Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/060 animals suicide

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: Many animals seem to kill themselves, but it is not suicide [1] <> Shin dabbobi na kashe kansu da kansu? [2]

#: Do dogs, whales, horses and other animals intend to end their lives? [3] <> Da gaske ne karnuka, dawaki da sauran dabbobi kan hallaka kansu da gangan? [4]

#: In 1845 a curious story appeared in the Illustrated London News. [5] <> A 1845 jaridar Illustrated London News ta wallafa wani labari mai ban mamaki. [6]

#: A black dog, described as "fine, handsome and valuable" was reported to "throw himself into the water" [7] <> Wani kare da jaridar ta bayyana a matsayinlafiyayye, kyakkyawa kuma mai daraja ya jefa kansa cikin ruwa[8]

#: in an attempted suicide. [9] <> da niyyar hallaka kansa. [10]

#: His legs and feet were in "perfect stillness" – [11] <> Kafafuwansa natsaye cik”, [12]

#: highly unusual for a dog in a river. [13] <> abinda ba a saba gani ba ga Karen da ke cikin ruwa. [14]

#: Even stranger, [15] <> Abinda ma yafi ba da mamaki shi ne, [16]

#: after he was dragged out [17] <> bayan tsamo shi [18]

#: he "again hastened to the water and tried to sink again…" [19] <> “sai ya sake afkawa cikin ruwan ya na kokarin nutsewa.” [20]

#: Eventually the handsome dog succeeded in his apparent suicidal mission and died. [21] <> Daga karshe dai sai da kyakkyawan karen ya yi nasarar hallaka kansa cikin kogin. [22]

#: According to the Victorian press, [23] <> A cewar jaridar, [24]

#: this dog was far from alone in attempting such a fate. [25] <> ba wannan karen ne kadai ya kashe kansa da kansa ba. [26]

#: Shortly afterwards, [27] <> Ba a jima bayan labarin karen ba, [28]

#: two other cases appeared in the popular press: [29] <> aka wallafa wasu labaran biyu; [30]

#: a duck drowned on purpose, [31] <> wata agwagwa da ta nutse a ruwa da gangan, [32]

#: and a cat hanged herself on a branch after her kittens had died. [33] <> da kuma labarin magen da ta rataye kanta a reshen bishiya bayan dayayanta su ka mutu. [34]

#: But what was the truth of these incidences? [35] <> To amma, me ye gaskiyar wadannan labarai? [36]

#: We know that animals can suffer from mental health issues in the same way humans do: [37] <> Mun san cewa dabbobi ma kan samu tabuwar kwakwalwa kamar yadda mutane ke yi: [38]

#: in particular they feel stress and get depressed, [39] <> musamman sanadiyyar damuwa da kuma matsananciyar gajiya: [40]

#: factors contributing to the act of suicide in humans. [41] <> abubuwan da ke jawo mutane su kashe kansu da kansu. [42]

#: We also know that behaviours once thought to be uniquely human have now been found in other animals. [43] <> Mun kuma san cewa dabioin da ada ake ganin mutane ne kawai ke yinsu an gano cewa wasu dabbobin ma na yi. [44]

#: But is suicide among them? [45] <> To amma, har da kashe kai da gangan a cikinsu? [46]

#: Do animals really, knowingly attempt suicide? [47] <> Da gaske dabbobi su kan yi kokarin hallaka kansu su na sane? [48]

#: It is not a new question: the ancient Greeks considered it too. [49] <> Wannan ba sabuwar tambaya ba ce: mutanen tsohuwar daular Girkawa ma sun yi nazarinta. [50]

#: Over 2,000 years ago, [51] <> Fiye da shekaru 2,000 da su ka wuce [52]

#: Aristotle cited a stallion that threw himself into an abyss [53] <> Aristotle ya ba da labarin wani doki da ya jefa kansa cikin rami [54]

#: after it became apparent that, like Oedipus, he had unknowingly mated with his own mother. [55] <> bayan da ta bayyana gare shi ya yi jimai da mahaifiyarsa ba tare da saninsa ba. [56]

#: In the 2nd Century AD, [57] <> A cikin karni na biyu na kididdigar Kirista, [58]

#: the Greek scholar Claudius Aelian devoted an entire book to the subject. [59] <> malamin Girkawa Claudius Aelian ya wallafa littafi akan lamarin. [60]

#: He cited 21 apparent animal suicides, [61] <> Ya kawo labarai 21 da dabbobi su ka kashe kansu da kansu da gangan, [62]

#: including a dolphin who let himself be captured, [63] <> ciki har da wani kifindolphinda ya bari aka kama shi da gangan, [64]

#: several instances of hounds starving to death following the passing of their owners, [65] <> da karnuka da dama da su ka hallaka kansu da yunwa bayan mutuwar iyayen gidansu, [66]

#: and an eagle that "sacrificed itself by combustion on the pyre of its dead master". [67] <> da kuma wata mikiyada ta hallaka kanta da wuta lokacin da ake kona gawar uban gidanta”. [68]

#: Just like the "handsome dog" that drowned, the idea of animal suicide remained a popular topic among 19th-Century Victorians. [69] <> A zamanin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria cikin karni na 19 na kididdigar Kirista, [70]

#: One psychiatrist, William Lauder Lindsay, [71] <> wani likitan kwakwalwa, William Lauder Lindsay, [72]

#: attributed "suicidal melancholia" [73] <> ya bayyana bacin rai da bakin ciki [74]

#: to animals of this disposition, describing how they could be "literally goaded into fury and mania" before a suicide. [75] <> a matsayin abubuwan da ke muzgunawa dabbobi har su kai ga hallaka kansu su na sane. [76]

#: At the time, these ideas were seized upon by animal rights groups, [77] <> Nan take kungiyoyin kare hakkin dabbobi a Burtaniya, [78]

#: such as the UK-based Royal Society for the Prevention of Cruelty to Animals (RSPCA). [79] <> irin su RSPCA su ka rungumi wannan fatawar. [80]

#: Animal activists [81] <> Masu kare hakkin dabbobi [82]

#: sought to humanise animal emotions, [83] <> sun yi kokarin kwatanta tunaninsu da na mutane, [84]

#: explains medical historian Duncan Wilson, of the University of Manchester, UK, [85] <> a cewar masanin tarihin aikin likita, Duncan Wilson na jamiar Manchester, a Biritaniya, [86]

#: who looked into historical cases of references to animal suicide in a 2014 research paper. [87] <> wanda ya yi nazari kan labaran da aka bayar a tarihi game da dabbobin da su ka hallaka kansu da gangan, a wani bincike da ya gudanar a 2014. [88]

#: They did so, he says, [89] <> Sun yi hakan ne, a cewarsa, [90]

#: to show animals [91] <> domin nuna dabbobi ma [92]

#: "shared the capacity for self-reflection and intent, [93] <> “na yin tunani da kulla aniya, [94]

#: which included intent to kill themselves out of grief or rage.” [95] <> abinda ya hada da kulla aniyar hallaka kansu sanadiyyar bakin ciki ko bacin rai.” [96]

#: For example, in the 1875 edition of the RSPCA journal Animal World, [97] <> Ga misali, mujallar RSPCA mai suna Duniyar Dabbobi ta 1875 [98]

#: the cover depicted a stag jumping to a suicidal death. [99] <> na dauke ne da hoton wata barewa da ta daka tsalle daga kan tsauni domin ta hallaka kanta. [100]

#: The accompanying editorial stated that [101] <> Sharhin da ya biyo bayan hoton ya ce: [102]

#: "a wild stag, rather than be overtaken by its pursuers, will fall into the jaws of an awful death". [103] <> “wannan barewar, ta zabi ta hallaka kanta, da ta bari mafarauta su cin mata.” [104]

#: However, as medicine advanced in the 20th Century [105] <> Sai dai kuma ci gaban da aka samu a kimiyyar lafiya cikin karni na 20 [106]

#: the human attitude to suicide became more clinical, [107] <> ya sa mutane na kallon kashe kai da kai a matsayin cuta, [108]

#: and these type of "heroic portrays" of suicidal animals dwindled. [109] <> don haka sai labarin gwarazan dabbobi masu hallaka kansu ya fara raguwa. [110]

#: Instead, the focus shifted onto suicide affecting larger populations, [111] <> Sai a ka mai da hankali kan yadda akan samu garken dabbobi sun hallaka kansu, [112]

#: often as a result of social pressure, says Wilson. [113] <> a mafi yawan lokuta sakamakon matsi, a cewar Wilson. [114]

#: Suicide became more of a social malady. [115] <> Sai ake kallon hallaka kai a matsayin wata cuta da kan shafi alumma. [116]

#: Take the examples of the lemmings [117] <> Misali shi ne berayen hamadar kankara da ake kiralemmingda turanci, [118]

#: who apparently march towards cliffs and throw themselves off, [119] <> wadanda kan yi tsalle daga kan tsauni su na dira cikin teku kungiya-kungiya [120]

#: or mass whale strandings. [121] <> ko kuma kifayenwhaleda kan fito gabar teku inda rashin ruwa kan hallaka su. [122]

#: But Wilson did not seek to answer whether animals really do attempt suicide. [123] <> Sai dai binciken Wilson bai yi kokarin gano ko da gaske dabbobi kan yi kokarin hallaka kansu da kansu ba. [124]

#: Instead, his work revealed that changing attitudes to human suicide were reflected in our stories about animals. [125] <> Abinda aikinsa ya bayyana shi ne yadda labarin dabbobi masu hallaka kansu ke sauyawa daidai da yadda mutanen zamanin labarin ke kallon mutanen da ke kashe kansu da kansu. [126]

#: However, another researcher wanted to answer the question head on. [127] <> Amma an samu wani mai binciken da ya yi kokarin samo amsar kai tsaye. [128]

#: Such stories should not fool us, according to Antonio Preti, [129] <> Bai kamata irin wadannan labarai su kidima mu ba, in ji Antonio Preti, [130]

#: a psychiatrist at the University of Cagliari in Italy, [131] <> mai nazarin kwakwalwa a jamiar Cagliari da ke Italy, [132]

#: who scoured the scientific literature on animal suicide. [133] <> wanda ya yi nazari akan littattafan kimiyya na baya da aka wallafa game da dabbobin da aka ce wai su na hallaka kansu da gangan. [134]

#: He looked at about 1,000 studies published over 40 years, [135] <> Ya yi nazarin sakamakon bincike kusan dubu guda da aka wallafa tsawon shekaru 40, [136]

#: and found no evidence of an animal knowingly attempting suicide in the wild. [137] <> amma bai samu hujja ko daya da ke nuna wata dabba a dawa da ta hallaka kanta da gangan ba. [138]

#: Cases such as those in Aelian's book are "anthropomorphic fables", he says. [139] <> A cewarsa, irin labaran da ke cikin littafin Aeliantatsuniyoyi ne kurum”. [140]

#: Researchers now know that the mass deaths of lemmings are an unfortunate consequence of a dense population of creatures emigrating together at the same time. [141] <> Masu bincike a yanzu sun gano cewa berayenlemmingsba hallaka kansu su ke ba, illa dai su kan mutu ne sanadiyyar kokarin yin kaura cikin lokaci guda. [142]

#: In cases where a pet dies following its master's death, [143] <> A lokutan da kuma dabbobin da ke ajiye a gida ke mutuwa bayan mutuwar iyayen gidansu, [144]

#: this can be explained by the disruption of a social tie, says Preti. [145] <> Preti ya ce, warwarewar alakar da su ka saba da ita ce kan jawo musu mutuwa. [146]

#: The animal does not make a conscious decision to die; [147] <> Wato dabbar ba ta kulla kudirin hallaka kanta; [148]

#: instead, the animal was so used to its master that it no longer accepts food from another individual. [149] <> amma, sabonta da uban gidanta kan sa ta ki karbar abinci daga kowa, inda daga karshe sai yunwa ta hallaka ta. [150]

#: This example points to the one important fact. [151] <> Wannan bayani ya nuna wani abu mai muhimmanci; [152]

#: Stress can change the behaviour of an animal in a way that can threaten its life. [153] <> wato damuwa kan sauya dabiar dabba ta yadda za ta iya barazana ga rayuwarta. [154]

#: This happened at SeaWorld's Tenerife park in May 2016. [155] <> Hakan ya faru a dandalin SeaWorld da ke Tenerife a Mayun 2016. [156]

#: A video went viral of a wild-born orca in one of SeaWorld's parks [157] <> An yayata wani hoton bidiyo a intanet wanda ke nuna wani kifinwhale[158]

#: that appeared to beach herself on the side of the tank for about ten minutes. [159] <> wanda ya fito daga kwamin da ake kiwonsa a dandalin SeaWorld tsawon mintuna goma. [160]

#: Dozens of articles appeared stating she had attempted suicide. [161] <> Daga nan fa sai marubuta su ka hau sharhin cewa kifin ya yi kokarin hallaka kansa ne. [162]

#: We know that orcas behave differently in captivity than in the wild, [163] <> Mun san cewa dabiar kifayenwhaleda ke tsare ta bambanta da wadanda ke sake. [164]

#: which is unsurprising given that a tank is a fraction of the size of the ocean. [165] <> Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne kasancewar kwamin da ake ajiye su bai ko kama kafar girman teku ba. [166]

#: Unnatural environments have been known to stress captive orcas, [167] <> A baya dai bincike ya nuna cewa takura kan kuntatawa tsararrun kifayenwhale’, [168]

#: triggering repetitive behaviours such as rubbing the side of their tanks and grinding their teeth. [169] <> ta yadda su kan gogi gefen tankin ko kuma su yi ta cije hakoransu. [170]

#: When it comes down to it, says Barbara King of the College of William & Mary in Virginia, US, [171] <> Abu na farko a cewar Barbara King ta kwalejin William & Mary da ke Virginia, US, [172]

#: it is important to understand just how deeply these animals experience emotions. [173] <> shi ne mu fahimci yadda tunanin irin wadannan dabbobin ya ke [174]

#: This can in turn inform us about what causes them to act in self-destructive ways. [175] <> kafin mu kai ga gano abinda ke sa su sauya ta dabia ta yadda za su iya cutar da kansu. [176]

#: "To my knowledge the vast majority of cases [177] <> “A sanina, mafi yawan lokuta [178]

#: are down to human intervention in some way, whether the result of poaching or confinement," says King, [179] <> wani aikin dan Adam ne ke harzuka su, misali farauta ko tsarewa,” in ji King, [180]

#: who has written extensively about animal grief and suicide. [181] <> wacce ta yi rubuce-rubuce game da bakin ciki da hallaka kai a tsakanin dabbobi. [182]

#: Other animals often cited as attempting suicide are whales that strand in the wild. [183] <> Dabbobin da aka fi ba da misali da su domin nuna cewa dabba kan hallaka kanta da gangan, su ne kifayenwhaleswanda su kan fito gabar teku su kasa numfashi har su mutu. [184]

#: It remains unclear why whales strand. [185] <> Kawo yanzu babu wanda ya san dalilin da ke sa kifayenwhalesfitowa daga teku. [186]

#: One idea is that standings can be caused by a sick individual seeking the safety of shallower water. [187] <> Wasu masanan na ganin abinda ke faruwa shi ne, akan samuwhalemara lafiya ne da kan matso kusa da wurin da ruwa bai da zurfi sosai domin yin jiyya, [188]

#: Because whales form social groups, others follow and strand also. [189] <> amma da yake danginsa su na da zumunci sai su ma su biyo shi. [190]

#: This idea is now called the "sick leader hypothesis". [191] <> Wannan shi ake kiraraayin shugaba mara lafiya[192]

#: But it is not considered suicide. [193] <> amma ba a daukar hakan a matsayin kashe kai da gangan. [194]

#: There are certain parasites that infect the minds of their hosts, [195] <> Baya ga wannan kuma, akwai wasu kananan halittu da kan tare a jikin dabbobi [196]

#: causing mind-altering behaviours that help the parasites thrive. The host often dies in the process. [197] <> su jirkita musu tunani ta yadda su dabbobin za su hallaka, halittun kuma su amfana. [198]

#: For example, the parasite Toxoplasma gondii infects mice and switches off their innate fear of cats. [199] <> Misali, halittar Toxoplasma gondii na kama beraye ta sa su daina tsoron mage. [200]

#: If the cat eats the mouse, the parasite reproduces. [201] <> Idan mage ta cinye beran, sai halittar ta ci gaba da hayayyafa a cikin magen. [202]

#: A 2013 study found that a T. gondii infection permanently deletes this fear, [203] <> Wani bincike a 2013 ya gano cewa T. gondii na hana bera tsoron mage har abada, [204]

#: even after the parasite has been exterminated. [205] <> ko da bayan an raba beran da shi. [206]

#: Similarly, a parasitic fungus called Ophiocordyceps unilateralis can control the minds of ants, turning them into zombies. [207] <> Haka kuma, akwai wata funfuna mai suna Ophiocordyceps unilateralis wacce ke iya juya akalar tururuwai. [208]

#: It steers the insects to their deaths in locations where the fungus can thrive. [209] <> Ta kan sa tururuwan su hallaka kansu a wurare masu danshi, inda funfunar za ta rayu. [210]

#: Lastly, mother spiders let their young eat them. [211] <> Bugu da kari, matan gizo-gizo kan bariyayansu su cinye su. [212]

#: Though they die in the process, [213] <> Koda yake su kan mutu sanadiyyar hakan, [214]

#: this sacrifice is not suicide, [215] <> wannan sadaukarwa ce ba hallaka kai da gangan ba, [216]

#: but rather an extreme act of parental care. [217] <> domin kuwa wannan na nuna tsananin kaunar da uwar ke yi wayayanta. [218]

#: The mother spiders provide their own bodies as a vital first nutritious meal that ensures their offspring's survival. [219] <> Mata kan ciyar dayayansu jikinsu ne domin ba su sinadiran da za su taimaka musu a rayuwa. [220]

#: To say such behaviour does not constitute suicide requires a definition of what does. [221] <> Cewar ba za a kira wannan dabiar hallaka kai da gangan ba, na bukatar mu bayyana me ake nufi da hallaka kai da gangan. [222]

#: Suicide is commonly defined as "the action of killing oneself intentionally". [223] <> Shi dai ana daukarsa ne a matsayinkashe kanka da kanka bisa niyyar yin hakan”. [224]

#: We know that some animals kill themselves. [225] <> Mun san cewa wasu dabbobin su kan kashe kansu. [226]

#: The question is whether they intend to. [227] <> Tambayar ita ce; da niyya su ke hakan? [228]

#: The mother spider, for example, may behave this way to primarily provide food, not die. [229] <> Misali matar gizo-gizo na iya yin haka ne don ciyar da iyalinta ba don ta mutu ba. [230]

#: Some experts believe this question is impossible to answer. [231] <> Zancen gaskiya shi ne, kawo yanzu ilimin dan Adam bai kai yadda zai iya gane tunanin dabba ba, a cewar King. [232]

#: But others disagree. [233] <> Sai dai wasu masanan ba su yadda da bayaninta ba. [234]

#: They say some people intend to kill themselves, while animals do not, due to differences in cognitive ability. The key difference, they say, is our ability to think far into the future. [235] <> Sun ce dabbobi ba za su iya kashe kansu da gangan ba saboda kwakwalwarsu ba ta kai ta yi tunanin halin da suke ciki a duniya tare da neman mafita ta hanyar mutuwa ba. [236]

#: "Humans have a capacity to imagine scenarios, reflect on them, and embed them into larger narratives," [237] <> Thomas Suddendorf, masanin dabiun halittu a jamiar Queensland da ke Australia, ya ce [238]

#: says Thomas Suddendorf, an evolutionary psychologist at the University of Queensland in Australia. [239] <> “akwai bambanci mai nisa tsakanin tunanin mutane da na dabbobi: mu mu kan tada hankali kan abinda mu ke hasashen zai iya faruwa amma su ba sa yi.” [240]

#: Depressed people truly appreciate reality, agrees Ajit Varki of the University of California, San Diego, US, who has written extensively about human uniqueness and our ability to deny death. [241] <> Ajit Varki, na jamiar California da ke San Diego ya goyi bayansa, inda ya ce: “Mutane sun san mutuwa amma dabbobi ba su santa ba. [242]

#: "What is suicide?" asks Varki. [243] <> “Menene ma kashe kai da kai?” in ji Varki. [244]

#: "It is inducing your own mortality, [245] <> “Shi ne ka jawo sanadin mutuwarka da kanka, [246]

#: but how can you induce it if you don't know you have mortality? [247] <> amma ta yaya za ka yi haka idan ba ka san za ka iya mutuwa ba? [248]

#: It's [[[therefore]]] quite logical that suicide should be uniquely human." [249] <> Don haka babu wanda zai iya kashe kansa da gangan sai mutum.” [250]

Contents