu. [190]

#: Only one book, apparently, scored 100%: Dave Eggers2013 novel, The Circle. [191] <> Haka kuma littafi daya ne kurum 'The Circle' na Dave Eggers ya cika duk sharuddan Archer da Jockers inda ya samu maki dari bisa dari. [192]

#: It has a solid opening sentence, [193] <> Littafin dai an bude shi da jumla mai daukar hankali, [194]

#: three themes that make up roughly 30% – thewinning formula’ – a three-act plotline, a symmetrical emotional plotline, a balanced style and a strong heroine with great agency, all of which make it the paradigmatic hit. [195] <> ga shi da salo mai kyau da tauraruwa mai kokari, [196]

#: It also just happens to be about technology. [197] <> sannan kuma ya danganci fasahar zamani. [198]

#: But the real kicker? In sales terms, The Circle was a flop. [199] <> Sai dai kuma da aka fitar da shi kasuwa, littafin 'The Circle' ko kudin wallafa shi ba a mayar ba, balle a yi zancen riba! [200]

Contents