Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Recent additions to the category

Central Theme of Suratul Yaseen <> Babban Jigon Surar

Quranic Diagrammatic Overviews QDO of 36 Yaseen
Quranic Diagrammatic Overviews QDO of 36 Yaseen

Acknowledge the inability of those other than Allah, and accept the ability, power and authority of Allah and accept Muhammad as His messenger, the Quran and the akhirah.


Bayanin ƙarfafan dalilai masu tabbatar da manzanci da kuma tashi bayan mutuwa.

Introduction to the Sura <> Mabuɗin Surar:

36 Yaseen Hausa Tafsir
36 Yaseen Hausa Tafsir
  1. Sunanta: Ana kiran ta da suna Suratu* Yasin, watau da haruffan farko na cikinta. *Not sure if Suratu was a typo.
    Its name: It goes by the name Suratul Yaseen, that is the first (2) letters of the sura. The Surah takes its name from the two letters of the alphabet with which it begins.
  2. Sanda aka saukar da ita (time period of revelation): Malamai sun haɗu a kan cewa Sura ce Makkiyya kamar yadda Ibni Aɗiyya ya ambata a tafsirinsa.
    A study of the style shows that it was either sent down during the last stage of the middle Makkan period, or it is one of those Surahs, which were sent down during the last stage of the Holy Prophet's stay at Makkah.
  3. Jerin Saukarwa: ita ce Sura ta arba'in da ɗaya (41) a jerin saukar surorin Alƙur'ani. Ta sauka bayan Suratul Jinni gabanin Suratul Furƙan.
  4. Adadin ayoyinta: Adadin ayoyinta tamanin da uku (83) a lissafin mutanen Kufa. Amma a lissafin sauran malamai, adadinta tamanin da biyu ne (82).
  5. Falalarta: Babu wani hadisi na Manzon Allah SAW da ya inganta game da falalarta.
  6. Babban Jigonta (kalli sama <> see central theme above): Bayanin ƙarfafan dalilai masu tabbatar da manzanci da kuma tashi bayan mutuwa.
  7. Daga cikin abubuwan da ta ƙunsa akwai:
    1. Nuna girman Alƙur'ani da gaskiyarsa da gaskiyar saƙon da ya zo da shi don ceton al'ummar Larabawa wadanda ba a aiko musu da wani manzo a baya ba.
    2. Bayanin siffofin wadanda suka bijire wa Musulunci suka ƙi amfana da shiriyarsa sabanin mumunai masu tsoron Allah wadanda suka bi tafarki madaidaici.
    3. Kwatanta bangaren muminai wadanda suka gaskata Manzon Allah SAW da kuma bangaren kafirai masu ƙartaya shi, kwatanta su da mutanen alƙarya wadanda suka ƙaryara manzonsu da bayanin bangarorin biyu.