Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/2/Rijayar Lemo Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 22:19, 15 May 2025 by Admin (talk | contribs)
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Baqara 1-5

  1. Alif Lam Mim. --Quran/2/1
  2. Wannan littafi ne da babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taqawa. --Quran/2/2
    • This is the Book about which there is no doubt in it! It's a guide/guidance for those mindful of Allah. (See also Quran/1/6, Quran/19/76, Quran/guidance)
    • dhālika l-kitābu lā rayba fīhi hudan lil'muttaqīn
  3. Wadanda suke yin imani da gaibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi. --Quran/2/3
    • Who believe in the unseen, establish prayer, and donate / spend out of what We have provided for them
    • alladhīna yu'minūna bil-ghaybi wayuqīmūna l-ṣalata wamimmā razaqnāhum yunfiqūn
  4. Wadanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira. --Quran/2/4
    • And who believe in what has been revealed to you, [O Muhammad], and what was revealed before you, and of the Hereafter they are certain [in faith]
    • and who believe in what has been revealed to you ˹O Prophet˺ and what was revealed before you, and have sure faith in the Hereafter.
    • wa-alladhīna yu'minūna bimā unzila ilayka wamā unzila min qablika wabil-ākhirati hum yūqinūn (yaƙini)
  5. Wadannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu samun babban rabo. --Quran/2/5
    • Those are upon [right] guidance from their Lord, and it is those who are the successful
    • It is they who are ˹truly˺ guided by their Lord, and it is they who will be successful.
    • ulāika ʿalā hudan min rabbihim wa-ulāika humu l-muf'liḥūn

Tafsiri:

Allah swt ya bud'e wannan Sura da harufin Alif da Lam da Mim.
Allah Almighty opened this Surah with the letters Alif, Lam and Mim.

Ban da ita wannan Sura da akwai surorin Alqur'ani da dama da Allah ya bud'e su da irin wadannan haruffa.
Apart from this Surah, there are many other Surahs of the Quran that Allah opened with similar letters.

Da dama daga cikin malamai suna cewa, Allah ne kad'ai ya san abin da yake nufi da su
Many scholars say that only Allah knows the meaning of these disjointed letters.

Wasu kuma sun yi qoqarin bayyana ma'anoninsu.
Others have tried to explain their meanings.

Amma magana mafi inganci ita ce, Allah yana nuna mu'ujizar AlQur'ani ne ta hanyar ambaton wadannan haruffa.
But the most correct statement is that Allah is showing the miracle of the Quran by mentioning these letters.

Domin suna tabbatar wa larabawa cewa babu wanda zai iya kawo wani abu irin Alqur'ani,
Because they are proving to the Arabs that no one can bring anything like the Quran,

duk kuwa da cewa haruffansa su ne haruffan da suke magana da rubutu da su.
even though its letters are the (same) letters with which they speak and write.

Allah ya siffanta wannan Alqur'ani da cewa, babu wani kokwanto a cikinsa,

  • Allah describes this Quran as having no doubt in it,

wato duk abin da ya qunsa tabbatacce ne kuma gaskiya ne,

  • that is, everything it contains is certain and true,

don haka ne ya zama shiriya ga masu taqwa,

yana nuna musu gaskiya da bayyana musu hukunce-hukunce wad'anda suka shafi aqidunsu da ibadunsu da kuma mu'amalolinsu.

  • showing them the truth and explaining to them the rulings that affect their beliefs, their worship, and their dealings.

An kira Alqur'ani da sunan Littafi duk kuwa da kasancewarsa ba a tattara shi wuri guda ba a lokacin;

  • The Quran was called the Book, even though it was not collected in one place at the time;

an yi haka ne domin a yi ishara zuwa ga cewa, nan gaba za a tattara shi wuri guda ya zama littafi wanda Musulmi a kowane lokaci za su riqa karantawa.

  • This was done to indicate that in the future it would be collected in one place and it will become a book that Muslims would read at all times.

Sannan Allah swt yana fayyace siffofin masu taqwa wadanda Alqur'ani yake shiryar da su.

  • Then Allah (swt) describes the characteristics of the pious people whom the Quran guides.

Sun siffantu da siffofi guda biyar kamar haka: <> They are described with five characteristics as follows:

  1. Suna yin imani da gaibu. Gaibu shi ne duk abin da manzanni suka zo da shi, suka ba da labarinsa, kuma ido bai gan shi ba. Wannan ya had'a da imani da ranar lahira da abin da ta ƙunsa na hisabi da mala'iku da labarin manzanni da littafan da Allah ya saukar gabanin zuwan Manzon Allah swt. Imani da gaibu shi ne yake bambance wa tsakanin mutum mumini da kafiri, saboda yana imani da duk wani abu da Allah ya ba da labarinsa ko Manzonsa ya fad'a ko da kuwa bai gano shi da hankalinsa ba.
    • They believe in the unseen. The unseen is everything that the messengers brought, reported, and the eye has not seen. This includes belief in the Day of Judgment and what it entails, the angels, the stories of the prophets, and the books that Allah revealed before the coming of the Messenger of Allah (swt). Belief in the unseen is what distinguishes a believer from a disbeliever, because he believes in everything that Allah has reported or His Messenger has said, even if he does not understand it with his own mind.
  2. Suna tsayar da salla, wato suna yin ta kamar yadda shari'a ta koyar da su tare da kula da lokutanta da rukunanta da wajibanta da sharuɗɗanta.
  3. Suna ciyar da abin da Allah ya azurta su da shi. Sukan fitar da zakkar dukiyoyinsu, hakanan suna sadaka ta nafila da abin da Allah ya hore musu.
    • They spend what Allah has provided for them. They pay the Zakat on their wealth, and they give voluntary charity with what Allah has given them. --Talk:Quran/2/3
  4. Su ne waɗanda suke yin imani da Alƙur'anin da Allah ya saukar wa Annabi Muhammadu (SAW) gaba ɗaya
    They are those who believe in the Quran that Allah revealed to the Prophet Muhammad (PBUH) in its entirety,

    ba tare da ware ɓangare ko sun riƙa tawilin karkatar da ma'anonin wani ɓangare na Alƙur'ani ba,
    without excluding any part or interpreting the meanings of any part of the Quran,

    kamar yadda 'yan bidi'a suke yi ga wasu ayoyin waɗanda ba sa goyon bayan bidi'o'insu da aƙidunsu. Hakanan suna yin imani da dukkan littattafan da Allah ya saukar wa manzanni da annabawan da suka gabata, har da su kansu manzannin da annabawan.
  5. Su ne waɗanda suka tabbatar da zuwan ranar tashin alƙiyama da abubuwan da za ta zo da su na tayar da matattu da yi musu hisabi da suka wa mutanen ƙwarai da Aljanna; masu miyagun laifuffuka kuwa a saka musu da wutar Jahannama. An ware batun imani da ranar lahira duk kuwa da cewa ya shiga cikin batun imani da gaibu, saboda a zaburar da mutane ga ayyukan alheri a kuma tsoratar da su game da munanan ayyuka.

Sannan Allah swt ya faɗi sakamakon masu waɗannan siffofi da cewa, suna kan wata shiriya mai girma daga Allah mai yi musu tarbiya ta ƙwarai. Domin babu wata shiriya da ta kai siffantuwa da waɗannan siffofi. Don haka su ne waɗannan suke da babban rabo daga Allah, wato samun yardar Allah da gidan Aljanna ranar gobe alƙiyama.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Girman mu'ujizar Alƙur'ani.
  2. Allah swt ya yi ishara zuwa ga cewa, za a tattara Alƙur'ani wuri guda don ya zama littafin da Musulmi za su riƙa ɗauka suna karantawa a kowane zamani.
    • Allah (swt) has indicated that the Quran will be collected in one place so that it will be a book that Muslims will carry and read at any point in time.
  3. Alƙur'ani shiriya ne ga mutane masu taqwa. Watau masu kiyaye dokokin Allah. Gwargwadon taƙawar bawa gwargwadon yadda zai dace da shiriyar Alqur'ani. Wanda kuma ya rungume shi yana aiki da shi to babu shakka shiriyarsa za ta riƙa hauhawa tana ƙaruwa.
    • The Quran is a guidance for the pious. That is, those who observe the laws of Allah. The measure of a servant's piety is as much as it is in accordance with the guidance of the Quran. And whoever embraces it and acts upon it, then undoubtedly his guidance will continue to increase and increase. (See also Quran/19/76)
  4. Duk abin da Alqur'ani ya qunsa gaskiya ne babu kokwanto ko kad'an a cikinsa.
  5. Falalar yin imani da gaibu, domin shi ne abin da yake buqatar qarfin imani, sab'anin abin da kowa yake iya gani ko yake iya ji, wannan abu ne da babu mai iya musanta samuwarsa.
    • The virtue of believing in the unseen, because it is something that requires strong faith, as opposed to something that everyone can see or hear. This is something that no one can deny its existence.
  6. Girman sha'anin tsai da salla, domin ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan Musulunci.
    • The importance of establishing prayer, because it is the second of the pillars of Islam.
  7. Falalar ciyar da dukiya don Allah. <> The virtue of giving zakat and donating sadaqa for Allah's sake.
  8. Siffar masu taqawa ta ƙunshi bauta wa mahalicci ba kyautata wa mahluki.
  9. Imani da duk littattafan da Allah swt ya saukar wa manzanninsa, domin sanin cewa Allah swt bai bar bayinsa hakanan sakaka ba tare da bayyana musu hanyar shiriya ba.
  10. Shiriya da rabauta ba za su taɓa samuwa ga bawa ba sai ya rungumi wannan hanyar, ya siffantu da waɗannan siffofi.

Baqara 6-7

  1. Lalle waɗanda suka kafirta, duk ɗaya ne a gare su, ka yi musu gargaɗi ko ba ka yi musu ba, ba za su yi imani ba. --Quran/2/6
  2. Allah Ya toshe zukatansu da jinsu, kuma akwai wani lulluɓi a kan idanunsu, kuma suna da azaba mai girma. --Quran/2/7

Tafsiri:

A nan Allah yana ba da labarin kafirai ne da irin taurin kansu wajen kafirce wa abin da Annabi SAW ya zo da shi na gaskiya.

  • Here, Allah is telling the story of the disbelievers and their stubbornness in rejecting what the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) brought as truth.

Allah ya faɗa wa Annabi (SAW) cewa, waɗannan kafirai sun kai matuƙa ga kafircinsu; yana da wuya wa'azinsa ya sa su saurare shi, har su yi imani, don haka kada kafircinsu ya dame shi.

  • Allah told the Prophet (PBUH) that these disbelievers had reached the extreme of their disbelief; it was difficult for his preaching to make them listen to him and believe, so he should not be troubled by their disbelief.

Domin Allah ya riga ya toshe musu zukatansu saboda zunubbansu, don haka imani ba zai sami hanyar shiga cikinsu ba.

  • Because God has already sealed their hearts because of their sins, faith will not find its way into them.

Kuma ya doɗe musu kunnuwansu saboda kafircinsu, don haka ba za su taɓa jin kiransa ba balle su amsa masa.

  • And He has deafened their ears because of their disbelief, so they will never hear his call, let alone respond to it.

Sannan akwai yanar da ta rufe musu idanuwansu ta yadda ba za su taɓa ganin gaskiya ba balle su yarda da ita.

  • And then there is a web/barrier that has blinded their eyes so that they will never see the truth, let alone believe it.

Saboda haka suka cancanci azaba mai girman gaske. <> Thus why they deserve a great punishment.

Wannan yana nuna cewa, kafirci idan ya yi yawa a tare da bawa yakan toshe masa dukkan ƙofofin samun shiriya,

  • This shows that, when disbelief becomes too much in a person, it blocks all the doors to guidance.

duk kuwa yadda aka yi fama da shi ba zai taɓa karɓar gaskiya ba, don ba ya jin ta, ba ya ganin ta kuma ba ya fahimtar ta saboda tsatsar zunubi da kafirci da suka lulluɓe shi.

no matter how people struggle with him, he will never accept the truth, because he does not hear it, see it, or understand it due to the sheer sins and unbelief that have enveloped him.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Lallashin Annabi SAW da nuna masa kada damuwa ta hallaka shi saboda ganin mutanensa sun ƙi yin imani da gaskiyar da yake kiran su zuwa gare ta.
  2. Idan mai kira zuwa ga Allah SWT ya bayyana wa mutane gaskiya suka bijre masa, to wannan ba zai cutar da shi komai ba, domin shi ya sauke nayin da yake kansa.
  3. Annabi ko waninsa babu wanda ya san abin da Allah ya riga ya rubuta wa wadanda ake kira na shiryuwarsu ko ɓatansu, Allah ne kaɗai ya san haka.
  4. Tsananin haɗarin girman kai da bijire wa gaskiya da dogewa a kan kafirci, domin yin haka yakan toshe zukata har ya zamanto duk wani alheri ba ya ratsa su.

Baqara 8-10

  1. A cikin mutane kuma akwai wadanda suke cewa: "Mun yi imani da Allah kuma mun yi imani da ranar lahira," alhalin su ba muminai ne ba. --Quran/2/8
  2. Suna ganin suna yaudarar Allah ne da wadanda suka yi imani, amma kuwa ba kowa suke yaudara ba sai kawunansu, kuma su ba sa jin hakan. --Quran/2/9
  3. Akwai wata cuta (ta munafunci) a cikin zukatansu, sai Allah Ya ƙara musu wata cutar, kuma suna da wata azaba mai raɗaɗi saboda ƙaryar da suke yi. --Quran/2/10

Tafsiri:

Daga nan har zuwa aya ta 20 Allah SWT yana mana bayanin munafuƙai ne tare da fallasa su da bankaɗo munanan siffofinsu don kowa ya gane su a kowane lokaci a kuma kowane yanayi.

A lokacin da Annabi SAW yana zaune a Makka mutane kashi 2 ne: muminai sai kafirai. To amma bayan Musulmai sun yi hijira zuwa Madina, sai aka samu kashi na uku, su ne munafuƙai. Munafiki shi ne wanda yake bayyana Musulunci a bakinsa, amma yana ɓoye kafirci a zuciyarsa. Allah ya bayyana wasu siffofinsu a nan.

Yana daga cikin siffofinsu suka riƙa bayyana imani da baki amma suna ɓoye kafirci a zukatansu, shi ya sa Allah ya ce: "Waɗannan ba muminai ne ba." Kuma saboda wautarsu suna yin haka ne wai don a zatonsu suna yaudarar Allah ne tare da muminai, watau a tsammaninsu Allah bai san abin da suke ɓoyewa ba. Wannan ta sa idan yaƙi ya ɓarke tsakanin muminai da kafirai to su ba za a taɓa su ba, kuma ba za a taɓa dukiyarsu ba, sannan in an ci nasara a kan cewa, kawunansu kadai suke yaudara ba, domin babu mai cutuwa da abin da suke yi su kadai.

Allah ya ce, akwai cuta a zukatansu. Cutar kuwa ita ce ta shakka da ruɗani da munafunci, wannan ya sanya Allah ya ƙara musu wata cutar, domin duk sanda aka saukar da wata aya ga Annabi SAW to za su kafirce mata, sai cutar zukatansu ta ƙara hauhawa, haka za su yi ta rayuwa har mutuwarsu sannan su je su tarar da azaba mai radadi tana jiran su a lahira saboda ƙaryar da suke ƙirƙira da kuma ƙaryara Annabi SAW da suka riƙa yi.

Narrated Abu Huraira:

The Prophet (ﷺ) said, "The signs of a hypocrite are three:

1. Whenever he speaks, he tells a lie.

2. Whenever he promises, he always breaks it (his promise ).

3. If you trust him, he proves to be dishonest. (If you keep something as a trust with him, he will not return it.)" https://sunnah.com/bukhari:33

An karɓo daga Abu Huraira rA yana cewa:

"Manzon Allah SAW yana cewa: "Alamar munafiƙi 3 ce:

1. Idan ya yi magana sai ya yi ƙarya,

2. kuma idan ya yi alƙawari sai ya saɓa,

3. idan kuma aka amince masa sai ya yi ha'inci." [Bukhari #33 da Muslim #59]

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Faɗakarwa a kan haɗarin munafurci da munafukai.
  2. Furta kalamar shahada da baki kawai ba zai wadatar ba har sai zuciya ta ƙudurce ta, domin Musulunci na gaskiya shi ne miƙa wuya ga Allah SWT a zahiri da baɗini.
  3. Munafukai suna nuna wa Musulmi cewa sun yi imani, alhalin ƙarya suke yi ba su yi imani ba.
  4. Luɗufin da Allah ya yi wa muminai yayin da ya tona asirin munafukai tun da wuri.
  5. Tabbatar da cewa munafukai ba muminai ba ne samsam.
  6. Munafukai mayudara ne, don haka wajibi ne ga muminai su yi hattara da su.
  7. Duk yaudarar mayaudari a kansa za ta ƙare.
  8. Munafurci yana toshe basira, don haka duk wani munafuki ba ya fahimtar cewa kansa yake cuta.
  9. Munafurci muguwar cuta ce wadda idan mai ita bai yi saurin magance ta ba, to za ta yi ta ƙaruwa ne har ta kai shi ga aukawa cikin azaba mai raɗaɗi.
  10. Haɗarin ƙarya da ƙaryara gaskiya. Ƙarya a wurin munafiki ƙaruwa take yi koyaushe.

Baqara 11-13

  1. Idan kuma aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a bayan ƙasa", sai su ce: "Mu fa masu gyara ne kawai." --Quran/2/11
  2. Saurara, lalle su su ne maɓarnata, amma ba sa jin hakan. --Quran/2/12
  3. Idan kuma aka ce da su: "Ku yi imani kamar yadda mutane suka yi imani", sai su ce: "Shin za mu yi imani ne kamar yadda wawaye suka yi imani?" Saurara, lalle su ne wawayen, sai dai ba su sani ba. --Quran/2/13

Tafsiri:

Har ila yau, Allah yana ƙara bayyana wani mugun halin na munafuƙai wanda shi ne, duk sa'adda sahabbai za su yi musu wa'azi su nuna musu kuskurensu, su neme su da su tuba zuwa ga Allah, sai su riƙa yi wa sahabban kallon wasu wawaye jahilai marasa hankali da har suka yarda suka bar garuruwansu da gidajensu da dukiyoyinsu suka yi hijira don wai su yi addinin Musulunci; sai su nuna su fa ba za su taɓa yin wauta irin wannan ba. Sai Allah ya mayar musu da martani da cewa, ai ko su ne tsantsar wawaye, tun da har suka guje wa abin da zai amfane su na imani da Allah suka rungumi abin da zai cutar da su saboda tsabar jahilci da wauta.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Munafurci babbar ɓarna ce a bayan ƙasa.
  2. Yana daga cikin babban bala'i ga mutum a ƙawata masa mummunan aikinsa har ya riƙa ganinsa kyakkyawa.
  3. Haɗarin dake tattare da rikirkicewar tunani wanda zai kai ga maɓarnaci ya riƙa ɗaukan kansa mai shi mai gyara ne.
  4. Daga cikin mummunar siyasar munafukai a kowane zamani shi ne yadda suke sanya rigar masu kawo gyara cikin al'umma, masu fafutukar daidaita rayuwar jama'a, amma a fakaice suna yaƙi da addini da masu addini, suna yi wa abokan gabar Musulmi farfaganda domin lalata aƙidun Musulmi da kyawawan halayensu na addini da zamantakewa da shugabanci.
  5. Faɗakar da muminai da jawo hankalinsu a kan kada su ruɗu da da'awar munafukai da yaudararsu.
  6. Kiran munafukai zuwa ga abin alheri sau tari ba shi da wani amfani, domin yadda suke taƙama da marnar da suke kai yana ƙara musu bijire wa gaskiya.
  7. Faɗakar da Musulmi da kada su ruɗu da farfagandar Munafukai.
  8. Kariyar da Allah yake ba wa sahabban Annabi SAW da muminai.
  9. Tabbatar da hajilcin munafukai.
  10. Duk ɓarancin da ba ya gane cewa shi maɓarnaci ba ne, to shi wawa ne.

Baqara 14-15

  1. Idan kuma suka haɗu da waɗanda suka yi imani sai su ce: "Mun yi imani." To amma idan suka keɓanta da shaiɗanunsu (iyayen gidansu) sai su ce: "Mu fa lalle muna nan tare da ku, mu kwai izgili ne muke yi." --Quran/2/14
  2. Allah Yana yi musu izgili, kuma Yana yi musu talala cikin shisshiginsu suna masu ɗimuwa. --Quran/2/15

Tafsiri:

Wata muguwar sifa ta munafuƙai kuma har ila yau ita ce, yin fuska-biyu, wato idan sun shiga cikin muminai ko sun haɗu da su a hanya sai su riƙa nuna musu suna tare da su, su ma wai muminai ne. To amma da zarar sun koma ga manyan kafirai ko Yahudawa sai su nuna musu cewa, mu fa tare da ku muke, ku bar waɗancan muminai izgili kawai muke yi musu, amma zuciyarmu ba ta son su ko kaɗan. Allah SWT ya mayar musu da martani da cewa: Ai Allah ne yake yin izgili gare su, shi ya sa ya ƙyale su ba tare da ya ba wa muminai dama su gama da su ba, yake kuma ƙawata musu munanan ayyukansu, har ma suke zaton ko a kan gaskiya suke, ba su san cikin ɗimuwa da duhu suke rayuwa ba.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Ƙasƙancin munafukai da wulaƙanta kansu da suke yi da kuma nuna son duniya shi ne ya haifar musu da munafurci a zukatansu.
  2. Duk wanda zai riƙa nuna fuska-biyu ya kuma riƙa ɓoye rashin gaskiyarsa, to wannan ƙasƙantaccen mutum ne.
  3. Bayyana yadda munafukai suke haɗa kai da kafirai maƙiya Musulunci domin yaƙar Musulmi.
  4. Damuwar munafukai har kullum ita ce, yadda za su gamsar da 'yan'uwansu kafirai cewa, manufarsu guda ɗaya ce, kuma su fa imaninsu ba na gaskiya ne ba.
  5. Bayanin yadda Allah SWT yake kunyata munafukai, yake fallasa abin da suke faɗa wa kafurai a asirce.
  6. Haɗarin yi wa muminai izgili, domin yin haka siffa ce ta munafukai.
  7. Irin aikin mutum irin sakamakonsu, yadda munafukai suke yi wa muminai izgili su ma haka Allah SWT yake saka musu da yi musu izgili.

Aya 16

Waɗannan su ne suka musanya shiriya da ɓata, don haka kasuwancinsu bai yi riba ba, kuma ba su zamo shiryayyu ba.

Tafsiri:

A nan Allah SWT yana fito da haƙiƙanin matsayin munafuƙai, ta yadda suke nuna tsananin sha'awarsu da ƙaunarsu ga hanyar ɓata, suke ɗaukar ta a matsayin wata kadara mai daraja da za su iya kashe ko nawa ne don su mallake ta. Don haka suka amince su bayar da shiriya a matsayin kuɗin da za su fanshi wannan mummunar kadara (wato ɓata) da ita. Wannan shi ne haƙiƙanin kasuwancinsu a duniya; ashe kuwa wannan kasuwanci ne maras riba, kuma mai cike da hasara ta duniya da ta lahira.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Bayani game da tsantsar wautar munafukai da rashin basirarsu wadda har ta kai su suke fifita ɓata a kan shiriya, domin kuwa babu wautar da ta kai irin ta wanda zai ba da kuɗi tsababa don a ba shi wata lalatacciyar kadara.
  2. Duk wani attajiri yana fatan samun riba ne daga abin da zai kashe kuɗinsa ya saya. To haka su ma munafukai suna zaton cewa za su sami riba a cikin wancan lalataccen kasuwanci da suke yi, alhalin asara kawai suke tabkawa.
  3. Shiriyar Allah ita ce riba ta gaske. Duk wanda yake kan shiriya ta Allah SWT to shi ne mai samun ribar kasuwancinsa a duniya da lahira. Wanda kuwa ya rungumi ɓata kamar munafuki, to ya tabka hasara ta har abada.
  4. Sau tari munafukai ba su cika shiriyuwa su dawo kan gaskiya ba.

Baqara 17-18

  1. Misalinsu kamar misalin wanda ya wahala ga kunna wuta ne, yayin da ta haskaka abin da yake daura da shi, sai Allah Ya tafiyar da haskensu Ya bar su cikin duffai ba sa gani. --Quran/2/17
  2. Su kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka ba za su taɓa dawowa (kan gaskiya) ba. --Quran/2/18

Tafsiri:

A nan ma Allah yana ƙara yi mana bayani ne a kan waɗannan munafuƙai, inda ya yi mana kwatance na zahiri domin mu fahimta da gaggawa; ya faɗa mana cewa, misa;in halin da munafuƙai suka tsinci kansu a ciki kamar misalin wani mutum ne da yake tafiya ya samu kansa cikin matsanancin duhu, ga tsoro da ya mamaye shi ta ko'ina, sai ya yi ta fafutukar neman haske, ya wahala sosai har ya samo wuta wadda ta haskaka masa kewayansa, ya zamanto yana ganin komai da ke gabansa da bayansa, ya daina jin tsoron da yake ciki a farko, ya fara farin ciki, sai kwatsam hasken ya ɗauke, ga wuta na ci gabansa balbal, ga zafinta yana bugo shi, amma kuma babu haske sai dai duhu yana dukan duhu; ga duhun dare, duhun hadari, ga na ruwan sama, ga duhun rashin haske, ya samu kansa cikin duffai daban-daban ba ya ganin ko da tafin hannunsa.

To haka sha'anin munafukai yake. Da farko suna rayuwa cikin duhun kafirci, sai Musulunci ya bayyana, sai suka ɗosani haskensa, suka sami kariya ta rayukansu da dukiyoyinsu. To amma da yake ba a kan gaskiya suka yi imani ba, sai hasken Musuluncin ya ɓace musu, yayin da suka mutu aka kai su ƙaburburansu, sai suka tsinci kansu cikin duhu na dukan duhu, ga duhun ƙabari, ga na kafirci, ga na munafunci, ga na saɓon Allah iri-iri, ga uwa-uba duhun wutar Jahannama. Tir da wannan makoma.

Dalilin haka ya sa Allah ya ce da su, su kurame ne ba sa jin duk wata gaskiya ji na fahimta; bebaye ne ba sa iya faɗin gaskiya, sannan makafi ne ba sa ganin gaskiya su bi ta. Don haka ne ma babu yadda za a yi su dawo kan hanya.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Fasahar Alƙur'ani wajen buga misalai don a fahimta.
  2. Munafukin da ya yi imani sannan daga baya ya yi ridda, to munafurcinsa zai gusar da alamun hasken imaninsa, don haka rayuwarsa ba ta da sauran wani amfani.
  3. Munafukai sun shiga Musulunci ne saboda kwaɗayin samun ganimar duniya, don kuma su kare kansu daga kisa. To amma da zarar sun mutu duk wannan tagomashin da suke samu ya ƙare, sai azaba mai raɗaɗi ce za su haɗu da ita a ranar alƙiyama.
  4. Munafukai ba sa ƙaruwa da komai na hasken wahayi da shari'a. Idan sun halarci majalisin da ake karanta shari'ar Allah, to kafircinsu da munafurcinsu ba za su ƙyale su su amfana da komai ba.
  5. Sanin gaskiya ba zai yi wa bawa amfani ba idan har bai miƙa wuya ya karɓi gaskiyar ba.
  6. Munafukai a duniya suna rayuwa ne ta ɗimuwa da kiɗimewa, domin suna cikin duhu ne iri-iri da zai hana su ganin gabansu.
  7. Hanyar gaskiya ɗaya ce, amma hanyoyin ɓata yawa gare su.
  8. Munafukai ba sa amfana da zamansu cikin mutanen kirki, domin munafurcinsu ba zai bar su su amfana da su ba.
  9. Ishara zuwa ga cewa, duk wanda zai san gaskiya amma ya yi watsi da ita, to lamarinsa ya fi muni a kan wanda da ma can bai san gaskiyar ba.
  10. Gaɓoɓin da Allah ya ba wa duk wani mutum don ya amfana da su, munafukai sam ba sa amfana da su.
  11. Makantar zuciya da ta basira ta fi makantar ido muni. Kuma munafukai ba za su taɓa dawo wa kan gaskiya ba, domin suna ganin kyawon abin da suke aikatawa.

Baqara 19-20

  1. Ko kuma (misalinsu) kamar wani mamakon ruwan sama ne, wanda yake ɗauke da duffai da tsawa da walƙiya, har ta kai suna sanya 'yan yatsunsu tsawarwaki saboda tsoron mutuwa. Allah Kuma Yana kewaye da kafirai (da iliminsa). --Quran/2/19
  2. Walƙiyar ta kusa ta fauce idanuwansu. Duk sa'adda ta haska musu sai su ci gaba da tafiya cikin (haskenta); idan kuma ta rufe su da duhu sai su tsaya cak. Da kuwa Allah Ya ga dama da sai Ya tafiyar da jinsu da ganinsu. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai. --Quran/2/20

Tafsiri:

A nan kuma Allah SWT ya bayar da misali na biyu game da munafuƙai. Ya misalta su da mutanen da suke tafiya cikin dare sai ruwan sama ya goce kamar da bakin ƙwarya, sannan ga duhu ya baibaye su ta ko'ina; duhun dare da na hadari da na ruwan sama, baya ga haka, ga tsawarwaki da walkiya. Duk sa'adda walƙiya ta haska sai su ɗan motsa gaba ɗaya daga inda suke. Idan kuma duhu ya rufe su sai su ɗan motsa gaba ɗaya daga inda suke. Idan kuma duhu ya rufe su sai su tsaya cak a inda suke. Sannan idan rugugin tsawa ya dame su sai su sanya yatsunsu cikin kunnuwansu saboda tsoron halaka. Sun manta cewa ilimin Allah da Ƙudurarsa suna zagaye da kafirai.

To kamar haka su ma munafuƙai suke, suna rayuwa cikin duhu iri-iri, suna cikin damuwa, duk sa'adda Musulmai suka samu wata ɗaukaka da rinjaye sai su kawo kai don su sami ganima, amma duk lokacin da wasu ayoyin Quran da suka sauka suna maganar azabar Allah SWT da narkonsa ga munafukai sai su ji kamar asirinsu ne zai tonu. Ba su son sauraron ayoyin da suke bayanin wani umurnin Allah ko haninsa, don haka sai su riƙa toshe kunnuwansu da 'yan yatsunsu. To sai Allah ya razanar da su da cewa, da ya ga dama da ya gusar musu da jinsu da ganinsu, su wayi gari dunɗum ba sa ganin komai ba sa jin komai sakamakon biris da gaskiya da suka yi. Domin kuwa Allah mai iko ne kan komai.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Tsoratarwa da tsawatarwa ga kafurai.
  2. Yana da kyau Musulmi ya riƙa roƙon Allah SWT ya jiyar da shi daɗi da jinsa da ganinsa.
  3. Daga cikin mutane akwai wanda ba ya iya ginin hasken gaskiya ko mai karfinsa, domin zuciyarsa ba ta son gaskiya, kamar yadda ido ba ya iya jure wa kallon hasken walƙiya.
  4. Hasken ilimi da imani a tare suke ga mumini, da shi yake ganin hanyar binsa. Amma kafiri kuwa ba ya iya ganin hanyarsa.
  5. Guje wa sauraron gaskiya ba zai kuɓutar da mutum ba, ko ya nuna rashin tsayuwar hujja a kansa.

Baqara 21-22

  1. Ya ku mutane, ku bauta wa Ubangijinku Wanda Ya halicce ku, da wadanda suka gabace ku, ko kwa yi taqwa. --Quran/2/21
  2. Shi ne Wanda Ya sanya muku ƙasa ta zama shimfida kuma Ya sanya muku sama ta zama gini kuma Ya saukar da ruwa daga sama Ya fitar muku da arziƙi na 'ya'yan itatuwa, don haka kada ku sanya wa Allah kishiyoyi alhalin kuna sane. --Quran/2/22

Tafsiri:

Bayan da Allah ya gama maganar kashe-kashen mutane, wato muminai masu taqwa da siffofinsu da kafirai da siffofinsu da munafukai da nasu siffofin, sai kuma ya dunƙule su gaba daya ya kirawo su zuwa ga bauta masa shi kadai. Da ma bautar ita ce manufar halittarsu, kamar yadda ya fada a cikin Surat Az-Zariyati aya ta 56, Sannan ya kafa musu manya-manyan hujjoji guda hudu:

  1. Hujja ta farko ita ce, shi ne wanda ya halicce su har da wadanda suka gabace su, ya ba su ci da sha da bukatunsu, don haka wanda ya yi halitta ai shi ne ya fi cancanci a bauta masa ba wani can daban ba.
  2. Hujja ta biyu ita ce, shi ne wanda ya shimfida musu kasa wadda suke yawo a kanta, su yi gine-ginensu duk a kanta. Lalle wanda ya yi wannan ai shi kadai ya cancanta a bautawa ba wani ba can daban ba.
  3. Hujja ta uku ita ce, shi ne wanda ya daukaka musu rufin samaniya, ya ƙawata shi da rana da wata da taurari, wadanda suke amfanarsu a rayuwarsu a bayan kasa. Wanda ya yi wannan aiki lalle shi ne ya cancanci bauta ba wani abu ba can daban.
  4. Hujja ta huɗu ita ce, shi ne ya sauko musu da ruwan sama daga girgije, wanda suke sha su da dabbobinsu, kuma ya shayar musu da gonakinsu suka sami amfanin gona da kayan marmari iri-iri da ganyayyaki daban-daban. Lalle mai wannan aiki shi ne wanda ya cancanci bauta ba wani can daban ba.

Wadannan ayoyi suna nuni ne ga Tahudin Rububiyya wanda yake jagoranci zuwa ga fahimtar Tauhidin Uluhiyya, wato bautar Allah shi kadai ba tare da yi masa kishiya ba.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Imani da Tauhidin Rububiyya yana wajabta wa bawa ya yi imani da Tauhidin Uluhiyya.
  2. Zamantowar Allah SWT shi ne mahalicci komai, mai kuma bayar da arzuki ga bayinsa, shi ne ya sa ya cancanci a bauta masa shi kadai.
  3. Taqwa wani babban matsayi ne da ba a samunsa sa ta hanyar tsantanta bauta ga Allah shi kadai.
  4. A cikin ni'imomin na duniya ni'imar halitta ita ce mafi girma, domin duk wata ni'ima ta ginu ne a kanta.
  5. Rahamar Allah ga bayinsa da bayanin girman Ƙudurarsa.
  6. Allah yana ba da arzikinsa na duniya ga kowa da kowa; mumini da kafiri babu banbanci.
  7. Haramcin sanya wa Allah kishiya ta hanyar shirka babba ko karama.

Baqara 23-24

  1. Kuma idan kun kasance cikin kokwanto game da abin da Muka saukar wa bawanmu, to ku zo da kwatankwacin sura ɗaya kamarsa, kuma ku kirawo masu taimakonku ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya. --Quran/2/23
  2. To idan har ba ku aikata hakan ba, kuma ba za ku taɓa iyawa ba, to ku kiyayi wata wuta wadda mutane ne da duwatsu makamashinta; an kuwa tanade ta domin kafirai. --Quran/2/24

Tafsiri:

A wadannan ayoyi Allah yana magana ne a kan gaskiyar annabcin Annabi SAW da gaskiyar Alkur'ani da ya zo da shi. Allah ya kawo wata hujja ce mai karfi wadda za ta kawo karshen duk wani shaci-fadin da kafirai suke yi game da Alqur'ani. Allah ya bayyana cewa, shi fa Annabi SAW, mutum ne kamarsu, yana magana da irin harshensu, kuma bai koyi wani ilimi na rubutu da karatu ba. To idan har shi ne ya kirkiri Alkur'ani da kansa ba wahayi Allah ya yi masa ba kamar yadda suke da'awa, to su ma ai Larabawa ne irinsa, sai su kawo ko da sura daya kamar ta Alqur'ani wajen hikima da fasaha. Kuma suna iya gayyato duk wani wanda suke ganin zai taimaka musu don cim ma wannan bukatar tasu. Idan kuwa har suka kasa yin hakan, kuma ba za su iya din ba, to su yi maza su karbi gaskiya don kare kansu daga azabar Allah wadda wuta ce ba irin wadda suka sani ba a nan duniya, domin ita wannan makamashin hura ta mutane ne masu laifuka da duwarwatsu, kuma an riga an yi tanadinta musamman domin kafirai.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Alkur'ani mu'ujiza ce da Allah SWT Ya kuma ƙalubalanci duk masu fasahar larabawa da su kawo kamarsa amma sun kasa.
  2. Alkur'ani ne mafi girmar mu'ujiza da Allah SWT ya ba wa Manzonsa SAW.
  3. Matsayin zama bawan Allah matsayi ne babba, saboda haka Allah ya zabi ya siffanta Manzonsa SAW da shi a irin wannan babban wuri.
  4. Tabbatar wa kafurai cewa ba za su taba kawo wata magana kamar Alkur'ani ba har abada.
  5. Tabbatar da gaskiyar Alkur'ani, domin ya nuna musu cewa ba za su kawo kamarsa ba har abada, kuma ga shi ya tabbata din sun kasa kawo irinsa.
  6. Wuta tana nan, Allah SWT ya riga ya halicce ta, ya kuma tanade ta domin kafirai.

Baqara 25

25. Kuma ka yi albishir ga wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai cewa suna da wasu aljannatai wadanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Duk sa'adda aka arzuta su da 'ya'yan itatuwa daga gare ta sai su ce: "Wannan shi ne irin abin da aka arzuta mu da shi ɗazu." An kawo musu shi yana mai kama da juna, kuma suna da wasu matan tsarkaka a cikinta, kuma su masu zama ne a cikinta dindindin.

Tafsiri:

Bayan Allah ya ambaci sakamakon kafirci a ayar da ta gabata, sai kuma a nan ya ambaci sakamakon wadanda suka yi imani, domin wannan shi ne tsarin salon Alƙur'ani wajen haɗa tsoratarwa da kwadaitarwa. Allah ya fada wa Annabi SAW cewa, ya yi albishir ga wadanda suka yi imani da shi da abin da ya zo da shi na gaskiya, kuma suka aikata kyawawan ayyuka wadanda suka nuna gaskiyar imaninsu da su, ya yi musu albishir da cewa, a lahira suna da wani sakamako na gidajen Aljanna wadanda koramu suke gudana ta karkashin bishiyoyinsu da shuke-shukensu da dakunansu. Duk sa'adda aka kawo musu kayan marmari sai su zaci irin wanda aka taba kawo musu ne ba da dadewa ba a Aljanna, saboda kamanninsu iri daya ne, amma ba su san akwai banbanci ba wajen dandano. Sannan baya ga kayan marmari na Aljanna, har ila yau, suna da wasu mata na aure wadanda suke tsarkaka ne daga duk wani abin kyama, kamar yadda suke da kyawawan halaye da dabi'u. Sannan wani abin kwantar da hankali gare su shi ne, za su dawwama a cikin wannan jin dadi ba zai yanke musu ba har abada.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Babu mai shiga Aljanna sai wanda ya yi imani ya kuma yi aiki nagari.
  2. Sakamakon 'yan Aljanna ya fi ayyukansu.
  3. Cikar Kudurar Allah SWT.
  4. Sakamakon 'yan Aljanna ni'ima ce cikakkiya. Allah ya musu tanadin kayan dadi iri-iri tare da kari.
  5. Kwadaita wa zukata ni'imomin gidan Aljanna don zaburar da su su yi aiki nagari cikin nashadi da walwala.

Baqara 26-27

  1. Lalle Allah ba Ya jin kunyar buga kowanne irin misali komin kankantarsa, sauro da abin ya fi shi. To amma wadanda suka yi imani suna sanin cewa, lalle shi (wannan misali) gaskiya ne daga Ubangijinsu. Amma wadanda suka kafirta sai su rika cewa: "Me Allah Yake nufi da wannan misalin?" Yana kuwa batar da mutane da yawa da shi, kuma Ya shiryar da mutane da yawa da shi, kuma ba kowa Yake batarwa da shi ba sai fasikai. --Quran/2/26
  2. Wadanda suke warware alkawarin Allah bayan ƙulla shi, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi, kuma suke ɓarna a bayan ƙasa. Wadannan su ne cikakkun hasararru. --Quran/2/27

Tafsiri:

A wadannan ayoyi kuma Allah yana sanar da cewa, ba ya jin kunyar bayar da wani misali da kowane abu na halittarsa komai/komin kankantarsa kuwa, kamar sauro da abin da ya ɗara shi girma ko kankanta saboda hikimar da take cikin wadannan misalan da fito da bayanai dalla-dalla don a gane. To yayin da Allah ya ba da irin wadannan misalan masu sauraro sukan kasu gida biyu;

  1. kashi na farko su ne muminai masu yaqini cewa, wannan misali da Allah ya bayar gaskiya ne.
  2. Kashi na biyu kuma su ne kafirai, sai wannan misali ya ɗimautar da su har su nuna rashin yardarsu a kai, suna ganin don me Allah zai rika bayar da irin wadannan misalin, sai su kara kafircewa a kan kafircinsu na farko.

Sun kasa gane cewa, hikimar da ta sa Allah yake yin haka ita ce don kara bambancewa tsakanin mumini da kafiri. Don haka wadannan misalan sukan zama sanadiyyar shiriyar muminai da dama, sannan kuma sukan zama sanadiyyar bacewar kafirai da dama. To amma fa ba wasu ne suke bacewa ta hanyar wadannan misalan ba sai wadanda suke kangare wa ɗa'ar Allah, wadanda suke warware duk wani alƙawari da suka yi tsakaninsu da Allah, sannan suke yi wa shari'ar Allah karan-tsaye, kamar ƙin sadar da zumunci, sannan su yi yaɗa ɓarna ta kafirci da munafinci da zalunci a bayan ƙasa. To irin wadannan halaye nasu su ne suka yi katutu a zukatansu har suka toshe musu zukata ya zamana ba su fahimtar duk wani misali da Allah zai bayar a Littafinsa.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Tabbatar wa da Allah SWT siffar kunya kamar yadda ya dace da girmansa da ɗaukakarsa.
  2. Haɗarin yin izgili da maganar Allah SWT.
  3. Duk wani abu na gaske da Allah SWT ya tabbatar da shi, ba ya halatta wani ya yi musun samuwarsa.
  4. Wani abu guda yakan iya zama sanadiyar shiriyar wani, kuma sanadiyar ɓatan wani.
  5. Haɗarin yin jayayya ba bisa gaskiya ba.
  6. Ma'abota shiriya ko da kuwa su 'yan kaɗan ne a cikin mutane, to amma alherinsu da amfaninsu mai yawa ne. Su kuma ma'abota ɓata ko da suna da yawa, amma alherinsu da amfaninsu kaɗan ne a cikin al'umma.
  7. Yin jayayya da hukuncin Allah SWT abu ne da yake kore imani.
  8. Bai dace kunya ta hana mai kira zuwa ga Allah ya bayyana wani hukunci na Allah ba ko faɗar wata gaskiya, ko da kuwa yin haka zai jawo masa suka daga masu suka.

Baqara 28-29

  1. Ta yaya kuke kafirce wa Allah alhalin a da kun kasance matattu, sannan Ya raya ku, sannan zai kuma mayar da ku matattu sannan Ya raya ku (a karo na biyu) sannan zuwa gare Shi ake mayar da ku? --Quran/2/28
  2. Shi ne wanda Ya halitta muku abin da yake cikin ƙasa gaba ɗaya, sannan Ya nufi sama Ya daidaita su sammai bakwai, kuma Shi Masanin komai ne. --Quran/2/29

Tafsiri:

A nan Allah yana nuna mamakin yadda wadannan kafirai masu kafirce masa da kafirce wa shiriyar da ya aiko Manzonsa SAW da ita, tare da cewa, dalilai masu nuna girman Qudurarsa sun bayyana a sarari. Daga cikin irin wadannan dalilai akwai ewa Allah ne ya kashe su sau biyu ya kuma raya su sau biyu.

  1. Kashewa ta farko, ita ce lokacin da babu si sannan ya samar da su;
  2. kashewa ta biyu, ita ce lokacin da yake karbar rayukansu yayin mutuwarsu.

Rayawa ta farko ita ce, halittarsu babu, sannan rayawa ta biyu ita ce, tayar da su daga ƙaburburansu bayan sun mutu. Su kansu kafirai za su tabbatar da hakan ranar gobe ƙiyama, kamar yadda ya zo a 'Suratu Ghafir', aya ta 11.

Sannan yana daga cikin manya-manyan dalilan cancantar a bauta wa Allah shi kadai, cewa ya halicci abin da yake cikin kasa gaba daya domin amfanin dan'Adam, sannan bayan ya gama halittar kasa ya nufi sama ya yi mata kyakkyawar halitta ya mayar da ita sammai bakwai. Kuma shi mai cikakken sani ne ga duk abin da ya halitta, kuma iliminsa ya game ko'ina.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Cikar Ƙudurar Allah da tabbatar da tashi bayan mutuwa, kuma makomar duk halitta zuwa ga Allah take.
  2. Ni'imar samuwa daga babu, ni'ima ce da ta cancanci a gode wa Allah SWT a kanta, a bauta masa shi kadai kada a kafirce masa.
  3. Bayanin halaccin komai daga abubuwan da Allah ya hore wa ɗan'adam domin amfaninsa, sai abin da nassi ya bayyana haramcinsa.
  4. Allah ya hore komai a duniya domin amfanin ɗan'adam, don haka bai dace ga ɗan'adam ba ya bautar da kansa ga duniya, idan kuma ya yi haka to ya hallaka kansa da kansa.
  5. Tunatar da ɗan'adam ni'imomin da Allah SWT ya yi masa domin ya gode masa ta hanyar bauta masa shi kadai.
  6. Yalwar ilimin Allah SWT da gamewarsa ko'ina.

Baqara 30-33

  1. Kuma ka tuna sa'adda Ubangijinka Ya ce da mala'iku: "Lalle ni zan sanya wani halifa a bayan ƙasa." Suka ce: "Yanzu za Ka sanya mata wanda zai yi ɓarna a cikinta kuma ya zubar da jini, alhali ga mu muna tasbihi tare da gode Maka, kuma muna tsarkake Ka?" (Allah) Ya ce: "Ni fa tabbas Na san abin da ku ba ku sani ba." --Quran/2/30
    1. ˹Remember˺ when your Lord said to the angels, “I am going to place a successive ˹human˺ authority on earth.” They asked ˹Allah˺, “Will You place in it someone who will spread corruption there and shed blood while we glorify Your praises and proclaim Your holiness?” Allah responded, “I know what you do not know.”
    2. And [mention, O Muhammad], when your Lord said to the angels, "Indeed, I will make upon the earth a successive authority." They said, "Will You place upon it one who causes corruption therein and sheds blood, while we declare Your praise and sanctify You?" Allah said, "Indeed, I know that which you do not know."
  2. Kuma sai (Allah) Ya koya wa Adamu dukkan sunaye (na abubuwa) sannan Ya kawo su gaban mala'iku, sai Ya ce: "Ku fada min sunayen wadannan abubuwan in kun zamanto masu gaskiya." --Quran/2/31
  3. Sai suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, ba mu da wani ilimi sai wanda Ka sanar da mu. Lalle Kai ne cikakken Masani, Mai hikima." --Quran/2/32
  4. Ya ce: "Ya Adamu fada musu sunayensu." Yayin da ya fada musu sunayensu, sai (Allah) Ya ce: "Ba Na fada muku cewa, lalle Ni ne Nake sane da gaibin sammai da kasa ba, kuma Nake sane da abin da kuke bayyanawa da kuma abin da kuke boyewa ba?" --Quran/2/33

Tafsiri:

Bayan da Allah ya gama maganar halittar kasa da abubuwan da ke cikinta, da halittar sammai da abubuwan da suka kunsa, sai ya shiga bayanin halittar dan'adam na farko, wato Annabi Adam AS wanda Allah ya damƙa masa alhakin raya wannan kasar ta hanyar bin tsarin da ya hado shi da shi na shiriya, da kuma shimfida adalci a bayan kasa da bauta masa shi kadai ba tare da hada shi da komai ba.

Allah yana ba wa Annabinsa SAW labarin abin da ya fada wa mala'iku na cewa, zai halicci wata halitta da zai ajiye a bayan kasa, wadanda wasunsu za su rika maye gurbin wasu, wato Annabi Adamu AS da zurriyarsa.

  • Allah was telling His Prophet (PBUH) about what He had told the angels, that He would create a creation that He would upon the earth, some of whom would replace some, namely Prophet Adam (PBUH) and his descendants.

Sai mala'ikun suka yi wa Allah tambayar neman sani, amma ba ta jayayya ba, <>

The angels then asked Allah genuinely for knowledge not out of argument,

suka ce: "Shin za ka ajiye wadanda za su rika barna a bayan kasa, suna kashe juna, alhali ga mu muna yi maka tasbihi da tsarkake ka a ko da yaushe? Me zai hana ka saka mu a madadinsu?"

Sai Allah ya fada musu cewa, akwai abin da ba su sani ba na maslahar da ke tattare da sanya dan-Adam ya zama khalifa a bayan kasa.

  • Then God told them that there was something they did not know about the benefits involved in making Adam a caliph on earth.

Daga nan sai Allah ya fara nuna wa mala'ikun wasu hikimomin da yake nufi game da halittar Annabi Adam AS, sai ya koyar da shi sunayen dukkanin abubuwa sannan ya nuna wa mala'iku su nemi su fada masa sunayensu idan har gaskiya suke a da'awar sun san abubuwa, kuma sun fi Annabi Adamu AS cancantar khalifanci a bayan kasa. To fa a nan take sai mala'iku suka tsarkake Ubangijinsu, kuma suka ƙara tabbatar da cewa, lalle su ba komai suka sani ba. Allah ne ya san komai kuma shi ne yake saka duk wani abu a mahallinsa da ya dace. To daga nan sai Allah ya umarci Annabi Adamu AS da ya faɗa musu sunayen wadannan abubuwan. Yayin da kansu, kuma sai Allah ya ƙara tuna musu cewa, da man ai shi ne masanin gaibun da yake sama da wanda yake ƙasa, kuma ya san abin da suke bayyanawa da abin da suke boyewa.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Allah SWT yakan jarrabi bayinsa da abin da ya ga dama. Allah ya jarrabi mala'ikunsa da halittar Annabi Adamu AS, sai ya bayyana a gare su cewa, ba su gane hikimar da take tattare da halittar Adamu da ta 'ya'yansa a bayansa ba.
  2. Dacewar yabo ga wanda ya cancanci yabo da bayyana falalar mai falala, musamman ga wanda bai san shi ba, kamar yadda Allah SWT ya yabi Adamu AS.
  3. Mala'iku suna ƙin aukuwar ɓarna a bayan ƙasa.
  4. Halaccin yin tambaya game da hikimar yin wata halitta idan ya kasance manufar tambayar ita ce neman sani, ba nuna rashin yarda ba.
  5. Mala'iku ba su san gaibu ba.
  6. Falalar Annabi Adamu AS da matsayinsa a wurin Allah.
  7. Allah ya yi magana da Annabi Adamu AS, don haka shi Annabi ne da Allah ya yi magana da shi, kamar yadda ya zo a cikin hadisin da Ibn Hibban ya ruwaito. [Ibn Hibban #6190]
  8. Bayanin ladabin mala'iku ga Ubangijinsu.
  9. Dalili game da fifita annabawa a kan mala'iku.
  10. Girman matsayin ilimi da falalarsa da falalar mai ilimi.
  11. Allah ne kadai masanin gaibun sammai da kasa da abin da yake boye a cikin zukatan bayinsa.

Baqara 34-39

  1. Kuma ka tuna lokacin da Muka ce wa mala'iku: "Ku yi sujjada ga Adamu." Sai duk suka yi sujjada, in ban da Iblis, sai shi ya ƙi, ya kuma yi girman kai, kuma ya tabbata a cikin kafirai. --Quran/2/34
  2. Kuma Muka ce: "Ya kai Adamu, ka zauna gidan Aljanna kai da matarka, kuma ku ci (kayan marmarinta) cikin yalwa a duk inda kuka ga dama, kada kuma ku kuskura ku kusanci wannan bishiyar, sai ku kasance daga cikin azzalumai." --Quran/2/35
  3. Sai Shaidan ya sa suka zame, sai ya fitar da su daga ni'imar da suke ciki. Sai Muka ce: "Ku sauko ƙasa sashinku yana mai gaba da sashi; kuma kuna da mazauni a bayan ƙasa da wani jin daɗi zuwa wani ɗan lokaci." --Quran/2/36
  4. Sai Adamu ya karɓi wasu kalmomi daga Ubangijinsa (na neman gafara), sai Ya yafe masa; lalle Shi ne Mai yawan karɓar tuba kuma Mai yawan jin ƙai. --Quran/2/37
  5. Muka ce: "Dukkanku ku sauko daga cikinta, sannan idan wata shiriya ta zo muku, to wadanda suka bi shiriyata, babu wani tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba. --Quran/2/38
  6. Kuma wadanda suka kafirta kuma suka ƙaryata ayoyinmu, wadannan su ne 'yan wuta, su masu dawwama ne a cikinta. --Quran/2/39

Tafsiri:

📘 Sheikh Abubakar Mahmud Gumi:

Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriya ta, to babu tsoro a kansu, kuma ba su yi baƙin ciki."

📗 Dr. Aliyu Kamal Junaidu:

Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriyarTa, babu tsoro a kansu, kuma ba su yi baƙin ciki."

📕 Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo:

Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriyarTa, babu tsoro a kansu, kuma ba za su yi baƙin ciki ba."

version 2

Muka ce: "Dukkanku ku sauko daga cikinta, sannan idan wata shiriya ta zo muku, to wadanda suka bi shiriyata, babu wani tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba. --Quran/2/38

A wadannan ayoyi, Allah yana sanar da Manzonsa SAW cewa, ya umarci mala'iku da su faɗi su yi sujjada ga Annabi Adamu (AS), kuma nan take suka karɓa umarninsa suka faɗi suka yi masa sujjada, sai Iblis shi kaɗai ya nuna girman kai, ya bijire wa umarnin Allah ya ƙi yi wa Annabi Adamu sajjada. Sai Allah ya umarci Annabi Adamu da matarsa Hawwa'u da su shiga Aljanna su zauna a cikinta, ya yi musu izini da su ci komai na kayan marmari da ke cikinta a wadace, in ban da wata itaciya guda ɗaya wadda ya nuna musu ita ya ce, su nisance ta kada su ci 'ya'yanta domin idan har suka ci to sun ƙetare iyakokin da Allah ya gindaya musu.

Sai Shaiɗan ya yaudare su ta hanyar yi musu waswasi ya sa suka ci 'ya'yan wannan bishiyar, wanda a dalilin haka Allah ya fitar da su daga gidan Aljanna, ya umarce su da su dawo bayan ƙasa su zauna, wanda a nan ne ƙiyayya za ta bayyana a tsakaninsu, kuma nan ne wurin rayuwarsu, idan kuma sun mutu a cikinta ne za a binne su har zuwa lokacin tashin alƙiyama. Bayan haka kuma sai Allah ya laƙanta wa Annabi Adamu wasu kalmomi da zai faɗa Allah ya yafe masa laifinsa, sai ya faɗa shi da matarsa, kuma Allah ya karɓi tubansu domin shi ne mai yafe wa muminai duk wani laifi da za su yi su nemi ya yafe musu.

Daga nan kuma Allah ya umarci Annabi Adamu da Hawwa'u da Iblis da su sauko daga gidan Aljanna gaba ɗaya, kuma ya faɗa musu cewa, idan wani abu na shiriya ya zo musu, littafi ne ko kuma wani manzo ne wanda zai nusar da su hanyar shiriya, idan har suka karɓe shi suka yi aiki da shi to za su samu cikakken zaman lafiya da farin ciki na har abada. Wanda kuwa ya bijire ya ƙi yarda da gaskiya ya ƙaryata ayoyin Allah, to wannan sakamakonsa gidan wuta ne, kuma zai zauna ciki har abada babu fita.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Babbar karramawar da Allah SWT ya yi wa Annabi Adamu da zurriyarsa.
  2. Bayanin kafircin Iblis da girman kansa wajen ƙin bin gaskiya da wulaƙanta halittar Allah SWT.
  3. Falalar mala'iku da yadda suke amsa umarnin Allah cikin gaggawa.
  4. Duk hukunci na Allah ne, shi yake hukunta abin da ya ga dama. Ya yi umarni a yi wa wanda ya ga dama sujjada, ya hana yi wa wani sujjada idan ya ga dama, kamar yadda ya hana wannan al'umma yi wa wani sujjada ba shi ba.
  5. Wajabcin bin umarnin Allah SWT ko da ya saɓa wa son zuciya.
  6. Girman kai game da yi wa Allah ɗa'a yakan iya kai bawa zuwa ga kafurci.
  7. Bayani game da baiwar da Allah ya yi wa Annabi Adamu da matarsa Hauwa ta shiga gidan Aljanna.
  8. 'Ya'yan marmarin gidan aljanna ana samun su a koyaushe ake da buƙatarsu.
  9. Allah SWT yakan iya jarrabar bayinsa ta hanyar hana su wasu abubuwa.
  10. Idan shari'a ta haramta wani abu to sai ta hana duk wani abu da zai iya kai mutum ga abin da aka haramta masa.
  11. Mahallin zama da samun abinci suna daga cikin manya-manyan ni'imomi ga ɗan'Adam.
  12. Abubuwan da aka halatta sun fi waɗanda aka haramta yawa.
  13. Haɗarin saɓon Allah SWT, domin yakan yi sanadiyyar bawa ya rasa wata babbar ni'imata ta Ubangijinsa.
  14. Samuwar Aljanna tun gabanin halittar ɗan'adam.
  15. Ƙiyayyar Iblis ga ɗan'adam da ƙoƙarinsa koyaushe na ya ga ya ɓatar da shi, ya jefa shi cikin saɓon Allah SWT, ya raba shi da ni'imar Allah.
  16. Babu wani wuri da dan'adam zai iya rayuwa sai a bayan ƙasa. Duk wani yunƙuri da fafutuka da wasu suke yi na neman wani wuri na daban da za a rayu a cikinsa ba doron ƙasa ba, to aikin banza ne ba zai yi nasara ba.
  17. Duniya ba matabbata ce ba. Rayuwar dan'adam a cikinta iyakantacciya ce.
  18. Rahamar Allah SWT ga dan'adam da ya tanada masa matsuguni tun kafin ya saukar da shi ƙasa.
  19. Baiwar da Allah ya yi wa Adamu da Hauwa'u; bai bar su cikin zunubi ba, ya bude musu kofar tuba, suka kuma tuba Allah ya karbi tubansu ya kara musu daraja da matsayi a wurinsa.
  20. Falalar tuba zuwa Allah SWT. Idan bawa ya yi laifi ya kuma tuba zuwa ga Allah SWT tuba ta gaskiya, to Allah zai yafe masa ya karbi tubarsa.
  21. Wani abu marar dadi zai iya faruwa ga bawa, amma daga karshe ya zamo masa alheri. Don haka koyaushe bawa ya zamanto yana mayar da al'amarinsa ga Allah yana neman yardarsa cikin komai.
  22. Tun farkon saukowar dan'adam bayan kasa Allah SWT ya hado shi da shiriya da tsarin da zai rayu a kansa, saboda haka babu wani lokaci da Allah SWT ya bar dan'adam sakaka ba tare da wata shiriya ba.
  23. Bin shiriyar Allah SWT da tsarinsa kadai ne zai haifar wa da dan'adam nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsa ta duniya da ta lahira. Kauce wa tsarin Allah SWT shi ne yake bude masa duk wata kofar fitina da rashin zaman lafiya.
  24. Daga cikin dalilan dauwama a cikin wutar Jahannama akwai karyata ayoyin Allah SWT. Wanda ya karyata ayar Allah daya da ya saukar to ya kafirta, kuma zai dauwama a cikin wuta ranar alqiyama.

Baqara 40-46

  1. Ya ku 'ya'yan Isra'ila, ku tuna ni'imata da Na yi muku, kuma ku cika alkawarina zan cika muku alkawarinku, kuma ku kasance Ni Ni kadai. --Quran/2/40
  2. Kuma ku yi imani da abin da Na saukar yana mai gaskata abin da yake tare da ku (na wahayi), kada kuma ku zama farkon jinsinku da zai kafirce masa, kuma kada ku sayar da ayoyina da dan kudi kadan, kuma ku kiyaye dokokina. --Quran/2/41
  3. Kuma kada ku gauraya gaskiya da karya, kuma ku boye gaskiya, alhalin kuna sane. --Quran/2/42
  4. Kuma ku tsayar da salla, kuma ku ba da zakka, kuma ku yi ruku'i tare da masu ruku'i. --Quran/2/43
  5. Shin yanzu kwa rika umartar mutane da ayyukan alheri ku kuma kuna mantawa da kawunanku, alhalin kuna karanta Littafi? Ashe ba za ku hankalta ba? --Quran/2/44
  6. Kuma ku nemi agajo ta hanyar hakuri da kuma salla, kuma lalle ita (salla) babban abu ne sai dai ga masu kaskantar da kai. --Quran/2/45
  7. Wadanda suka tabbatar da cewa, su masu haduwa ne da Ubangijinsu, kuma su zuwa gare Shi suke komawa. --Quran/2/46

Tafsiri:

Bayan da Allah ya ambaci asalin halittar dan-Adam da kuma kiyayyar Shaidan a gare shi, ya kuma faɗa wa Annabi Adamu da zurriyarsa bayan ya saukar da su bayan ƙasa, ya ce kuma zai zo musu da shiriya wadda duk wanda ya bi ta to ya kuɓuta daga kowane irin tsoro da baƙin ciki. Sannan ya yi kashedi ga wadanda za su saɓa wa wannan shiriyar da fuskantar wata azaba mai tsanani ta wutar Jahannama.

To, a wadannan ayoyi Allah yana bayani a kan Banu Isra'ila ne wadanda suka yi ƙaurin suna wajen nuna wa annabawansu taurin kai da butulce wa ni'imar Allah mai yawa da ya yi musu.

Banu Isra'ila su ne jikokin Annabi Yaqoob AS. A nan Allah yana nuna musu ni'imar da ya yi musu, kuma yana umartar su da su zama masu cika alƙawari, idan sun yi hakan shi kuma zai ba su abin da ya alkawarta musu na shiga Aljanna. Ya tunatar da su kan su ji tsoronsa shi kadai sannan ya umarce su da su gaskata Alkur'ani ta hanyar imani da shi da aiki da abin da ya ƙunsa na shari'a, saboda yana ɗauke da irin abin da ya zo cikin littafin Attaura ta Annabi Musa wanda ya danganci Tauhidi, don haka ya gargaɗe su da kada su zama su ne na farko da za su kafirce wa wannan Alƙur'ani da wanda aka saukar wa Alkur'anin shi ne Annabi Muhammadu SAW. Har ila yau ya hana su musanya ayoyin Allah da wani abu na ƙyale-ƙyalen duniya wanda a wurin Allah ba a bakin komai yake ba, ta hanyar watsi da imani da Alkur'ani da abin da Manzon Allah ya zo da shi da ɓoye gaskiya da take ta.

Hakanan ya hana su cakuɗa ƙarya da gaskiya tare da ta alhalin sun san irin illar da take cikin yin hakan. Kuma ya umarce su da tsayar da salla da rukunnanta da wajibanta, su bayar da zakkar dukiyarsu, sannan su tsayar da salla cikin jam'i tare da sauran muminai. Sannan Allah ya zarge su da abin da suke yi na umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, amma kuma su a karan kansu ba sa aiki da abin da yake cikinta na hukunce-hukunce, wanda yin haka ya saɓa wa aikin mutane masu hankali. Daga bisani Allah ya umarce su da su nemi taimako ta hanyar tsayar da salla da hakuri cikin duk al'amura, duk da cewa salla tana da nauyi ga wasu in ban da masu ƙasƙantar da kansu ga Allah wadanda su ne suka tabbatar da cewa, akwai ranar gamuwarsu da Ubangijinsu wadda ita ce ranar alkiyama.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Tuna wa bawa ni'imar da Allah SWT ya yi masa ya fi zama hujja a kansa, yakan kuma sanya shi ya karbi gaskiya da wuri.
  2. Allah SWT ya yi babbar ni'ima ga Banu Isra'ila.
  3. Idan Allah ya yi wa kakanni ni'ima to kamar ya yi wa jikokinsu ne, domin birbishin ni'imar da ya yi musu dole sai ta shafe 'ya'yansu da jikokinsu. Kuma ba don ya kuɓutar da kakanninsu ba ai da su ma ba a same su ba.
  4. Wajabcin gode wa ni'imomin Allah SWT da guje wa butulce masa.
  5. Wajibi ne wanda ya yi bakance na alheri ya cika bakancensa.
  6. Alkur'ani littafi ne da yake gaskata littattafan da suka gabace shi, yake kuma tabbatar da abin da suka zo da shi na gaskiya da kadaita Allah. Hakanan su ma littaffan da suka gabata suna tabbatar da gaskiyar Alkur'ani da ingancin manzancin Annabi SAW.
  7. Duk wanda ya fara kafirce wa Allah, kuma ya zamanto abin koyi ga na bayansa cikin kafirci, to lalle zai dauki nayin zunubansa da na wadanda suka bace a dalilinsa.
  8. Duk wanda ya sayar da ayoyin Allah da 'yan kudi kadan, to lalle ya yi koyi ne da Yahudawa.
  9. Wajabcin bayanin gaskiya ga mutane da haramcin boye ta. Idan kuma wani ya boye gaskiya saboda wani abin duniya da zai samu, to wannan laifinsa ya fi tsanani.
  10. Wajibi mai karantawa ko da'awa ya riqa qoqarin yaye wa mutane shubuhohi da yi musu bayanin duk abin da ba su fahimta ba. It is obligatory for the reciter or preacher to try to clear people's doubts and explain to them everything they do not understand. Kuma duk wanda yake a wurin da babu wanda zai koyar da mutane sai shi, to dole ne ya tashi ya koyar da su abin da suke buqata na addini. And whoever is in a place where there is no one to teach people except him, then he must rise up and teach them what they need in religion.
  11. Haramun ne a riqa qawata qarya don a jawo hankalin mutne zuwa gare ta, ko kuma gurɓata gaskiya don mutane su nisance ta. It is forbidden to embellish a lie to attract people's attention to it, or to distort the truth so that people avoid it.
  12. Yana daga cikin salon Yahudawa na yaɗa ɓarna su riƙa cakuɗa ƙarya da gaskiya.
  13. Mummunan tasirin ɓatattun malamai.
  14. Muhimmancin bayyana gaskiya domin shiryar da ɓatattu zuwa ga miƙaƙƙiyar hanya.
  15. Kamalar wannan shari'a ta Musulunci, domin ta zo da abin da zai tsarkake zukata da kuma dukiyoyi.
  16. Falalar salla a cikin jama'a, domin za a ninnika wa masallaci ladansa.
  17. Haɗarin aikin mutum ya riƙa saɓa wa maganarsa.
  18. Laifin wanda ya san hukunci ya saɓa masa ya fi na wanda ya jahilci hukuncin tun farko.
  19. Hankali yakan hana mai shi aikata mummunan aiki yana sane.
  20. Girman sha'anin salla, sai dai tana da sauki ga wanda Allah SWT ya sauwake masa.
  21. Kwadaitarwa a kan neman sahhale al'amuran rayuwa ta hanyar salla da hakuri.
  22. Girman falalar hakuri.
  23. Sakankancewa da haduwa da Allah SWT yana sanya bawa ya dage wajen kyautata ayyukansa, domin ya samu yardar Allah SWT.
  24. Tabbatar da ranar lahira wadda ita ce makomar dukkan halittu.

Baqara 47-48

  1. Ya ku 'ya'yan Isra'ila, ku tuna ni'imata da Na yi muku, kuma Ni Na fifita ku a kan sauran mutanen duniya. --Quran/2/47
  2. Kuma ku ji tsoron wata rana da babu wani (mai) rai da zai isar wa da wani (mai) rai komai a cikinta; kuma ba za a karbi wani ceto daga gare shi ba, kuma ba za a karbi wata fansa daga gare shi ba, kuma ba za a taimaka musu ba. --Quran/2/48

Tafsiri:

Daga nan har zuwa aya ta 61 Allah ya bayyana irin ni'imomi daban-daban da ya yi ta yi wa Banu Isra'ila, amma maimakon su yi masa godiya ta hanyar biyayya ga Manzonsa Annabi Musa AS sai suka rika nuna butulci da kangare wa umarnin Allah da kin biyayya da girmamawa ga Annabi Musa AS. Allah ya kirawo su yana tuna musu irin ni'imominsa ga iyayensu wanda ko la'alla yin hakan zai sa musu godiyar Allah da shiga cikin addinin gaskiya na Musulunci, ya kuma tuna musu yadda ya fifita su a kan sauran al'ummomi na zamaninsu ta hanyar aiko musu da manzanni daga cikinsu da saukar musu da littattafai, sannan ya tsoratar da su azabar lahira, ranar da kowa ta kansa yake, babu wani wanda zai iya magance wa dan uwansa wata matsala a wannan rana, ko ya fanshi dan'uwansa kafiri ta hanyar ceto shi daga azabar Allah.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Wajibi ne ga Banu Isra'ila su gode wa ni'imar da Allah SWT ya yi musu. Yana daga cikin godiyar Allah SWT su bi Annabinsa Muhammadu SAW da ya aiko musu.
  2. Fifita Banu Isra'ila a kan sauran mutane fifiko ne da ya shafi zamaninsu kadai, saboda yawancinsu a wancan lokacin suna da ilimi da imani da kuma ayyuka nagari.
  3. Bayanin tsananin ranar alqiyama wanda a cikinsa duk wata dangantaka ba za ta amafani kowa ba wajen ta kare shi masa azabar Allah ko ya samu sassauci, sabanin rayuwar duniya.
  4. Kafirai ba za su sami ceto ko fansa ko taimako ba a ranar alqiyama.

Baqara 49-50

  1. Kuma ku tuna lokacin da Muka kubutar da ku daga jama'ar Fir'auna wadanda suke dandana muku mummunar azaba, suna yanka 'ya'yanku maza, kuma suna kyale 'ya'yanku mata. A cikin wannan lamari akwai babbar jarraba daga Ubangijinku. --Quran/2/49
  2. Kuma ku tuna lokacin da Muka raba muku kogi, sai Muka kubutar da ku, kuma Muka nutsar da jama'ar Fir'auna, alhalin kuna kallo. --Quran/2/50

Tafsiri:

A nan kuma Allah ya tuna musu irin yadda Fir'auna shi da magoya bayansa suka rika gana wa iyayensu azaba ta hanyar yanka 'ya'yansa maza da kyale mata don su bautar da su a gidajensu, amma sai Allah ya kubutar da su daga wannan matsananciyar azaba. Wannan kuwa ba karamar ni'ima ce gare su ba, don haka ya zama wajibi a kansu su yi wa Allah godiya.

Sai kuma Allah ya ambata musu wata ni'imar ta daban wadda ya yi musu lokacin da Fir'auna da rundunarsa suka biyo su don halakar da su. Bayan sun iso gabar kogi sai Allah ya umarci Annabi Musa AS da ya daki kogi da sandarsa, sai ko ta rabu gida biyu, suka ga hanya totar a gabansu suka bi suka ketare. Lokacin da Fir'auna ya iso shi da rundunarsa suka fara bi ta wannan hanyar sai Allah mayar da wannan kogi ta hade da su suka halaka gaba daya, mutanen Annabi Musa AS suna gani domin su huce haushin abin da ya faru gare su a baya.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Babbar ni'ima ce ga mutane Allah (SWT) ya kubutar da su daga hannun maqiyansu azzalumai.
  2. Bayanin makircin Fir'auna da jama'arsa yayin da suka yi mummunan tanadin rage yawan Banu Isra'ila ta hanyar yanka 'ya'yansu maza da barin mata da rai domin su riqa yi musu aikin bauta a gidajensu.
  3. Daga cikin munanan ɗabi'un azzalumi akwai wulaƙanta mutane da tirsasa su su riƙa yi musu hidima ba da son ransu ba.
  4. Ni'imar da Allah SWT ya yi wa Banu Isra'ila ta hallakar da maƙiyinsu a gaban idanuwansu, domin su huce haushin azabar wulaƙanci da suka gana musu.
  5. Girman Ƙudurar Allah SWT wadda ta bayyana yayin da ya raba kogi gida biyu, kowane tsagi kamar wani ƙaton dutse.
  6. Allah SWT ya nuna wa Fir'auna ƙarshensa, saboda da ya tashi hallaka shi sai ya hallaka shi da abin da ya kasance yana yi wa mutanensa alfahari da shi, watau ruwa.

Baqara 51-54

  1. Kuma ku tuna lokacin da Muka yi wa Musa wa'adin (ganawa da shi) na kwana arba'in, sannan ku kuma kuka kama bautar ɗan maraƙi a bayansa, alhalin kuna masu zaluntar kawunanku. --Quran/2/51
  2. Sannan sai Muka yi muku afuwa bayan haka, la'alla ko kwa yi godiya. --Quran/2/52
  3. Kuma ku tuna lokacin da Muka ba wa Musa Littafin (Attaura) da abin da yake rarrabewa (tsakanin gaskiya da ƙarya) ko kwa shiriya. --Quran/2/53
  4. Kuma ku tuna lokacin da Musa ya cewa mutanensa: "Ya ku mutanena, lalle ku kun mayar da ɗan maraƙi abin bauta, don haka ku tuba zuwa ga Mahaliccinku, kuma ku kashe kawunanku; wannan shi ne ya fi alheri a gare ku a wajen Mahaliccinku. Lalle shi Mai yawan karɓar tuba ne, Mai yawan jin ƙai." --Quran/2/54

Tafsiri:

Sannan kuma Allah ya sake tuna musu lokacin da Annabi Musa AS ya je ganawa da shi ta tsawon kwana arba'in, su kuma Banu Isra'ila bayan tafiyarsa suka riƙa bauta wa ɗan maraƙi, suka zalunci kansu ta hanyar ɗaukar hakkin Allah na bauta su sanya wa ɗan maraƙi. Daga baya da suka tuba sai Allah ya yafe musu ko wataƙila sa yi godiya.

Allah ya faɗi yadda tubar tasu za ta kasance yayin da Annabi Musa AS ya kirawo su ya shaida musu cewa, sun fa zalunci kansu ta hanyar bautar ɗan maraƙi. Don haka dole ne su tuba; tubar kuwa ita ce, wadanda ba su yi bautar ba daga cikinsu su kashe wadanda suka yi, domin ta haka ne kadai Allah zai yafe musu laifinsu, don kasancewarsa mai karbar tuba mai jin kai.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Banu Isra'ila ba su da wani uzuri na aikata shirka. Sai dai kawai sun yi amfani da tafiyar Annabi Musa AS wajen ganawa da Allah, sai suka shiga aikata kafirci da barna a bayan kasa.
  2. Rashin samuwar wani malami a cikin jama'a yakan haddasa bayyanar shirka da bidi'a a tsakaninsu.
  3. Bayanin cewa bautar wanin Allah SWT babban zalunci ne.
  4. Bayanin yalwar hakurin Allah SWT, kuma Allah yana gafarta shirka ga wanda ya tuba.
  5. Hukunci mai tsanani da Allah (SWT) ya yi wa Banu Isra'ila yayin da ya umarce su da su kashe kawunansu kafin ya karbi tubansu.
  6. Allah SWT ya ba wa Banu Isra'ila Littafin Attaura bayan ya kubutar da su daga Fir'auna da jama'arsa. Babbar hikimar yin haka shi ne domin su kafa al'umma mai bin shari'ar Allah, su zamanto suna da wani saƙo da za su rayu a kansa su kuma yi aiki da shi.
  7. Kyakkyawan abu ne ƙwarai ga mai kira zuwa ga Allah SWT ya riƙa amfani da salo na laluna da lallashi don jan hankulan mutane su saurari maganarsa su karbi gaskiya daga gare shi.
  8. Wajabcin tuba zuwa ga Allah SWT nan take bayan aikata laifi.
  9. Allah SWT yana karbar tuban bayinsa komai girman laifinsu idan har sun tuba sun bar shi.
  10. Tuna wa wanda ya yi wa Allah SWT laifi ni'imomin da ya yi masa don ya ƙara fahimtar munin laifinsa na yi wa Allah butulci.

Baqara 55-57

  1. Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: "Ya Musa ba za mu yi imani da kai ba har sai mun ga Allah a sarari", sai tsawa ta halaka ku, alhali kuma kuna kallo. --Quran/2/55
  2. Sannan sai Muka tashe ku bayan mutuwarku, ko wala'alla kwa yi godiya. --Quran/2/56
  3. Kuma Muka yi muku inuwa da girgije, kuma Muka saukar muku da darɓa da (soyayyun) tsuntsayen salwa, ku ci daga daɗaɗan abin da Muka arzuta ku da shi; kuma ba su zalince Mu ba, sai dai kawunansu kaɗai suke zalunta. --Quran/2/57

Tafsiri:

A nan har ila yau Allah ya sake tuna musu lokain da suka faɗa wa Annabi Musa AS cewa, ba za su taɓa yarda da abin da ya zo musu da shi na gaskiya ba har sai ya nuna musu Allah a fili ɓaro-ɓaro sun gan shi. A dalilin haka Allah ya saukar musu da wata tsawa ta riƙa kashe su ɗaya bayan ɗaya suna kallo da idonsu. Sannan bayan duk sun mutu sai Allah ya sake tayar da su don su gode masa a kan wannan ni'imar.

Allah kuma har wa yau ya tuna musu ni'imar da ya yi musu lokacin da suke yawon ɗimuwa a cikin saharar Sina, ga tsananin zafin rana yana dukan su, sai Allah ya sauko musu da wani girgije ya riƙa yi musu inuwa, sannan ya saukar musu da Mannu da Salwa, watau darɓa da soyayyun tsuntsayen salwa, ya ce su rika cin wannan daddaɗan abinci. To amma duk da irin waɗannan ni'imomi bai sa sun natsu sun gode masa ba, sai ma ƙara butulce masa da suka riƙa yi. To amma wannan duk ba zai cutar da shi da komai ba; kawunansu kadai suke cutarwa.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Bayanin girman Ƙudurar Allah SWT ta raya matattu.
  2. Ba wanda zai ga Allah SWT a fili a nan duniya komai matsayinsa.
  3. Tsananin taurin kan Banu Isra'ila wanda har ya kai su ga sharɗanta wa Annabi Musa AS abin da ba mai yiwuwa ba kafin su yi imani da shi.
  4. Samun inuwa mai sanyi da abinci mai gina jiki da abin sha mai daɗi, suna daga manya-manyan ni'imomin Allah SWT.
  5. Cikar adalcin Allah SWT, don haka ba ya zaluntar kowa.

Baqara 58-59

  1. Kuma ku tuna lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alƙaryar ku ci daga (kayan marmarinta ta) inda kuka ga dama cikin yalwa, kuma ku shiga ƙofar garin a duƙe, kuma ku ce: "(Allah ka) kankare mana laifuffukanmu", za Mu gafarta muku laifuffukanku. Kuma za Mu ƙara wa masu kyautatawa. --Quran/2/58
  2. Sai waɗanda suka yi zalunci suka canza maganar da aka faɗa musu, sai Muka saukar da wata azaba daga sama a kan waɗanda suka yi zalunci saboda abin da suke aikatawa na fasiƙanci. --Quran/2/59

Tafsiri:

A nan Allah yana ci gaba da tuna wa Banu Isra'ila lokacin da ya umarci kakanninsu da cewa, su shiga Baitul Maƙadisi, su ci irin arzikin da Allah ya aje a cikinta a wadace, kuma idan sun zo shiga ta ƙofar garin su sunkuyar da kansu su shiga a duƙe suna neman gafarar Allah. Ya yi musu alƙawarin cewa, idan har sun aikata hakan to zai gafarta musu zunubbansu sannan duk wani wanda ya kyautata aiki daga cikinsu zai ƙara masa falalarsa.

To amma saboda kangarewarsu sai suka canza maganar da aka umarce su da ita, sai suka riƙa cewa: "Ƙwaya a cikin gashi." Sannan kuma suka shiga garin suna jan gindi a ƙasa, a dalilin haka ne Allah ya saukar da azabarsa a kansu.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Idan Allah SWT ya ba wa wasu daga cikin bayinsa nasara a akan maƙiyansu wajibi ne su ƙanƙantar da kansu gare shi, su gode wa ni'imar da ya yi musu ta samun wannan nasarar.
  2. Kyautatawa tana jawo ƙaruwar alheri.
  3. Ƙasƙantar da kai da godiya ga Allah sun sanya bawa ya samu gafarar Allah SWT.
  4. Canja maganar Allah ta fuskar lafazinta ko ma'anarta mummunan aiki ne kuma babban zalunci ne.
  5. Wa'azi da gargaɗi ga masu wasa da maganar Allah da sanya ta inda ba mahallinta ba.

Baqara aya ta 60

Kuma ka tuna lokacin da Musa ya roƙa wa mutanensa ruwan sha, sai Muka ce: "Ka bugi dutse da sandarka", sai idanuwan marmaron ruwa goma sha biyu suka ɓuɓɓugo daga cikinsa. Haƙiƙa kowaɗanne mutane sun san mashayarsu. (Muka ce): "Ku ci kuma ku sha daga arzikin Allah, kuma kada ku yaɗa ɓarna a bayan ƙasa.

Tafsiri:

Sannan Allah ya ƙara tuna musu lokacin da suka nemi ruwan sha daga Annabi Musa yayin da suka tsinci kansu a saharar Sina, sai Annabi Musa ya roƙi Allah ya shayar da su ruwa, sai Allah ya umarce shi da ya doki dutse da sandarsa, da ya aikata hakan, nan take kuwa Allah ya fitar musu da idanuwan marmaro na ruwa har guda sha biyu, wato adadin yawan ƙabilar Banu Isra'ila. Kowace ƙabila ta gane mashayarta. Sannan ya umarce su da su ci su sha daga abin da Allah ya azurta su da shi, kuma kada su kuskura su yaɗa ɓarna a bayan ƙasa. Watau dai Allah ya hore musu ci da sha ba tare da wata wahala ba, kuma ya hore musu ruwan sha isasshe ba tare da wani tirmitsitsi ba. --Quran/2/60

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Allah ne kadai mafakar bayinsa yayin da suka shiga cikin wata matsala.
  2. Tabbatar da mu'ujiza ga Annabi Musa AS. Allah ya fitar masa da ruwa mai yawa daga dutse ba tare da wata wahala ba bayan ya doke shi da sandarsa, kuma ya fitar musu da idanuwar ruwa goma sha biyu adadin ƙabilun Banu Isra'ila.
  3. Bayanin girmar Ƙudurar Allah SWT mai aikata abin da ya ga dama a sanda ya ga dama.
  4. Wata babbar ni'imar da Allah SWT ya yi wa Banu Isra'ila a nan shi ne gusar musu da duk wani abu da zai haddasa gaba da husuma a tsakaninsu da samar musu da buƙatarsu ta ruwa ba tare da wata takura ba.
  5. Allah SWT yana iya arzuta bawa ba tare da wata wahala ko wani aiki mai yawa ba.
  6. Bayanin cewa Yahudawa wasu mutane ne da suka shahara da ɓarna a bayan ƙasa, shi ya sanya Allah SWT ya hane su da ɓarna a nan.

Baqara aya ta 61

Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: "Ya Musa, ba za mu iya haƙuri a kan abinci iri ɗaya ba, don haka ka roƙa mana Ubangijinka ya fitar mana (wani abincin) daga abin da ƙasa take tsirarwa, daga mabunƙusanta da gurjinta da alkamarta da wakenta da albasarta." Sai ya ce, "Yanzu kwa nemi musanya ƙasƙantaccen abu da wanda yake shi ne mafifici? To ku sauka kowane gari, domin za ku samu abin da kuka roƙa (a cikinsa)." Don haka sai aka sanya musu ƙasƙanci da talauci, kuma suka koma da fushin Allah. Hakan ya faru gare su ne saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani haƙƙi ba. Hakan ya faru saboda saɓon da suka yi da kuma ta'addancin da suka riƙa yi. --Quran/2/61

Tafsiri:

Sannan Allah ya ci gaba da tuna musu wata kangarar tasu da butulcewarsu ga ni'imar Allah yayin da suka nuna wa Annabi Musa cewa, su fa sun gaji da cin abinci iri daya, (wato Mannu da Salwa) wanda Allah yake ba su a kullum ba tare da sun sh wata wahala ba. Don haka suka nemi Annabi Musa AS da ya roqa musu Ubangijinsa don ya riqa ba su irin abincin da qasa take fitarwa, irin su duma da alkama da albasa da wake da sauraransu. A kan haka Annabi Musa ya zarge su da butulci da renuwa, yayin da suka fifita abinci mafi qasqanci a kan mafificin abincin da ba inda za a same shi. Don haka ya ce musu, su je su shiga kowane gari za su sami duk abin da suke nema. To ganin yadda suka rena ni'imar da Allah ya yi musu, sai aka jarrabe su da qasqanci da talauci wanda zai tilasa su su rusuna wa wasu suna neman taimako a wurinsu tun da sun rena d'aukakar da Allah ya yi musu. Abu mafi muni ma da ya auka musu shi ne, fushin Allah da suka jawo wa kansu. Kuma Allah ya ce, ya yi musu haka ne saboda bijire wa ayoyinsa da suka yi ta yi, suna kashe annabawansa don sun fad'a musu gaskiya, kuma duk abin da ya kai su ga haka shi ne sab'on Allah da qetare iyakokin da suka riqa yi.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Bayanin wautar Banu Isra'ila da rashin hankalinsu yayin da suka fifita abu mafi qasqanci, watau abincin da ake samu ko'ina, a kan abu mafi daraja watau mannu da tsintsayen salwa.
  2. Yahudawa mutane ne da suka shahara da talaucin zuci da tsananin kwad'ayi, kuma komai aka ba su ba sa gamsuwa.
  3. Yana daga cikin siffofin Yahudawa qetare iyakokin Allah da ta'addanci a kan bayin Allah.
  4. Bayanin hatsarin wulaƙanta ni'imar Allah, kuma duk wanda yake aikata haka Allah na iya raba shi da wannan ni'imar da ya ba shi.
  5. Halaccin yin tawassuli da addu'ar wadanda ake sa tsammanin Allah SWT yana karbar addu'arsu, kamar mutanen kirki da iyaye.
  6. Duk wani qarfi da daukaka na zahiri da Yahudawa za su samu, to Allah SWT ya tabbatar da cewa, su a wajensa mutane ne qasqantattu wulaqantattu.

Baqara 62

Kuma lalle waɗanda suka yi imani da Yahudawa da Nasara da Sabi'awa, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar Lahira kuma ya yi aiki na ƙwarai, to suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.

Tafsiri:

Hikimar kawo wannan ayar ana tsakiyar bayanin laifuffukan Banu Isra'ila ita ce, don a nuna musu cewa, ƙofar tuba gare su a buɗe take matuƙar za su tuba su inganta imaninsu da ranar lahira su yi kyakkyawan aiki, to Allah zai ba su ladansu cikakke kuma babu wani tsoro a tare da su game da abin da za su je lahira su iske, kuma babu wani baƙin ciki da za su yi na abin da suka tafi suka bar shi a nan duniya.

Wadanda suka yi imani a nan ana nufin al'ummar Annabi Muhammadu SAW wadda ta yi imani da shi, ta yi imani da dukkan littafan Allah da manzanninsa. An ware su da wannan suna domin ƙarfin imaninsu da cikarsa.

Yahudawa kuwa ana nufin mabiya Annabi Musa AS wadanda suka yi imani da shi, suka yi aiki da abin da aka saukar masa kafin a shafe aiki da addininsa, ko kuma kafin su gurɓata shi.

Nasara kuma, ana nufin mabiya Annabi Isa AS kafin a shafe addininsa ko kafin su jirkita shi.

Sabi'awa kuwa wasu ƙungiyoyi ne, daga cikinsu akwai wadanda suka kasance a kan aƙidar kaɗaita Allah da haramta duk wata alfasha da zalunci, duk da kasancewarsu ba bisa wani addini suke ba, to amma ba sa aikata kafirci. To duk wanda ya kyautata aiki daga cikin wadannan al'ummomi da suka gabata, yana da kyakkyawan sakamako a wurin Allah, ba zai ɓata masa rayuwarsa ta lahira ba.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Falalar imani da aiki na ƙwarai. Duk mai wannan siffa zai samu aminci a nan gaba, kuma ba zai yi bakin cikin abin da ya bari a bayansa ba.
  2. Muhimmancin yin bayanin hukuncin Allah ga mabiya wasu addinai da ba Musulunci ba.
  3. Yahudawa da Nasara da Sabi'awa wadanda suka yi imani da Kadaitakar Allah, suka yi aiki da shari'un annabawansu, har suka mutu a kan haka kafin aiko Annabi Muhammadu SAW, ko kuma wadanda suka riski Musulunci daga cikinsu suka musulunta suka bar addininsu na farko, to duk wadannan sun tsira sun kuma rabauta.

Baqara 63-66

  1. Kuma ku tuna lokacin da Muka ɗauki alƙawari mai ƙarfi daga gare ku, kuma Muka ɗaga dutsen Ɗuri a kanku (Muka ce): "Ku karɓi abin da Muka ba ku da ƙarfi (Attaura), kuma ku tuna abin da yake cikinsa, wala'alla ko kwa yi taƙawa." --Quran/2/63
  2. Sannan bayan haka sai kuka juya da baya, to ba domin falalar Allah da rahamarsa a gare ku ba, lalle da kun kasance daga cikin asararru. --Quran/2/64
  3. Kuma hakika kun san wadanda suka yi shisshigi daga cikinku game da ranar Assabar, sai Muka ce da su: "Ku zama birrai kuna ƙasƙantattu." --Quran/2/65
  4. Sai Muka sanya ta (wannan uƙubar) ta zama izina ga al'ummomin da suke zamanin faruwarta da kuma garuruwan da suke daura da su, kuma don ta zama wa'azi ga masu taƙawa. --Quran/2/66

Tafsiri:

A nan Allah ya ci gaba da tunatar da Banu Isra'ila alkawarin da ya yi da su na cewa, za su yi imani da Manzonsa SAW; za su rike shari'arsa, kuma za su qanqame Attaura da gaske, har ma sai da ya daga dutsen Ɗuri a samansu don su karbi wannan alkawari da ya yi da su, su ci gaba da karanta Attaura suna aiki da abin da yake cikinta na ilmantarwa don su zama masu taqwa. Amma kuma daga bisani sai suka warware wannan alkawari, suka bijire masa. Ba don Allah ya nufe su da falalarsa, ya ba su damar tuba kuma ya karbi tubarsu ba, to da sun wayi gari cikin halakakku a duniya da lahira.

Kuma Allah ya tunatar da su labarin wasu kangararru daga cikinsu wadanda suka kangare wa dokar Allah wadda ta hana su kamun kifi a duk ranar Assabar, ya neme su da zauna gidajensu, amma sai suka bijire ma wannan dokar, sai Allah ya mayar da su birai, ya qasqanta su. Kuma Allah ya sanya wannan uquba da ya yi musu ta zama abin tsoratarwa kuma wa'azi da izina ga masu laifuka irin nasu, har ma da garuruwan da suke maqotaka da su, hakanan kuma ta zama tunatarwa ga masu taqwa.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Bayanin karfin Kudurar Allah SWT da cikar ikonsa ta yadda ya tunɓuke dotse daga inda yake, ya ɗaga shi sama ya bar shi yana reto ba tare da wani abu ya riƙe shi ba.
  2. Wajabcin riƙo da addini da ƙarfi a koyaushe.
  3. Mummunan halin Banu Isra'ila na taurin kai da rashin wa'azantuwa da ayoyin Allah SWT.
  4. Haramcin bin wasu dabaru don kyauce wa hukunci shari'ar Allah da aikata haramun.
  5. Allah SWT yana bayar da labaran wadanda suka gabata domin wa'azantarwa.
  6. Babu masu wa'azantuwa da ayoyin Allah sai masu taqwa kadai.

Baqara 67-74

  1. Kuma ku tuna lokacin da Musa ya ce wa mutanensa: "Allah Yana umartar ku da ku yanka saniya", sai suka ce: "Yanzu ka riƙa yi mana izgili?" Sai ya ce: "Ina neman Allah Ya kiyaye ni da zama cikin jahilai!" --Quran/2/67
  2. Sai suka ce: "Ka roƙa mana Ubangijinka Ya yi mana bayanin yaya take?" Sai ya ce: "Lalle Shi yana cewa, lalle ita saniya ce, ba tsohuwa ba kuma ba budurwa ba, tana tsakatsakin haka". Don haka ku aikata abin da ake umartar ku. --Quran/2/68
  3. Sai suka ce: "Ka roƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana mene ne launinta?" Sai ya ce, "Lalle Shi yana cewa, lalle ita saniya ce mai launin fatsi-fatsi mai tsananin cizawa, tana faranta wa masu kallonta rai". --Quran/2/69
  4. Sai suka ce: "Ka roƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana yaya take, lalle shanu sun rikitar da mu, kuma lalle mu in Allah Ya so masu shirywa ne." --Quran/2/70
  5. Ya ce: "Lalle Shi yana cewa, ita saniya ce wadda ba horarriya ba ce da take noma kasa, kuma ba ta shayar da shuka; lafiyayya ce, babu dabbare-dabbare a jikinta". Sai suka ce: "Yanzu ne ka zo da gaskiya". Sai suka yanka ta, kamar dai ba za su aikata ba. --Quran/2/71
  6. Kuma ku tuna lokacin da kuka kashe wani mutum, kuma kuka riƙa tura wa juna (laifin kisan), Allah kuma Mai bayyanar da abin da kuka kasance kuna ɓoyewa ne. --Quran/2/72
  7. Sai Muka ce: Ku doke shi (mataccen) da wani sashinta (saniyar)." Kamar haka ne Allah Yake raya matattu, Yake kuma nuna muku ayoyinsa don ko kwa hankalta. --Quran/2/73
  8. Sannan sai zukatanku suka ƙeƙashe bayan haka, suka zama kamar dutse ko ma fiye da dutse ƙeƙashewa. Kuma lalle daga cikin duwatsu akwai waɗanda ƙoramu suke ɓuɓɓugowa daga cikinsu; akwai kuma wadanda suke tsatssagewa ruwa ya fito daga cikinsu; akwai kuma wadanda suke faɗowa saboda tsoron Allah. Allah ba marafkani ne ba game da abin da kuke aikatawa. --Quran/2/74

Tafsiri:

A wadannan ayoyi, Allah ya tunatar da Banu Isra'il labarin iyayensu da Annabi Musa AS lokacin da suka neme shi da ya taimaka musu da binciken gano wani daga cikinsu da ya yi kisan kai, kuma ba su gane kowane ne shi ba.

  • In these verses, Allah reminds the Children of Israel of the story of their parents and Prophet Moses (peace be upon him) when they asked him to help them investigate and find one of their own who had committed suicide, but they did not recognize who it was.

Sai Allah ya yi masa wahayi da ya umarce su da su yanka saniya, domin su doki wannan mamaci da wani bangare daga jikinta, sai ya sake rayuwa ya faɗa musu wasu siffofi takamaimai na saniyar ba, domin yana nufin kowace iri suka yanka ta gamsar. To amma saboda tsaurin kansu da ta'annutinsu, sai suka dauki maganar Annabi Musa AS a matsayin izgili yake yi musu. Sai Annabi Musa ya nemi Allah ya tsare shi daga kasancewa cikin wawayen mutane masu yi wa mutane izgili. Duk da haka wannan bai sa Banu Isra'ila sun yanka saniyar ba, sai suka ci gaba da yi wa Annabi Musa AS tambayar ƙwaƙwa, suka ce ya roƙi Ubangijinsa ya faɗa musu wace irin saniya za su yanka? Sai Annabi Musa AS ya fada musu cewa, Allah ya ce saniyar ce wadda take tsakatsaki, ba babba ba sosai, ba kuma karama sosai ba. To duk da haka ba su wadatu sun tsaya iya nan ba, sai suka kara zaƙulo wata tambayar suka ce, Annabi Musa ya tambayo musu Ubangijinsa launin saniyar da za su yanka. Annabi Musa ya ce, Allah ya fada masa cewa saniya ce mai rawayar launi tsantsa, kuma kyakkyawa wadda kyanta yake faranta wa duk wanda ya kalle ta rai.

To maimakon Banu Isra'il su tsaya iya nan da tambayoyinsu na kwakwa, sai suka ci gaba da ce wa Annabi Musa, su fa shanu sun rikita su, har sun kasa gano wacce ake so su yanka, don haka Annabi Musa ya sake neman Ubangijinsa da ya kara fayyace masa irin saniyar da yake nufi. To amma a wannan karo, sai suka ce in Allah ya so za su gano saniyar da ake musu bayani. Daga nan Annabi Musa ya sake fada musu cewa, Allah ya fada masa cewa saniyar da ba a taba sa ta wani aiki ba na noma ko na ban ruwa ba, sannan kuma ba ta da wata naƙasa a tare da ita, kamar yadda kuma launin nata na rawaya ne tsantsa, ba tare da ya gauraya da wani launi ba. To fa sai a nan ne suka ce wa Annabi Musa, yanzu suka ji ya zo da batu na gaskiya wajen tantance musu siffofin saniyar. Sai suka tafi neman ta, har suka samo ta suka yanka ta, abin da kamar ma ba za su iya yi ba. Wato sun yanka ta ba da son ransu ba (begrudgingly). Ko kuma saboda irin yadda suka riqa tambayar qwaqwa, har sun kusa su ce ma sun fasa yanka saniyar. Domin da suna da sha'awar zartar da umarnin da Allah ya yi musu, da a karon farko sun zartar, to amma sai suka tsaya tambayoyi na rashin yarda, suka tsananta, sai su ma Allah ya tsananta musu. Daga nan Allah ya umarce su da su doki wannan mamaci da wani bangare na saniyar, sai suka yi hakan, Allah kuma ya sake raya shi, ya tashi ya fad'a musu sunan wanda ya kashe shi.

Wannan abu da ya faru yana cikin dalilai da Allah ya nuna wa Banu Isra'ila da sauran 'yan'Adam cewa, Allah zai iya sake tayar da matattu don yi musu hisabi a ranar gobe qiyama. Allah ya ce ya yi musu haka ne don su yi hankali, su bar aikata duk wani abu wanda zai cutar da su a wurin Allah. To amma maimakon su yi hankali su qara nutsuwa, sai zukatansu suka bushe, suka qeqashe, suka zama masu tauri kamar dutse, ko ma fiye da dutse, domin dutse duk da taurinsa, ya fi zukatan Yahudawa laushi, domin a cikin duwatsu akwai wadanda ruwa yake kwarara daga cikinsu, akwai kuma wanda yake tsagewa yana fitar da ruwa, akwai kuma wanda yake fad'owa qasa saboda tsoron Allah.

Allah yana qara tsoratar da su ta hanyar fad'a musu cewa yana sane da duk abin da suke kitsawa na sab'on Allah, kuma sai ya yi musu cikakkiyar sakayya a kan aikinsu.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Taurin kan Banu Isra'ila da rashin ladabinsu ga annabawansu, har ta kai sun tuhumi Annabi Musa AS da yi musu izgili ko cewa, ya yi wa Allah ƙarya ya jingina masa abin da bai faɗa ba ya ce ya faɗi.
  2. Girman kan Banu Isra'ila da rashin karɓar umarnin Allah a karon farko, sai bayan an sha daga da su. Kuma dubi yadda suka kasa cewa: 'Ka roƙa mana Allah", sai dai su ce: "Ka roƙa mana Ubangijinka." Me zai hana su su ce: "Ubangijinmu"? Ba komai wannan yake nunawa ba, sai girman kai da nuna tawaye.
  3. Tambayar ƙwaƙwa marar amfani tana iya sa a faɗa cikin tsanani. Domin tun farko da sun yanka kowace irin saniya, da ta gamsar, to amma sai suka tsananta tambaya, sai Allah ya ƙara tsananta musu.
  4. Yi wa mutane izgili yana daga cikin ɗabi'a ta wawayen mutane marasa tunani, shi ya sa Annabi Musa AS ya nemi Allah ya kiyaye shi daga faɗawa cikin wannan ɗabi'a.
  5. Sandararrun halittu na Allah, kamar duwatsu da makamantansu, duk suna jin tsoron Allah, saboda sun san girmansa da ɗaukakarsa.

Baqara 75-82

  1. Yanzu (ku muminai) kwa sa ran su amince da ku, alhalin wata ƙungiya daga cikinsu suna sauraron maganar Allah sannan su jirkita ta bayan sun fahimce ta alhalin kuwa suna sane? --Quran/2/75
  2. Kuma idan suka haɗu da waɗanda suka yi imani sai su ce: "Mun yi imani", amma kuma idan sashinsu ya keɓance da sashi sai su ce: "Yanzu kwa riƙa faɗa musu abin da Allah Ya yi muku buɗi da shi don su kafa muku hujja da shi a wurin Ubangijinku? Shin ba za ku hankalta ba?" --Quran/2/76
  3. Shin ko ba su san Allah Yana sane da abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanawa ba? --Quran/2/77 (see also 67:13 [2], 64:4 [3])
  4. Kuma daga cikinsu akwai jahilai waɗanda ba su san Littafi ba sai burace-burace, kuma zato kawai suke yi. --Quran/2/78
  5. To tsananin azaba ya tabbata ga waɗanda suke rubuta littafi da hannayensu sannan su ce: "Wannan daga Allah yake", don su musanya shi da wani ɗan kuɗi kaɗan. To tsananin azaba ya tabbata a gare su saboda abin da suka kasance suna tsuwurwuta. --Quran/2/79
  6. Kuma suka ce: "Wuta ba za ta shafe mu ba sai cikin wasu 'yan kwanaki ƙididdigaggu." Ka ce: "Shin kun yi wani alƙawari ne da Allah, don haka Allah ba zai saɓa alƙawarinsa ba? Ko kuma kuna faɗar abin da ba ku da ilimi ne kuna jingina wa Allah?" --Quran/2/80
  7. E! Wanda duk ya aikata mummunan aiki kuma laifuffukansa suka kewaye shi, to waɗannan su ne 'yan wuta, su masu dawwama ne a cikinta. --Quran/2/81
  8. Waɗanda kuma suka yi imani kuma suka yi ayyuka na ƙwarai, to waɗannan 'yan Aljanna ne, kuma su masu dawwama ne a cikinta. --Quran/2/82

Tafsiri:

Bayan Allah ya ba da labarin yanayin da zukatan Banu Isra'ila suka zama, yadda suka taurare kamar duwatsu ko ma fiye da duwatsu, sai ya dawo kan muminai a waɗannan ayoyi yana faɗa musu cewa, su fitar da rai game da imanin wadannan mutane, domin babu wata alama da ta nuna suna shirye da karbar shiriya. Hasali ma malamansu ma wadanda suke karanta musu Attaura da abin da yake cikinta na maganar Allah, suna canja ta, suna gurbata ta, bayan kuwa sun fahimce ta, sai suka canza ma'anoninta zuwa wata ma'ana daban da za ta yi daidai da son ransu.

Sai kuma Allah ya fadi mummunan hali na wasu Yahudawa, wadanda suka yafa rigar munafinci a jikinsu. Wato duk lokacin da suka hadu da Annabi SAW da sahabbansa, sai su ce: "Ai mu muminai ne", amma idan sun koma cikin 'yan uwansu Yahudu, sai sauran Yahudawan da ba su yafa rigar munafinci ba, su rika zargin wadancan munafukan Yahudawan, suna ce musu: "Me ya sa za ku rika fada wa Musulmi abin da Allah ya sanar da mu a Attaura na siffofin Annabi ko labarin irin azabar da Allah ya saukar wa kakanninmu saboda kangararsu ko kuma abin da ya sanar da mu na cewa, akwai Annabin da zai bayyana mai siffofi iri kaza da kaza? Domin fa yin haka ai wata hujja ce kuke ba su da za su kafa mana ita gobe kiyama a gaban Allah cewa mun san gaskiya, kawai mun ki yin imani ne da gangan. Wannan abu da kuke yi rashin hankali ne." Sai Allah ya ce, Yahudawa suna irin wadannan maganganu da 'yan uwansu a boye, kamar ba su san Allah ya san duk abin da suke bayyanawa, da abin da suke boyewa ba, shi a wurinsa babu wani bambanci tsakanin abin da suke bayyanawa, da abin da suke boyewa a zukatansu.

Sannan Allah SWT ya bayyana cewa, Yahudawa ba dukkansu ne suke da ilimi ba; a cikinsu akwai ma wadanda ba su iya ko rubutu da karatu ba, don haka ba ma sa iya karanta littafin Attaura; abin da kawai suka sani shi ne tatsuniyoyi da shaci-fadi, kamar ganin da suke yi cewa babu wanda zai shiga Aljanna sai su, ko su ba za a sa su a wuta ba sai na 'yan kwanaki kadan, da ire-iren wadannan tatsuniyoyi marasa kan-gado. Allah ya ce babu komai na ilimi a tare da irin wadannan Yahudawa, in ban da zato da kame-kame. Kamar yadda ya fada a Suratun Nisa'i, aya 157.

Sannan kuma sai Allah SWT ya bayyana wani kason na Yahudawa, wadanda su ne miyagun malamansu, wadanda babu Allah a zukatansu, sai neman abin duniya kawai, don haka sai su rika canza littafin Attaura, suna kuma rubuta wasu qarairayi da hannuwansu, amma sai su ce maganar Allah ce. To wadannan miyagun malaman za su gamu da azaba mai tsanani saboda karyar da suka rika yi wa Allah SWT domin su ci haram da ita, don haka sakamakon mai muni ne kwarai da gaske a lahira.

Daga nan kuma sai Allah ya ambaci aqidar da ta ja wadannan miyagun malaman suka rika yi wa Allah karya don cin dukiyar mabiyansu, ta cewa, wai wuta a lahira ba za ta ci su ba, sai cikin wasu 'yan kwanaki kadan, daga nan sai a fitar da su, don haka ba su da wata babbar matsala a lahira komai suka aikata a nan duniya. Sai Allah ya umarci Annabi SAW da ya mayar musu da martani, ya tambaye su, ko suna da wata yarjejeniya da suka yi tsakaninsu da Allah SWT a kan hakan, wadda za ta tabbatar da abin da suke da'awa? Idan suna da ita, to shi ke nan suna da hujja a hannunsu, domin Allah ba ya karya alkawari. Idan kuwa babu wannan yarjejeniyar, to saboda me za su rika fadar karya suna jingina wa Allah?

Sannan sai Allah ya karyata waccan magana tasu ta cewa, su ba za a sanya su a wuta ba, sai na wanin dan takaitaccen lokaci, ya ce, ba haka ne ba, hukuncin Allah shi ne, duk wanda ya aikata laifi, kamar irin hada Allah da wani ko yi masa karya, har zunubansa suka dabaibaye shi ta ko'ina, ya kuma mutu a kai bai tuba ba, to zai shiga wuta ne ya kuma zauna cikinta har abada babu fita. Su kuma wadanda suka ba da gaskiya da Allah, suka yi kyawawan ayyuka, to wadannan 'yan Aljanna ne masu zama a cikinta har abada babu fita.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Allah SWT yana lallashin Annabinsa SAW da nuna masa kada ya damu da irin halin Yahudu, saboda su mutane ne masu taurin kai, zai yi wahala su yi imani.
  2. Canza ma'anonin ayoyin Allah SWT bayan fahintarsu ya fi matukar muni, fiye da wanda zai canza ma'anar saboda rashin fahinta, domin jahili ana iya yi masa uzuri da jahilcinsa, sabanin wanda ya sani amma ya karkace.
  3. Ya kamata ga mutum ya zama mai lura da hankaltar abubuwa, ya zama yana tunani game da duk abin da zai aikata, ko zai fada, kafin ya kai ga aikatawa ko ya fada.
  4. Abu ne mai matukar muni mutum ya zauna ba tare da yana fahintar littafin Allah ba, sai dai bibiyar tatsuniyoyi da maganganu marasa tushe, ko kuma ya zama mai karatun littafin Allah, amma ba tare da neman sanin ma'anoninsa ba, sai tilawarsa kadai.
  5. Imani da fatar baki kadai ba zai shigar da mutum Aljanna ba, sai idan ya hada da kudurin zuciya da ayyuka na kwarai, wannan shi ne ya sa munafukai ba zaa su shiga Aljanna ba.
  6. Yana daga cikin miyagun dabi'u na Yahudawa, karya da ha'inci da yin baki-biyu.
  7. Yana daga cikin siffofin Allah, kasancewarsa mai gaskiya kuma ba mai saba alkawari ba. Wannan yana nuna cikar ikonsa da kuma cikakkiyar gaskiyarsa. Saboda gazawa, ko kuma qarya suna daga cikin dalilan saba alkawari. Allah kuwa ya tsarikaka daga gare su.

Baqara 83-86

  1. Kuma ka tuna lokacin da Muka ɗauki alƙawari daga Banu Isra'ila cewa, ba za ku bauta wa kowa ba sai Allah, kuma za ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku riƙa yi wa mutane kyakkyawar magana, kuma ku tsai da sallah, kuma ku ba da zakka, sannan sai kuka ba da baya sai 'yan kaɗan daga cikinku, alhalin kuna masu bijirewa. --Quran/2/83
  2. Kuma ku tuna lokacin da muka ɗauki alƙawari da ku cewa, ba za ku zubar da jinanenku ba, kuma ba za ku fitar da junanku daga gidajenku ba, sannan kuka tabbatar da hakan, alhalin kuna masu shaida. --Quran/2/84
  3. Sannan sai ga ku, ku ɗin nan kuna kashe junanku, kuma kuna fitar da wata ƙungiya daga cikinku daga gidajensu, kuma kuna taimaka wa juna wajen cutar da su ta hanyar laifi da zalunci. Idan kuma sun zo muku suna kamammun yaƙi sai ku fanshe su, alhali fitar da su haramun ne a gare ku. Yanzu kwa riƙa yin imani da sashen Littafi kuma ku riƙa kafircewa da wani sashen? To ba komai ne sakamakon wanda yake aikata haka daga cikinku ba face wani wulaƙanci a rayuwar duniya, kuma ranar alƙiyama a mayar da su zuwa ga mafi tsananin azaba, kuma Allah ba rafkananne ba ne game da abin da kuke aikatawa. --Quran/2/85
  4. Waɗannan su ne waɗanda suka musanya rayuwar duniya da ta lahira, kuma ba za a sassauta musu azaba ba, kuma ba za a taimaka musu ba. --Quran/2/86

Tafsiri:

A wadannan ayoyi Allah yana tuna wa Banu Isra'ila wani ƙaƙƙarfan alƙawari da ya yi da su na cewa, kada su bauta wa kowa sai shi kaɗai, ba tare da sun yi shirka da komai ba, kuma su kyautata wa iyayensu ta duk hanyoyin kyautatawa, hakanan su taimaka wa marayu, wato yaran da suka rasa iyayensu maza kuma ba su balaga ba, mazansu da matansu. Sannan ya umarce su da su zamo masu faɗa wa mutane maganganu masu daɗi, wanda hakan ya ƙunshi yi musu nasiha da wa'azi ta hanyar da ta dace, ya ƙunshi yafiya da afuwa da sauransu. Kamar yadda ya umarce su da su tsayar da salla tare da kula da hukunce-hukuncenta, su kuma fitar da zakkar dukiyoyinsu su ba wa talakawa. To amma duk bayan wannan alkawari mai karfi da ya yi da su, sai ya zamana 'yan kadan ne daga cikinsu suka cika wannan alkawari.

Bayan wancan alkawarin, ya sake tuna musu wani alkawarin na daban da ya yi da su, wanda shi ne ya hana su su rika kashe junansu ko kuma wasu daga cikinsu su rika korar wasu daga gidajensu haka kawai, ba tare da wani laifi ba, kuma suka amince da wannan alkawari, suka ba da shaida a kansa, ba su musa ba ko kadan. To amma kuma sai ga shi daga baya sun zo suna fada da junansu, har suna kashe juna, wasu daga cikinsu suna korar 'yan uwansu Yahudawa daga gidajensu ba gaira ba dalili, har ta kai ga suna taimaka wa wasu a kan cutar 'yan uwansu, saboda tsabar aikata laifi da ta'addanci irin nasu.

Wata sabuwar kuma ita ce, bayan wannan kashe-kashe da suke yi a junansu da korar junansu daga gidajensu, sai kuma ga shi idan wasu daga cikin 'yan uwansu Yahudawa sun fada hannayen abokan gabarsu a matsayin fursunonin yaki, sai kuma su zo suna fansar su da dukiyoyinsu, tare da cewa tun farko Allah ya hana su korar 'yan uwan nasu daga gidajensu, ya hana su su taimaka wa wasu makiyansa a kan yakar 'yan uwansu, amma ba su hana daga aikata hakan ba. Shi ne a nan Allah SWT yake zargin su da irin wannan danyen aikin nasu. Yaya za su ba da gaskiya da wani hukunci na Attaura, wanda shi ne fansar 'yan uwansu daga hannayen makiyansu, amma kuma su kafirce wa wasu hukunce-hukuncen, wadanda su ne (suka) hana kashe-kashe a junansu da fitar da juna daga gidajensu?!

Sannan sai Allah SWT ya fadi sakamakon duk mai aikata irin wadannan ayyuka da cewa, yana tare da taɓewa a nan duniya, kuma ranar lahira zai gamu da matsananciyar azaba, domin duk irin abin da suke aikatawa Allah yana sane da shi, babu abin da yake ɓuya a gare shi.

Sannan Allah SWT ya nuna mana irin wadannan Yahudawa su ne wadanda suka yi musanyar rayuwar duniya da ta lahira, a dalilin kafirce wa shari'ar Allah da suka yi, don haka ba za a taɓa sassauta musu azaba ba ranar gobe ƙiyama, kuma babu wani mai kawo musu ɗauki ya ƙwace su daga azabar Allah.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Girman haƙƙin iyaye, sannan haƙƙin da yake bi masa shi ne haƙƙin dangi da 'yan uwa na kusa, sannan hakkin maraya, wanda saboda ƙanƙantarsa da tsananin bukatarsa ga wanda zai kula shi, shi ne ya sa aka fara ambaton sa kafin a ambaci mabuƙaci, saboda shi mabukaci babba ne, zai iya kula da kansa ta hanyar aikin karfi, sabanin maraya.
  2. Duk wata al'umma da addini ɗaya ya haɗa ta, to tamkar jiki guda ne, shi ya sa a nan Allah ya ce, "Kada ku riƙa zubar da jininku, kuma kada ku riƙa fitar da kawunanku daga gidajenku."
  3. Ba ya halatta ga muminai su ƙulla yarjejeniya da wasu wadda ta ƙunshi warware yarjejeniyarsu da Allah ko ta ci karo da wata maslaha ta al'ummar Musulmi da sunan kare kai ko haɓaka tattalin arziki.

Baqara 87-90

  1. Kuma hakika Mun ba wa Musa Littafi, kuma Muka biyo bayansa da manzanni, kuma Mun bai wa Isa ɗan Maryam hujjoji bayyanannu, kuma Mun ƙarfafe shi da Ruhi mai tsarki. Ashe yanzu duk sa'adda wani manzo ya zo muku da abin da zukatanku ba sa so, sai ku yi girman kai, don haka sai ku ƙaryata wasu, kuma ku kashe wasu? --Quran/2/87
  2. Suka ce kuma: "Zukatanmu rufaffu ne." A'a ba haka ba ne, Allah dai Ya la'ane su ne saboda kafircinsu, don haka kaɗan ne waɗanda suke yin imani. --Quran/2/88
  3. Yayin da kuma wani littafi ya zo musu daga Allah, yana mai gaskata abin da yake tare da su, alhali kuma a da sun kasance suna addu'ar neman nasara a kan wadanda suka kafirta (mushrikai). To yayin da abin da suka sani ya zo musu sai suka kafirce masa. Don haka la'anar Allah ta tabbata a kan kafirai. --Quran/2/89
  4. Tir da wadannan abu da suka sayar da kawunansu da shi, wato suka kafirce wa abin da Allah Ya saukar, don hassadar cewa, (don me) Allah zai saukar da falalarsa ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, sai suka wayi gari da fushin Allah a kan wani fushin. Kuma azaba ta wulakanci ta tabbata ga kafirai. --Quran/2/90

Tafsiri:

A wadannan ayoyi, Allah SWT yana fada mana cewa, ya ba wa Annabi Musa AS littafin Attaura, sannan a bayansa ya ci gaba da aiko wasu manzannin zuwa ga al'ummar Banu Isra'ila, wadanda suka ci gaba da aiki da shari'ar Annabi Musa AS, har zuwa lokacin da ya aiko Annabi Isa AS, ya kuma bayyana gaskiyarsa ta hanyar ba shi mu'ujizoji daban-daban, kamar tayar da matattu, da warkar da marasa lafiya da izinin Allah, hakanan ya karfafa shi da Mala'ika Jibrilu AS wanda ya rika taimaka masa.

Sannan Allah ya nuna mana kyamar irin ta'annutin da Banu Isra'ila suka rika yi wa annabawa da ya aika musu. Wato duk sa'adda wasu manzanni suka zo musu da hukunce-hukuncen da suka saɓa wa soye-soyen zukatansu, sai su ji cewa wadannan manzanni suna matsa musu ne, kuma sun rena musu wayo, don haka sai girman kansu ya ingiza su, sai su karyata wasu daga cikin wadannan manzannin, wasu kuma ma su kashe su. Sai kuma sai suka rika fadar wata karyar cewa, wai su abin da ya hana su su yi imani shi ne, zukatansu a rufe suke rif, don haka ba sa iya fahintar wani abu da manzanninsu suke fada mus. Sai Allah ya karyata su, ya nuna abin da suke inkari ba haka yake ba; kafircinsu ne kawai ya jawo Allah ya la'ance su, ya nisantar da su daga rahamarsa, sakamakon abin da suka zaba na bijire wa koyarwar manzanninsu da annabawansu. Saboda haka sai ya kasance 'yan kadan ne a cikinsu suka ba da gaskiya, ko kuma abin da suka yi imani da shi kadan ne kwarai.

Sai Allah SWT ya ba mu labarin wani hali na Yahudawa tun sa'adda wani fada ya barke tsakaninsu da Larabawa mutanen Madina masu yin shirka, sukan ce musu: "Akwai wani Annabi da za a aiko nan ba da jimawa ba; idan ya bayyana za mu bi shi, mu hada karfi da shi, mu yi muku irin kisan da aka yi wa Adawa da Samudawa." Wato suna nufin kisan ƙare-dangi. Su Yahudawa a zatonsu Annabin zai bayyana ne daga cikinsu, sai kuma ya bayyana daga cikin Larabawa kuma Quraishawa, abokan fadansu.

Yayin da Annabi Muhammad SAW ya zo da littafin Alkur'ani, wanda yake gaskata abin da Annabi Musa da sauran annabawa suka zo da shi na Tauhidi, kuma Banu Isra'ila suka gane shi ne Annabin da suke fadar zai bayyana, suka kuma fahimci gaskiyar da ya zo da ita, to maimakon su yi imani kamar yadda suka kasance suna shelantawa, sai kawai suka kafirce masa, a dalilin haka sai Allah SWT ya la'ance su, ya nisantar da su daga rahamarsa. Wannan kuma shi ne sakamakon kowane kafiri a duniya.

Sannan Allah SWT ya yi tir da irin wannan mugun zabi da Yahudawa suka yi wa kawunansu, wato suka zabi su kafirce wa Annabin da suka san gaskiyarsa, suka zabar wa kawunansu shiga wutar Jahannama, ba don wani abu ba, sai don kawai tsabar hassada da kabilanci da suke yi wa Larabawa, wai don me Allah SWT zai aiko da Annabi a cikinsu ba a cikin Banu Isra'ila ba, tare da cewa sun san shi Allah SWT yana bayar da falalarsa ne ga wanda ya ga dama daga cikin bayinsa bau mai iya hana shi. Wannan ne ya sa Yahudawa suka cancanci wani fushi daga Allah (SWT) a kan fushin da suka cancanta a baya na laifukan da suka rika tabkawa. Don haka ne duk wadanda za su bijire wa sakon Annabi Muhammadu SAW a kowane zamani ne to suna da wata azaba mai wulakantarwa.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Annabawan da suka zo daga cikin Banu Isra'ila bayan Annabi Musa AS sun rika aiki ne da shari'arsa.
  2. Daga cikin ayyukan mala'iku akwai karfafar manzannin Allah.
  3. Asali zukatan 'yan'adam a bude suke, gaskiya na iya shigar su, kafircin dan'adam ne yake musabbabin Allah ya la'ance shi, sai ya kulle masa kofofin shirya.
  4. Annabya falala ce daga Allah SWT da yake bayar da ita ga wanda ya zaba.

Baqara 91-93

  1. Idan aka ce da su: "Ku yi imani da abin da Allah Ya saukar", sai su ce: "Mu muna yin imani ne da abin da aka saukar mana". Kuma suna kafircewa da duk wani abu da ba shi ba, alhalin shi gaskiya ne, kuma mai gaskata abin da ke tare da su ne. To ka ce: "Me ya sa a da kuke kashe annabawan Allah idan kun kasance muminai?" --Quran/2/91
  2. Hakika Musa ya zo muka da hujjoji bayyanannu, sannan kuka bauta wa dan maraƙi bayansa alhalin kuna azzalumai. --Quran/2/92
  3. Kuma ku tuna lokacin da Muka dauki alkawari da ku, Muka kuma daga dutsen Ɗuri a kanku, Muka ce: "Ku riƙi abin da muka ba ku da karfi, kuma ku saurara". Sai suka ce: "Mun ji kuma mun saɓa". Kuma aka sanya musu tsananin son bautar dan maraƙi a zukatansu saboda kafircinsu. Ka ce: "Tir da abin da imaninku yake umartar ku da shi, idan har kun kasance muminai." --Quran/2/93

Tafsiri:

A nan Allah SWT ya bayyana mana yadda Banu Isra'ila suke iqrarin cewa, su sun yi imani ne da Attaura kawai, kuma ta wadatar da su, ba sa bukatar sai sun yi imani da Alkur'ani. To shi ne a nan Allah yake karyata su, yana bayyana cewa, hatta ita ma Attaurar ba wani cikakken imani suka yi da ita ba. Duk da cewa shi Alkur'ani Allah ya saukar da shi ne bayan Attaura, kuma yana gaskata abin da yake cikin Attaura na Tauhidi da rukunnan imani. Wannan magana tasu tubka da warwara ce, domin duk wanda ya karyata Alkur'ani, to ya karyata sauran littattafan ma gaba daya.

Sannan sai Allah ya umarci Annabinsa Muhammad SAW da ya tambaye su, idan har da gaske suke sun yi imani da Attaura, me ya sa suke kashe annabawan Allah wadanda su ma suna gaskata abin da yake cikinta? Kuma a cikin Attaura an haramta kashe kowane Annabi.

A karshe sai Allah ya nuna a fili cewa, karya suke yi, ba su yi imani da Attaurar ba, domin tun farko da Annabi Musa ya zo musu da hujjoji bayyanannu masu tabbatar da gaskiyar annabcinsa, sai suka koma suna bautar dan maraqi lokacin da ya tafi ganawa da Ubangijinsa saboda qetare iyaka da zalunci.

Sannan Allah SWT ya sake tuna wa Banu Isra'ila labarin lokacin da ya dauki alkawarin mai karfi a wurinsu, har ya daga dutsen D'uri a samansu, kamar ya rufto ya fado musu, domin a tsoratasu a kan dole su yi aiki da umarnin da aka ba su na cewa lalle su rike Attaura gamgam da himma da nashadi, kuma su saurari maganar Allah, sauraro na karba da mika wuya, amma sai suka amsa wa Allah SWT da cewa, sun ji da kunnuwansu, amma kuma sun sab'a da ayyukansu. Son bautar dan maraqi ya riga ya ratsa zukatansu, sun kwankwad'e shi da gaske, kamar yadda mai jin qishirwa yake kwankwad'ar ruwa idan ya samu, har ya ratsa ko'ina a jikinsa.

Bayanan da suka gabata sun tabbatar da cewa, imanin Yahudawa na jabu ne, tun da bai hana su kashe annabawan Allah ba, bai hana su bautar dan maraqi ba, bai kuma hana su bijire wa umarnin Ubangijinsu ba. Don haka sai Allah ya yi tir da wannan imani nasu, ya tabbatar da cewa, imani na qwarai shi yake sanya mai shi ya aikata alheri ya kuma kauce wa sharri.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Qaryar Yahudu wajen da'awar sun yi imani da Attaura, alhalin suna sab'a mata a fili da ayyukansu.
  2. Wajibi ne ga mumini ya karbi shari'ar Allah da karfi da nishadi, ba da kasala ba.
  3. Wajibi ne mutum ya karbi gaskiya daga bakin duk wanda ya fad'e ta.

Baqara 94-96

  1. Ka ce: "Idan gidan lahira ya kasance kebantacce a gare ku a wurin Allah ku kadai ban da sauran mutane, to ku yi burin mutuwa idan har ku masu gaskiya ne." --Quran/2/94
  2. Ba za su tab'a burin mutuwa ba har abada, saboda abin da hannayensu suka aikata. Kuma Allah Masani ne ga azzalumai. --Quran/2/95
  3. Kuma za ka same su sun fi kowa kwad'ayin tsawon rai, fiye ma da wadanda suka yi shirka. Kowane d'ayansu yana burin ina ma za a raya shi shekara dubu. Kuma Allah Mai ganin abin da suka kasance suna aikatawa ne. --Quran/2/96

Tafsiri:

A nan Allah yana fada wa Annabinsa cewa, idan Yahudawan Madina suna da'awar cewa, don su kadai Allah (SWT) ya tanadi ni'imar gidan Aljanna a lahira, ban da sauran mutane, to ga wata hanya da za a bi a gane mai gaskiya, ita ce su hadu su yi addu'ar tsinuwa, wato su roqi Allah ya halaka maqaryaci daga cikinsu. Allah SWT ya nuna cewa, sam-sam Yahudawa ba za su tab'a karb'ar wannan kira nasa ba, saboda suna sane da irin laifuffukan da suka tabka na kafirce wa Annabi da boye gaskiya, kuma suna sane da cewa hanyar haduwa da mummunan sakamakon miyagun ayyukansu ita ce mutuwa; da zarar sun mutu, to sun fada cikin abin qi ke nan har abada. Wannan kadai ya isa ya hana su son mutuwa. To amma fa kada su manta da cewa, Allah yana sane da duk wani azzalimi mai keta dokarsa a bayan qasa, kuma komai dadewa sai Allah ya damqe shi ya nuna masa sakamakonsa.

Daga nan sai Allah ya tabbatar da cewa, ai babu wani jinsi na mutane da yake gudun mutuwa irin jinsin Bayahude, domin ya san abin da yake jiran sa a lahira na azaba, don haka za ka ga kowane dayansu yana son ya yi tsawon rai a duniya, ta yadda soyayyarsu da rayuwa a nan duniya, har ta zarce ta mushrikai wadanda ma ba su yi imani da akwai ranar lahira ba, ballantana har su yarda da cewa akwai wani sakamako da zai biyo baya. Ai shi Bayahude burinsa shi ne ya rayu shekara dubu a duniya, to amma ya manta cewa, ko da an ba shi tsawon rai irin wannan, ba zai hana shi mutuwa ba, kuma da zarar ya mutu wuta ce makomarsa. Allah kuma yana ganin duk abin da suke aikatawa na miyagun ayyuka, ba abin da yake buya a gare shi kuma zai yi musu sakayya a kansu daya bayan daya.

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Tsawon rai idan ya kasance cikin sab'on Allah ne, to ba shi da wani amfani ga mutum. Don haka ka roka wa wanda kake kauna jinkiri mai amfani, kamar yadda ya zo cikin addu'o'in da Annabi SAW ya koyar da al'ummarsa:
    • "Ya Allah ka raya ni matukar rayuwa ce mafi alheri a gare ni, ka kuma karbi raina idan mutuwar ce ta fi alheri a gare ni."
    • "O Allah! Keep me alive as long as life is better for me, and let me die if death is better for me.' " [Bukhari #5671 da Muslim #2680]
  2. Yahudawa sun fi kowa son rayuwa a duniya, saboda yadda suka fitar da qauna daga ni'imar lahira.
  3. Allah ya nuna mana su Yahudawa da masu halaye irin nasu, suna sha'awar rayuwar duniya ce ko ma wace iri, kuma ba ruwansu da kyanta ko rashin kyanta, sabanin Musulmi; shi yakan yin fatan rayuwa ce mai albarka a gare shi da al'ummarsa.

Baqara 97-101

  1. Ka ce: "Duk wanda ya kasance maqiyi ne ga Mala'ika Jibrilu, to lalle shi ne ya saukar da shi (Alkur'ani) a kan zuciyarka da izinin Allah yana mai gaskata abin da ya gabace shi (na littattafai), kuma shiriya ne da bushara ga muminai." --Quran/2/97
  2. Duk wanda ya kasance maqiyi ne ga Allah da mala'ikunsa da manzanninsa da Jibrilu da Mika'ilu, to lalle Allah maqiyin kafirai ne. --Quran/2/98
  3. Kuma haqiqa Mun saukar maka da ayoyi bayyanannu, babu kuma mai kafirce musu sai fasiqai. --Quran/2/99
  4. Yanzu ashe duk sa'adda suka qulla wani alqawari sai wani b'angare daga cikinsu ya yi watsi da shi?! Bari! Yawancinsu ba sa yin imani. --Quran/2/100
  5. Yayin da wani manzo daga Allah ya zo musu yana mai gaskata abin da yake tare da su (na Littafin Attaura), sai wani b'angare daga cikinsu suka jefar da littafin Allah a bayansu kamar ba su san komai ba. --Quran/2/101

Tafsiri:

Imamut Tirmizi #3117 da Imam Ahmad #2483 sun ruwaito hadisi daga Abdullahi dan Abbas rA ya ce: "Yahudawa sun zo wurin Manzon Allah SAW suka ce masa: "Ya Baban Alqasim, mun zo ne mu yi maka tambaya a kan abubuwa guda biyar, idan ka ba mu amsarsu, to mun fahinci kai Annabi ne, kuma za mu bi ka. Sai Annabi SAW ya kafa musu shaida da Allah, kamar yadda Annabi Yakubu AS ya yi da 'ya'yansa, lokacin da suka ce: "Allah ne wakili bisa duk abin da za mu fada." Sai Annabi SAW ya ce: "To ku yi tambayoyinku." Sai suka ce: "Ka fada mana mece ce alamar annabi?" Sai ya ce: "Alamarsa ita ce, idanuwansa za su yi barci, amma zuciyarsa ba za ta yi ba." Sai suka ce: "To ka fada mana mene ne ya sa mace wani lokaci ta haifi 'ya mace, wani lokaci kuma ta haifi ɗa namiji?" Sai ya ce: "Idan ruwan 'ya mace ya rinjayi ruwan ɗa namiji, to sai ta haifi 'ya mace, idan kuwa namijin ne ya rinjayi na matar , sai ta haifi ɗa namiji." Sai suka ce: "To faɗa mana, wane irin abinci ne Isra'ilu (Ya'aƙub) ya haramta wa kansa?" Sai ya ce: "Ya yi fama da cutar ciwon kwankwaso da kafafu (Sciatica), bai samu wani magani da ya yi masa amfani ba, sai nonon abu kaza da abu kaza. (Imam Ahmad ya ce wasu sun ce nonon rakumi ne ya samu). Daga lokacin sai ya haramta wa kansa cin namansu." Sai suka ce: "Ka yi gaskiya."

Sannan kuma su ka ce: "To fada mana mene ne wannan tsawar da muke ji?" Sai ya ce: "Wannan mala'ika ne da Allah ya wakilta shi don ya kula da girgije, yana dauke da wani takobi na wuta a hannunsa, yana kora wannan girgije da shi har zuwa inda Allah ya umarce shi." Sai suka ce: "To, shi kuma wannan karar da ake ji ta mece ce?" Sai ya ce: "Muryarsa (Mala'ikan) ce." Sai suka ce, "Ka yi gaskiya."

Sannan kuma suka ce masa: "To yanzu saura tambaya daya ta rage, idan ka amsa mana ita, to za mu yi maka mubaya'a, domin babu wani annabi face yana da wani mala'ika da yake kawo masa labarai. To ka fada mana kai wane ne mala'ikanka?" Sai ya ce: "Jibrilu ne (AS)." Cikin mamaki, sai suka ce: "Jibrilu? Ai wannan shi ne wanda yake saukowa da yaqi da kashe-kashe da azaba, ai wannan maqiyinmu ne! Da dai ka ce mana mala'ika ne wanda yake saukar da rahama da tsaro da ruwan sama, da abin ya yi kyau." Sai Allah SWT ya saukar da wadannan ayoyi (watau aya 97-99).

Allah ya ce wa Annabinsa SAW ya fada wa wadannan Yahudawa cewa, duk wanda yake gaba da Mala'ika Jibrilu, to ya sani cewa, shi Jibrilu yana saukar wa Annabi Alqur'ani ne da umarnin Allah, ba a gaban kansa yake yi ba, don haka ba shi suke nuna wa qiyayya ba, Allah ne da ya aiko shi suke nuna wa kiyayya. Sannan kuma Alkur'ani da yake saukar masa, koyarwar cikinsa tana daidai da abin da ya zo a littattafan annabawan da suka gabace shi, kamar Attaura. Wannan kuwa babban dalili ne da yake nuna gaskiyarsa, sannan shi Alkur'ani babbar bushara ce ga muminai ta irin abin da Allah ya tanadar musu na ni'ima mai d'orewar.

Sannan Allah ya ci gaba da fada musu cewa, duk wanda yake qin Allah ko yake qin wani mala'ika, ko Mala'ika Jibrilu, Mika'ilu ko yake gaba da wani manzo daga cikin manzannin Allah, to wannan kafiri ne, kuma Allah zai dauke shi a matsayin abokin gabarsa, domin Allah ba ya son kowane irin kafiri. Shi ya sa ya zo a hadisi qudsi inda Allah yake cewa: "Duk wanda ya yi gaba da wani masoyina, to lalle ina yi masa shelar yaqi." [Bukhari #6502]

Abdurrahman dan Abu Laila ya ruwaito cewa, wani Bayahude ya gamu da Sayyidina Umar AS sai ya ce masa: "Jibrilun nan da Annabinku yake ta fada fa makiyinmu ne." Sai Umar AS ya mayar masa da martani da cewa: "Wanda duk ya kasance maqiyin Allah da mala'ikunsa da manzanninsa... (har zuwa qarshen ayar)." Ya ce: "Sai wannan ayar ta sauka." [Duba Tafsirin Ibnu Abi Hatim 1:182, da Fathul Bari na Ibnu Hajar 8:16].

Sannan Allah ya ci gaba da fada wa Annabinsa cewa, ya saukar masa da ayoyi bayyanannu, masu nuna gaskiyar annabcinsa, babu wanda yake ja da su sai wanda ba mumini ba. Allah kuma ya fada masa cewa, Yahudawa wasu mutane ne marasa alqawari; duk sa'adda suka d'aukar wa Allah alkawarin za su yi aiki da Attaura da abin da ta qunsa na shari'a, to sai an samu wasu daga cikinsu sun warware alkawarin nan sun yi jifa da shi, ba komai ya jawo haka ba, sai domin yawancinsu ba masu imani ba ne, domin da suna da imani na gaskiya, to da sun kiyaye alkawari, ba su karya shi ba.

Daga cikin ire-iren karya alkawarin da suka yi shi ne, lokacin da Allah ya aiko Annabinsa SAW ya zo kuma kamar yadda Allah ya siffanta musu shi a cikin littattafansu, kuma ya yi alkawari da su a kan za su bi shi idan ya bayyana, to sai ga shi yanzu yawancinsu sun yi watsi da wannan alkawarin, sun yi jifa da littafin Attaura can bayansu, kamar ba su tab'a sanin wani abu ba dangane da wannan Annabi da siffofinsa.

Baqara 102-103

  1. Sai suka bi abin da sheɗanu suke karantawa a (zamani) mulkin Sulaimanu; kuma Sulaimanu bai kafirta ba, sai dai sheɗanun su ne suka kafirta suna koya wa mutane tsafi da abin da aka saukar wa mala'iku biyu, Haruta da Maruta, a garin Babila. Kuma ba sa koya wa wani (tsafin) har sai sun faɗa masa cewa: "Mu fa jarraba ce, don haka kada ka kafirta." Sai (mutane) suka riƙa koyo daga wajensu su biyu abin da suke raba tsakanin miji da matarsa da she. Kuma ba za su iya cutar da wani da shi ba sai da izinin Allah. Sai su koyi abin da zai cutar da su kuma ba zai amfane su ba. Kuma haƙiƙa sun san cewa, duk wanda ya zaɓi (sihiri) ba shi da wani rabo a lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da kawunansu da shi, da a ce sun san (haƙiƙanin makomarsu). --Quran/2/102
  2. Da a ce su sun yi imani kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa da sakamakon (da za su samu) daga Allah shi ne mafi alheri, da a ce sun sani. --Quran/2/103

Tafsiri:

A nan Allah ya ci gaba da ba da labarin halin da Yahudawa suka tsinci kansu a ciki, bayan sun yi watsi da littafin Allah da koyarwar annabawansu, sai suka rungumi koyarwar shaidanu a madadin haka, wanda sakamakon haka shi ne duk wanda ya bar koyarwar annabawa da ilimi mai amfani, to lalle a madadinsa sai ya rungumi wani ilimi marar kyau mai cutarwa.

pg108