Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/026 chinese status symbol

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: Western manners: The latest Chinese status symbol [1] <> Dabiun Turawa sun zama abin alfahari a China [2]

#: Five Chinese women are sitting upright in their chairs, [3] <> Wasu matayan China ne zaune reras kan kujeru, [4]

#: designer handbags at their heels, [5] <> kayatattun jakunkunansu na ajiye daura da kafafuwansu, [6]

#: listening attentively to a trendy Chinese Tatler magazine photographer [7] <> su na sauraron wani mai daukar hoto a mujallar Tatler ta kasar China, cikin nutsuwa [8]

#: describing how to pose in public. [9] <> ya na wassafa musu yadda ake bayyana cikin jamaa. [10]

#: He is talking makeup, [11] <> Ya na musu bayani game da kwalliya [12]

#: light and cheekbones. [13] <> da haskaka kundukuki. [14]

#: The room is decorated with Pierre Frey wallpaper [15] <> Dakin ya sha kwalliya da takardar kawata bango ta Pierre Frey, [16]

#: and the participants sip tea out of a Bernardaud tea set. [17] <> yayinda matan ke shan shayi daga kofin tangaran na Bernardaud. [18]

#: Notepad in hand, they are learning the dos and donts of camera etiquette. [19] <> Su na rike da takardu, su na daukar darasi kan yadda ake zaman daukar hoto. [20]

#: The course entitled [21] <> Darasin mai taken [22]

#: How to pose elegantly in front of the camera[23] <> “Yadda ake zaman daukar hoton hamshakai[24]

#: is one of many offered by Institute Sarita, [25] <> na daya daga cikin darussan da ake koyarwa a cibiyar Sarita, [26]

#: a modern-day version of European finishing schools that caters to Chinese nouveaux riche. [27] <> wata makarantar koyar da tarbiyyar Turai da ke horar da sababbin masu kudi na kasar China. [28]

#: Other courses offered by the school, located in the trendy Sanlitun district of Beijing, [29] <> Sauran darussan da makarantar da ke unguwaryan gayu ta Sanlitun da ke Beijing, [30]

#: include how to raise children, [31] <> sun hada da yadda ake rainon yara, tarbiyyar cin abinci, [32]

#: proper table manners and luxury brand pronunciation. [33] <> da yadda ake furta sunayen kayayyakin kasaita. [34]

#: Most of my clients had an embarrassing moment, overseas [35] <> “Mafi yawan dalibaina sun yi abin kunya ne a kasashen waje [36]

#: or during a business dinner. [37] <> ko kuma wurin liyafar kasuwanci. [38]

#: They come here because they want to make thing easier for themselves,” said Sara-Jane Ho, [39] <> Su kan zo nan ne domin saukaka wa kansu jin kunya,” in ji Sara-Jane Ho, [40]

#: the perfectly groomed school founder, as she sat in a drawing room furnished with imported French antique furniture. [41] <> wacce ta kafa makarantar, a yayin da take zaune cikin dakin da aka kawata shi da tsofaffin kujerun alfarma na Faransa. [42]

#: Its mostly learning about how to behave in an international environment,” said Ho, [43] <> “Yawanci mu na koyar da yadda ake muamala ne a kasashen waje,” in ji Ho, [44]

#: who herself studied etiquette at the Institut Villa Pierrefeu in Switzerland, [45] <> wacce ta yi karatun tarbiyya a Institut Villa Pierrefeu da ke Switzerland, [46]

#: one of the last proper finishing schools in the world. [47] <> daya daga cikin makarantar horar dayan mata tarbiyyar hamshakai da su ka rage a duniya. [48]

#: So far [49] <> Kawo yanzu dai [50]

#: she has attracted a couple hundred wealthy Chinese to her courses. [51] <> ta samu daruruwan masu kudin China da ke halartar makarantarta. [52]

#: She is opening a Shanghai branch in May. [53] <> A nan gaba kadan za ta bude reshe a birnin Shanghai. [54]

#: With 190 billionaires and more than two million millionaires, [55] <> Kasar China dai na da hamshakan masu arzikin da dukiyarsu ta zarta dala biliyan guda har su 190, [56]

#: China tags just behind the US in number of high-net-worth individuals, [57] <> kuma ta na da miloniyoyi fiye da dari biyu, inda ta ke matsayi na biyu a bayan Amurka, a jerin kasashe masu yawan masu kudin gaske, [58]

#: according to research from Forbes magazine and Boston Consulting Group. [59] <> a cewar wani bincike da mujallar Forbes da kamfanin Boston Consulting Group su ka gudanar. [60]

#: Many of these fortunes have grown rapidly, [61] <> Mafi yawan masu kudin sun yi arziki cikin dan kankanin lokaci [62]

#: in lock-step with Chinas newly expanding economy and multiplying business opportunities. [63] <> daidai da bunkasar tattalin arzikin China da yawaitar hanyoyin samun kudi. [64]

#: Some who find themselves newly wealthy [65] <> Wasu daga cikin sababbin masu kudin nan [66]

#: have little knowledge or training in how to behave in international business or social events. [67] <> na da karancin sanin yadda ya kamata su yi hulda dayan kasashen waje a harkokin kasuwanci ko muamalar rayuwa. [68]

#: "The country was so isolated 30 years ago," said Ho. [69] <> “Shekaru 30 da su ka wuce kasar China a ware take,” in ji Ho. [70]

#: "The spike in wealth has happened in a compressed time. [71] <> “Bunkasar tattalin arziki ya zo mata na kamar kiftawa da bisimilla. [72]

#: This transformation has created a lot of pressure on individuals." [73] <> Don haka sauyin ya janyo takura da yawa akan mutane.” [74]

#: As a result, [75] <> Sakamakon haka, [76]

#: some businesspeople may appear uncouth and blunt to their western or Asian counterparts. [77] <> wasuyan kasuwar ba su da kyawawan dabiu wurin hulda da Turawa ko ma takwarorinsu na nahiyar Asiya. [78]

#: Finesse, on the other hand, can smooth many business transactions. [79] <> Yayinda kyakkyawar muamala kan sa a samu nasara a harkokin kasuwanci. [80]

#: Simply knowing how to be comfortable with a knife and fork can be a deal clincher,” said James Hebbert, [81] <> “Sanin yadda ake amfani da wuka da cokali mai yatsu wurin cin abinci na da tasiri wurin kulla huldar kasuwanci,” in ji James Hebbert, [82]

#: who represents Seatton, a British etiquette school in China. [83] <> wakilin makarantar koyar da halaye na gari ta Burtaniya, Seatton, a China. [84]

#: Filling a niche [85] <> Cike gibi [86]

#: Clients who attend etiquette courses in China include government officials, [87] <> Daliban makarantun koyar da tarbiyya a China sun hada da jamian gwamnati, [88]

#: children enrolled in overseas schools, [89] <> yaran da su ke karatu a makarantun kasashen ketare, [90]

#: wives looking to entertain important guests and those who enjoy travelling abroad. [91] <> matan auren da ke saukar manyan baki, da kuma mutanen da ke tafiye-tafiye a kasashen duniya. [92]

#: There is a huge demand all along the spectrum,” said Hebbert, [93] <> “A na matukar bukatar wadannan darussa a kowanne mataki na alummar China,” in ji Hebbert, [94]

#: whose clients were first primarily drivers of Rolls Royces wanting to dress the part, [95] <> wanda dalibansa na farko direbobin motocin Rolls Royce ne da su ke son shigarsu ta dace da motocin, [96]

#: then evolved to middle-class customers in search of a British-lifestyle experience. [97] <> daga baya kuma sai masu kudi su ka fara zuwa domin su koyi dabioin mutanen Burtaniya. [98]

#: In just a few years, I have seen a real shift in clientele. [99] <> “A cikin shekaru kalilan, na ga sauyi a irin daliban da su ke zuwa nan. [100]

#: More and more Chinese are travelling. [101] <> ‘Yan China da dama na fita kasashen waje. [102]

#: They see the advantage of having an international edge.” [103] <> Sun fahimci amfanin sanin dabiun abokan huldarsu.” [104]

#: If learning how to peel an orange with a knife and fork may seem slightly superfluous in Europe, [105] <> Idan koyon yadda ake feraye lemo da wuka ba wani muhimmin abu ba ne a Turai, [106]

#: in China the newly rich are ready to pay what it takes to acquire the manners that come with their new status. [107] <> a China sababbin masu kudi a shirye su ke da su biya duk abinda ya kama don su koyi dabiun da su ka dace da sabon matsayinsu a rayuwa. [108]

#: The next time I visit Milan and dine in a nice restaurant I can confidently tell my husband he shouldnt hold his knife like a dagger,” [109] <> “Idan na sake komawa Milan mu ka je cin abinci, zan iya gaya wa mijina ya daina rike wukarsa kamar ya rike takobi,” [110]

#: said a participant of a two-hour Western dining etiquette course with James Hebbert in Shanghai, who didn't want her name used. [111] <> in ji wata dalibar darasin tsarin cin abinci na kasashen Yamma wanda James Hebbert ke gudanarwa a Shanghai. [112]

#: Hebbert charges 20,000 yuan ($3,243) per group of 10 for an afternoon session. [113] <> Hebbert na cajin yuan 20,000 (3,243) a darasi guda ga rukunin dalibai 10 domin daukar darasi da yamma. [114]

#: Institute Saritas most popular course, “Hostessing”, [115] <> Darasin da aka fi rububinsan a cibiyar Saritasaukar baki,’ [116]

#: costs 100,000 yuan ($16,216) for 12 days [117] <> akan biya yuan 100,000 ($16,216) a tsawon kwanaki 12, [118]

#: in which the client learns skills ranging from engaging in small talk [119] <> inda dalibai kan koyi darussan da su ka danganci yadda ake hira [120]

#: to pairing wines with a meal. [121] <> da kuma giyar da ta dace da kowanne nauin abinci. [122]

#: Lack of manners [123] <> Rashin tarbiyya [124]

#: Media and even the Chinese president have been critical of how some Chinese travellers have behaved on trips. [125] <> Kafafen yada labari da ma shugaban kasar China sun sha sukan irin dabiun da wasuyan China ke yi a kasashen waje. [126]

#: On a September trip to the Maldives, [127] <> A wata ziyara da ya kai kasar Maldives a watan Satumba, [128]

#: Chinese President Xi Jinping suggested Chinese citizens be [129] <> shugaban kasar China Xi Jinping ya shawarciyan kasar da [130]

#: a bit more civilised when travelling abroad.” [131] <> “su nuna wayewa a lokacin da su ka tafiye-tafiye a kasashen waje.” [132]

#: With more than 100 million Chinese travelling in 2014, [133] <> Fiye dayan China miliyan 100 ne su ka fita kasashen ketare a 2014, [134]

#: misbehaviours have grabbed headlines worldwide. [135] <> kuma rashin tarbiyyarsu ya yi shuhra a kafafen yada labarai. [136]

#: Among the most extreme: [137] <> Daga cikinsu akwai: [138]

#: defacing an Egyptian sculpture, [139] <> bata fuskar wani gunki a Masar, [140]

#: throwing boiling water on a flight attendant [141] <> zuba wa maaikaciyar jirgi ruwan zafi [142]

#: and urinating outside. [143] <> da kuma yin fitsari a waje. [144]

#: In October, Chinas National Tourism Administration issued strict guidelines on how to behave while travelling. [145] <> A watan Oktoban da ya gabata, hukumar yawon bude ido ta China ta gargardi matafiya da su nuna kyakkyawar tarbiyya a waje. [146]

#: In a 64-page booklet, Chinese tourists are warned against peeing in swimming pools, [147] <> A cikin wani littafi mai shafi 64, hukumar ta gargadiyan China masu fita waje da su guji yin fitsari a kwamin wanka, [148]

#: stealing life jackets from planes [149] <> satar lemar dira daga jirgi, [150]

#: and leaving footprints on the toilet seat. [151] <> ko tsugunawa kan masan tangaran da kafafunsu. [152]

#: Punishments for such behaviours include fining tour operators and [153] <> Daga cikin hukunce-hukuncen da aka tanadawa ma su irin wadannan dabiu har da cin tarar kamfanonin da su ka shirya tafiyar da kuma [154]

#: blacklisting rude tourists. [155] <> haramtawa mara sa tarbiyya sake fita daga kasar. [156]

#: The Chinese have no manners. [157] <> “Mutanen China ba su da tarbiyya. [158]

#: Its just not something that is taught by parents. [159] <> Iyayensu ba sa koya mu su kyautata muamala. [160]

#: I am always surprised when men hold the door for me in Paris. [161] <> Na kan yi mamaki duk san da maza su ka bude min kofa a birnin Paris. [162]

#: This would never happen in China,” [163] <> Wannan ba zai taba yiwuwa a China ba,” [164]

#: said Yue-Sai Kan, a Sino-American TV host and producer, [165] <> in ji Yue-Sai Kan, wata baamurkiyayar asalin China mai shiryawa da gabatar da shirye-shiryen talabijin, [166]

#: and author of Etiquette for the Modern Chinese, [167] <> kuma marubuciyar littafin koyar da tarbiyya, [168]

#: a national bestseller that has sold more than three million copies. [169] <> wanda aka sayar da fiye da kwafe miliyan uku kawo yanzu. [170]

#: Today, Kan lectures on etiquette [171] <> Kan ta na gabatar da lacca akan kyawawan dabiu [172]

#: and trains Chinese contestants for the Miss Universe contest. [173] <> kuma ita ke horar dayan matan China da ke shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya. [174]

#: While some of what is perceived as [175] <> Yayinda wasu dabiun da Turawa kan dauka [176]

#: rude by Westerners stems from cultural issuesthe notion of public space and privacy is very different in China[177] <> rashin mutunci ne sun samo tushe ne daga bambancin alada, [178]

#: other ill-manners date back to the Cultural Revolution [179] <> wasu kuma na da alaka ne da zamanin juyin-juya-halin aladu na zamanin mulkin gurguzu, [180]

#: when all that was seen as sophistication was considered bourgeois and severely punished. [181] <> inda ake daukar duk wata dabia da ke nuna alamun wayewa a matsayin tayan jari-hujja don haka ake yin hukunci mai tsanani. [182]

#: Lets say that when youre struggling to get food [183] <> “Idan ka na gwagwarmayar neman abinda za ka sa a baki, [184]

#: you are not thinking about private space,” Ho explained. [185] <> ba ka cika tunanin kyautatawa wasu ba,” a cewar Ho. [186]

#: What can seem to an outsider as impolite todaysuch as pushing, queue barging, speaking loudly or picking your nose in publicis common behaviour for the majority of Chinese. [187] <> Wasu abubuwa da ke kama da rashin tarbiyya a idon bakiirin su turareniya, datsen layi, magana da karfi ko kwakule hanci a bainar jamaahalayyar yau da kullum ce ga mafi yawanyan China. [188]

#: But as China opens up and engages with the world [189] <> Sai dai a yayin da China ke kara hulda da sauran kasashen duniya, [190]

#: awareness is growing among the population on how they are being perceived overseas. [191] <> a hankaliyan kasar sun fara fahimtar irin kallon da ake musu a kasashen ketare. [192]

#: A new face [193] <> Sabon salo [194]

#: To disassociate themselves from this reputation, [195] <> Domin nisanta kansu daga wannan kaurin sunan, [196]

#: many of the new elite are seeking refinement at etiquette schools. [197] <> da yawa daga cikin sababbin masu kudin na kokarin kyautata dabiunsa a makarantun tarbiyya. [198]

#: At the same time, they are looking to good manners as a new form of status symbol. [199] <> Haka kuma su na kallon kyawawan dabiu a matsayin alamar wayewa. [200]

#: “[[[The]] Chinese] understand that [201] <> “Mutanen China sun fahimci cewa [202]

#: their position as the most powerful country in the world [203] <> matsayinsu na kasar da tafi kowacce karfi a duniya [204]

#: puts them in a situation where they need to learn about other cultures and behaviours so as to smoothen political and business relationships,” [205] <> ya sa su a wani hali da zasu bukaci sanin aladu da dabiun da za su kyautata alakarsu ta siyasa da kasuwanci,” [206]

#: said Viviane Neri, principal of Institut Villa Pierrefeu, in an email. [207] <> in ji Viviane Neri, shugabar makarantar Institut Villa Pierrefeu. [208]

#: Before, it was about owning a big car,” said Hebbert. [209] <> “A da, mallakar mota shi ne abin birgewa,” in ji Hebbert. [210]

#: Now the rich are looking for something else to make the difference.” [211] <> “Yanzu masu kudi na neman wani abun dabam da za su bambance kansu da talakawa.” [212]

Contents